Topic: Ladubban shiga gida da ziyara a Musulunci (1)
Timeline: 2012-05-13 06:09:46
Ladubban shiga gida da ziyara a Musulunci (1)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin kowa da komai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Bayan haka cikin yardar Allah yau za mu duba wani babi da ya shafi rayuwarmu ta yau da kullum. Wato shiga gidajen da ba namu ba, ya alla lokacin kai ziyara ga ’yan uwa da abokan arziki ne ko saboda wani dalili na daban.
Kamar yadda malamai suka sha nanatawa Musulunci daukacin rayuwa ne, don haka babu wani abu da Musulmi zai yi face Musulunci ya ce ga yadda zai yi. Kuma mai Ahlari ya ce ba ya halatta ga Musulmi mukallafi ya aikata kowane aiki sai ya san hukuncin Allah a ciki, wannan ya dace da fadin Allah Madaukaki, “Ka sani (ka yi ilimi sanin) cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah...”
Don haka shiga gida don wata bukata ko yayin ziyarar da duk abin da Musulmi zai aikata kamar aure da kasuwanci da aikin gwamnati ko na kamfani da ko ma wane irin aiki ne wajibi ne ya san hukuncin Allah a ciki. Idan ya san hukuncin Allah a cikin duk abin da zai yi zai samu lada matukar ya yi da kyakkyawar niyya. Amma idan bai san hukuncin Allah a ciki ba, komai kyan aikin komai kyakkyawar niyya, aikin banza ya yi kuma maimakon lada zunubi zai samu.
Ziyarar ’yan uwa da abokai ibada ce, kuma yayin da ziyarar ’yan uwa ta zama wajibi, a matsayinta na daya daga cikin hanyoyin sada zumunta, Manzon Allah (SAW) ya sunnata mana ziyarar abokai da aminai kamar yadda littattafan Musulunci suka nuna. Ziyayar ’yan uwa da abokan arziki na daga cikin hanyoyin karfafa zumunta da aminci a tsakanin mutane.
Sai dai abin tambaya haka gatsau mutum zai kama hanya da sunan ziyarar ya shige gidan ’yan uwa da abokan arziki a duk lokacin da ya ga dama?
Musulunci ya tsara lokacin da ya kamata a kai ziyara da kuma yadda ake neman izinin shiga gidan da aka kai wa ziyarar, ba don komai ba, sai don ya kare hakkin dan Adam na ya shakata a wasu lokuta da galibi yake hutawa ko kadaita da iyalinsa ta yadda ba za a sanya shi a halin kunci ba.
Allah Madaukaki Ya fadi a cikin Alkur’ani Mai girma cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku shiga wani gida da ba gidajenku ba, har sai kun nemi izini kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan ne mafi alheri a gare ku, tsammaninku za ku yi tunani. Idan kuma ba ku samu kowa a ciki ba, kada dai ku shiga har sai an yi muku izini. Idan kuma aka ce ku koma, to ku koma, shi ne mafi tsarki a gare ku. Kuma Allah Masanai ne game da abin da kuke aikatawa. Amma babu laifi a kanku ku shiga gidajen da ba a zaune a cikinsu kuma kuke da kaya a cikinsu. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke bayyanawa da abin da kuke boyewa.” (Nur:27-29).
Wadannan ayoyi sun nuna mana ladubban shiga gida, kuma sun nuna mana ba a yarda mu shiga gida ba don kawai na ’yan uwanmu ne ko abokanmu, har sai an ba mu izini daga mazauna gidan.
Dokta Imtiaz Ahmad a cikin littafinsa Reminders for People of Understanding ya ce, wadannan ayoyi sun kasa gidajen zuwa kashi hudu, inda Musulunci ya tsara wa kowanne irin hukuncin da ya dace da shi.
Gidan da kake zaune a ciki kai kadai da gidan da wadansu suke zaune da gidan dab a kowa da kuma gidan ko ginin da yake na kasuwanci ko jama’a kamar gidajen saukar baki da ofisoshi da makamantansu
Sai ya ce:
“Na daya, gidanka da kake zaune a ciki kai kadai. Babu bukatar ka nemi izinin kowa don shiga ciki, shi ya sa ayoyin ba su ce komai a kai ba.
Na biyu, shi ne gidan da wadansu suke zaune a ciki. Ba a yarda ka shiga wadannan gida ba ba tare da ka yi sallama ga mazauna gidajen ba, kuma ka nemi izininsu (ta hanyar cewa “in shigo?”). Za ka shiga gidan ne kawai idan mazaunan gidan suka ba ka izini.
Na uku, shi ne gidan da ba wanda ke zaune a ciki ko ana jin a lokacin ba kowa a ciki. Duk da haka ba a yarda ka shiga gidan ba. Domin ba wanda aka yarda ya taba ko ya keta alfarmar dukiyar wadansu ba tare da amincewarsu ba, don haka an hana shiga irin wadannan gidaje duk da ba kowa a ciki. Saboda Musulunci yana nuna kula sosai tare da girmama mutane da dukiyarsu.
Kashi na hudu shi ne, gidajen da aka gina su don amfanin jama’a da dama. Kamar tashoshin jiragen kasa da makarantu da gidajen cin abinci da loji-lojin ko gidajen saukar baki, wadannan an yarda ka shiga ba tare da neman izni ba.
Hikimar tsara wannan ka’ida ta yin sallama da neman izini kafin a shiga gida abu ne da ke sarari Allah Ya ce: “Allah Ya sanya muku gidajenku ne domin ku natsu ku huta.” Ke nan idan Allah Ya sanya gida ya zamo wurin natsuwa da hutawa da jin dadi ba za a samu wannan jin dadi ba tare da cikakken ’yancin sakewa ga mai gidan ba. Mai gida ko mazauna gida kamar miji da mata suna iya sanya suturar da za su samu iska ta rika ratsa jikinsu a gidanjensu, kuma ba za su so a gan su a irin wannan yanayi ba.
Sai ya kara da cewa: “Don haka duk wata kutsawa daga waje da za ta rusa wannan natsuwa da jin dadi, Musulunci ya hana ta. Musulunci bai amince da kutsawa cikin ’yancin wadansu ba, domin kutsawar tana iya cutar da wadannan mutane da gangan kuma haka haram ne.”
Na tabbata da za mu kiyaye wannan ka’ida ta yin sallama da neman izini kafin mu shiga gida za mu kawar tare da magance matsaloli da dama da suka shafi zamantakewarmu. Amma abin mamaki galibi yanzu sai ka ga mutum sai ya kutsa kai cikin gida zai yi sallama ga mutanen gidan, alhali yana iya iske mazauna gidan a yananyin da bai dace ba, musamman iyayenmu mata. Don haka ya wajaba mu sabar wa kanmu da ’ya’yanmu aiki da wannan kyakkyawar koyarwa ta addinin Musulunci. Kada mu yarda mu rika shiga gidajen ’yan uwa ko abokanmu ba tare da neman izini ba. Mu kokarta mu rika cewa “in shigo” bayan mun yi sallama an amsa mana. Haka mu saba wa ’ya’yanmu su taso da dabi’ar yin sallama da neman izinin shiga gida a koyaushe, amma sai ka ga yara suna fadowa cikin gida wadansu har cikin dakunamu ba tare da sun yi sallama balle neman izini ba.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1115; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: ***.*14.6.229; associated: 4- /*}