Topic: Tuba da istigfari (10)
Timeline: 2012-03-27 19:26:45
Tuba da istigfari (10)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Shi kadai. Tsira da amincinSa su kara tabbata ga wanda ba wani Annabi a bayansa.
Bayan haka, a ci gaba da darasinmu kan tuba da istigfari, cikin yardar Allah yau za mu duba wasu misalai na tarihin tubar wadansu bayin Allah da sauran mas’alolin da suka shafi tuba.Kuma a yau muke kawo karshen wannan bincike kan wannan babi mai girma. Allah Ya sa mu amfana da abin da muka karanta ko muka ji:
1. kissar tubar Abu Muhjin As-Sakafi:
Daga Ibn Sairin ya ce: “Abu Muhjin As-Sakafi ya kasance bai gushe ba, ana yi masa bulala kan shan giya. Da abinsa ya yi yawa, sai suka daure shi a kurkuku. To a ranar fafatawar kadisiyya, sai ya yi mafarki lallai mushirikai sun samu galaba a kan Musulmi. Sai ya aika zuwa ga Ummu Waladi Sa’ad (kuyanga) ko matar Sa’ad cewa: “Lallai Abu Muhjan yana ce miki: “Idan kika kyale shi kuma kika dauke shi a kan wannan doki kika ba shi makami, wallahi zai kasance mutum na farko da zai dawo gare ki, sai dai in an kashe shi. Sai ta cire masa talalarsa aka dora shi a kan dokin da yake gidan, aka ba shi makami, sannan ya fita yana gudu har ya riski mutanen, ya rika dukan wuyan mutum ya kashe shi ya fincike salibunsa. Sai Sa’ad ya dube shi yana mamaki yana cewa “wane ne wancan mayaki? Ya ce, ba a dade ba, har Allah Ya wargaza su, Abu Muhjin ya koma, ya mayar da makamin aka mayar da daurin da aka yi masa a kafafunsa kamar yadda yake a baya. Sa’ad ya dawo, sai matarsa ta ce masa: “Yaya yakinku ya gudana? Sai ya rika ba ta labari yana cewa: “Mun buga, mun buga har Allah Ya aiko da wani mutum a kan doki, ba don na bar Abu Muhjin a daure ba da na ce, dabi’unsa na Abu Muhjin ne.” Sai ta ce: “Wallahi Abu Muhjin ne, al’amarinsa ya kasance kaza da kaza, sai ta ba shi labarin yadda aka yi. Sai ya ce kira shi, aka kwance masa daurinsa. Sannan ya ce, “Har abadan ba za mu sake yi maka bulala kan shan giya ba.” Shi kuma ya ce: “Wallahi ni kuma ba zan sake shanta ba har abada. A baya na kasa barinta ne saboda bulalarku.” Ya ce, bai sake shanta ba bayan haka.” (a duba Al-Isabah Fi Tamyizis Sahabah na Ibn Hajar, Mujalladi na 7 shafi na 360-362).
2. kissar tubar Fudailu Bin Iyal:
An karbo daga Aliyu Bin Khashram ya ce: “Wani daga cikin makwabtan Fudailu Bin Iyal ya ba ni labari ya ce: “Fudailu ya kasance yana tsare hanya (ya yi fashi) shi kadai. Wani dare sai ya fita don ya tsare hanyar, sai ya ci karo da wani ayarin fatake sun iso cikin dare. Sai suka ce wa juna: “Mu kwana a wannan alkarya, saboda a gabanmu akwai wani mutun da ke tsare hanya ana kiransa Fudailu. Ya ce: “Sai Fudailu ya ji, ya yi tsawa ya ce: “Ya ku mutane! Ni ne Fudailu. Ku wuce, wallahi zan yi kokari ba zan sake saba wa Allah ba har abada. Sai ya tuba daga abin da yake yi.” (Siyarul A’alamin Nubla, Mujalladi na 8 shafi na 423).
Wasu kura-kurai da ake yi game da tuba:
1. Jinkirta tuba:
Daga cikin mutane akwai wanda yake gano kuskurensa ya san haramcin abin da ya auka a ciki, amma sai ya jinkirta tuba, ya ci gaba da sabonsa, wannan babban kuskure ne. Domin wajibi ne a gaggauta tuba, kai jinkirta tuba ma wani zunubi ne da ya wajaba a nemi gafara a kansa.
Algazali yana cewa: “Amma wajibcin gaggauta ta abu ne da ba a kokwanto a kai, saboda sanin ayyukan sabo suna halakarwa a bangaren imani, don haka wajibi ne a gaggauta.” (Ihya’u Ulumid Din, Mujalladi na 4 shafi na 7).
Ibn kayyim ya ce: “Gaggauta tuba daga zunubi wajibi, ba ya halatta a jinkirta ta. A duk lokacin da ya jinkirta ta ya aikata sabon jinkirta ta. Idan ya tuba daga zunubin wata tuba tana kansa, ita ce tubarsa daga jinkirta tubar.” (Mudarijis Salikina, Mujalladi na 1 shafi na 283).
2. Gafala daga tuba daga abin da bawa bai sani na zunubinsa ba;
Wannan yana daga cikin kura-kuran da suke aukuwa a bangaren tuba, kadan ne suke lura da haka. Ibn kayyim ya ce: “Babu abin da zai tserar da mutum daga haka, sai tuba daga dukkan zunubin da mutum ya sani da wanda bai sani ba. Domin zunuban da mutum bai sani sun fi wadanda ya sani, kuma rashin sanin ba zai hana a kama shi da su ba, domin ya zama mai sabo ta hanyar barin ilimi da aiki, don haka sabon a game da shi ya fi tsanani.” (Mudarijis Salikina, Mujalladi na 1 shafi na 283). Kan haka ne Manzon Allah (SAW) ya ce: Shirka a cikin wannan al’umma ya fi boyuwa daga takun kafar tururuwa.” Sai Abubakar ya ce yaya za a kubuta daga gare shi ya Manzon Allah? Ya ce: “Ka ce: “Allahumma inni a’uzu bika an ushrika bika wa ana a’alamu, wa astagfiruka lima la’alamu.” Ma’ana: “Ya Ubangiji! Ina neman tsari da kai ga in yi maKa shirki alhali ina sane, kuma ina neman gafararKa daga wanda ba na sani ba.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
3. Barin tuba saboda tsoron sake aikata zunubi:
Ya wajaba a kan Musulmi ya tuba zuwa ga Allah a kowane lokaci da yanayi. Ba mamaki mutuwa ta riske shi alhali bai gama tuba ba. Kmara yadda ya wajaba a kansa ya kyautata zato ga Ubangijinsa, ya san cewa idan ya koma zuwa ga Allah, Allah zai fuskanto shi. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce: Ina inda bawaNa ya zace Ni, kuma ina tare da shi lokacin da ya tuna Ni.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
4. Barin tuba saboda tsoron zunden mutane:
Daga cikin mutane akwai wanda zuciyarsa za ta rika saka masa ya tuba ya tsayu kan daidai, amma kuma sai ya rika jin tsoron mutane da aibantawarsu gare shi da yadda za su rika siffanta shi da tsaurin ra’ayi, sai ya rika kai-kawo. Wannan babban kuskure ne. Don me zai gabatar da tsoron mutane a kan tsoron Ubangijin mutane? Ta yaya zai fifita abin halitta a kan Mahalicci? Allah ne Ya cancanci a ji tsoronSa!
5. kin tuba saboda tsoron rasa matsayi ko rasa girma da daukaka.
6. Ci gaba da aikata zunubi bisa dogaro da yalwar rahamar Allah:
Allah Madaukaki Yana cewa: “Ka ba bayiNa labari cewa lallai ne Ni Mai gafara ne Mai jin kai. Kuma azabaTa, ita ce azaba mai radadi.” (k:15:49-50).
7. Ruduwa da talalar Allah ga masu aikata laifi:
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yana yin talala ga azzalumi, amma idan ya kama shi ba zai kwace maSa ba.” Sannan ya karanta fadinSa Madaukaki: “Kuma kamar wancan ne kamun Ubangijinka, idan ya kama alkaryoyi alhali kuwa suna masu zalunci. Lallai kamunSa mai radadi ne mai tsanani ne.” (k:11: 102).
8. Yanke kauna daga rahamar Allah:
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai shi babu mai yanke kauna daga rahamar Allah face mutane kafirai.” Ka ce: (Allah Ya ce): “Ya ku bayiNa wadanda suka barna a kan rayukansu! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lallai Allah Yana gafarta zunubai gaba daya. Lallai Shi, Shi ne Mai gafara Mai jinkai.” (k:39:53).
Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabansa baki daya.
**{Legacy activities, comments etc counter: 599; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}