Topic: Boye Ilimi: Malami fajiri da kuma jahilin mai ibada su ke halaka al’ummar Musulm
Timeline: 2012-03-27 19:03:52
Boye Ilimi: Malami fajiri da kuma jahilin mai ibada su ke halaka al’ummar Musulm
A Rubuce Da Ahmad Muhammad
Daga wasikar Shehu danfodiyo
Ya ’yan uwana kada ku boye ilimi, Allah Mabuwayin Sarki Ya ce a cikin Alkur’ani Mai Tsarki, “ka ga wadanda suka boye abin da Muka saukar, daga dalilai masu bayyana karya da gaskiya, su kuma bayyana hanyar shiriya daga bata, bayan Mun bayyana su ga mutane cikin littattafai wanda Muka saukar, to wadannan mutane su ne wadanda Allah Yake tabbatar da la’anarSa a kansu. Su ne kuma wadanda suka cancanci duk la’anar masu la’ana.”
An samo hadisi, Annabi (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce, “wanda ya boye ilimi mai amfani, Allah Zai yi masa linzami (da shi ilimin) da linzami daga wuta”. Ya ku ’yan uwana, kada ku kuskura ku zauna tare da miyagun malamai, ma’abuta rafkana, mataimakan shaidanu, mamayan kujerar iblis, wajen barna. Su ne masu kutsawa cikin aikin kowace bidi’a saboda kwadayin abin duniya.
Allah Mabuwayin Sarki Ya ce, “ce (masu) jin dadin duniya, komai dadewarsa, kadan ne, a daure a saurari na lahira (mai dauwama) shi ya fi amma fa ga mai tsoron Allah (da ya kaunaci abin da karko zai kawo).”
To kuma ba ka dubi ga abin da Allah Ya ce, “ya ku wadanda suka ba da gaskiya, ku san fa akwai da yawa daga cikin manyan malaman Yahudawa da malaman Nasara ba sa yi don Allah, sai dai duniya, suna yin wayo domin su yi suna, su ci dukiyar mutane da yaudara, suna kuma kangewa ga bin hanyar Allah.”
Shaihu Abdulkarim dan Muhammadul Akiliy, cikin malaman kasar Tulmusan, ya ce da yawa daga cikin malaman wadannan al’umma da masu bautar ganin ido, dukiyar mutane suke ci ta hanyar damfara, kuma suna kangewa ga bin hanyar Allah saboda wadannan malamai da wadannan masu bautar ganin ido, barna ta watsu cikin dukkan garuruwa.”
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce, “halakar al’ummata, tana ga hannun mutum biyu.” 1. Malami fajiri (mai aikata miyagun aiki); da 2. Jahili (mai bautar ganin ido).
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) kuma ya ce, “ni fa ba dujjal kadai ne nake jiye muku ba, ni ina jiye muku tsoro daga wasu dujjalai.”
Sai Sahabbai suka ce, “daga wadanne, ya Manzon Allah?” Sai ya ce, “daga miyagun malamai.”
An ruwaito daga bakin Huzaifatu dan Yamani, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce, “wata rana a cikin jama’a, sai Annabi ya dauki farar tsakuwa sai ya sanya ta cikin tafinsa, sai ya ce, “addini dai ya haskaka, shi ne kwatancin wannan farar tsakuwa.” Sai ya damki turbaya a cikin tafin hannunsa guda, ya dinga barbada ta a kan wannan farar tsakuwa har ta rufe ta, sai ya ce, “na rantse da Wanda raina ke gare Shi, akwai wadansu mutane da za su zo bayana, wadanda suke aikinsu shi ne binne addini kamar yadda wannan turbaya ta binne wannan farin dutse. Daga mafi bayyana wurin gane su kuwa, shi ne sai ka ga su ba su gyara kuma ba su barin mai gyarawa ya gyara. Kwatancinsu kamar falale ne a cikin korama, ba ya sha kuma ba ya barin mai sha, ya sha. Kowane daya daga cikinsu yakan halakar da mutane fiye da shaidani dubu.” - Gani ya kori ji.
To, ya ku ’yan uwana Musulmi, ku sani miyagun malamai su ne masu tozarta hakkin Allah (dokokin Allah). Sun keta inda Ya iyakance musu daga abin da ya shafi sallah da azumi da sauran farillai, domin son dukiya da neman a girmama su. Sun cudanya a cikin fannoni na haram da laifuf*****a. Sun kuma tozarta abubuwa masu yawa daga al’amarin Allah wadanda Ya yi horon a aikata da wadanda Ya yi hani ga aikatawa.
Saboda haka sun kai wa Allah hari da aikata manyan miyagun ayyuka, sun yi zaman gaba-gadi da kwanciyar hankali da farin ciki da kawatuwa a rayuwarsu ta duniya. Wadannan su ne wadanda Allah Ya ce a kansu, “Za Mu cika musu sakamakon ayyukansu a nan cikin duniya, kuma ba za a tauye musu komai ba. Ka ga wadannan cikakken sakamakonsu shi ne ba su da wani rabo a lahira, sai wuta. Dukkan abin da suka aikata a nan duniya ya ruguje, abin da suke aikatawa kuma batacce ne.”
To ya ku ’yan uwana, ku sani kyautatuwar al’umma yana daga kyautatuwar malamanta ne. Haka kuma bacin al’umma yana daga miyagun malamanta ne. Domin su malamai, idan sun zama masu aiki da yardar Allah Mabuwayin Sarki, masu zabin lahira a kan duniya, to wadannan su ne halifan manzanni. Su ne kuma masu nasiha ga bayi, kuma su ne masu kira zuwa ga hanyar Allah. Su ne masu kira ga tafarkin tsira. Wanda ya amsa kiransu ya azurta. Wanda ya yi koyi da su ya samu babban rabo. Allah Mabuwayin Sarki Ya ce, “babu mafi kyautata magana kamar wanda ya yi kira zuwa ga Allah, ya aikata kyakkyawan aiki. Ya budi baki ba da shakkar komai ba ya ce, ‘ni a cikin musulmi nake.’
Ku sarara ku ji ya ’yan uwana, wani daga cikin bayin Allah ya fashe da kuka, sai ya ce, “kukana shi ne miyagun malamai sun zauna a kan hanyar da za a bi a samu lahira. Suka kuma kange bayin Allah ga bin wannan hanya da za su ji dadin saduwa da Allah.”
**{Legacy activities, comments etc counter: 1070; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}