Topic: Bayani Kan Azumin Watan Rajab - Fadakarwa
Timeline: 2012-06-19 02:30:56
Bayani Kan Azumin Watan Rajab - Fadakarwa
A Rubuce Da Auwal Zakari Ayagi
Da sunan Allah Mai yawan rahama Mai yawan jinkai, gaisuwa da yabo su tabbata ga Ma’aikin Allah (SAW) da alayensa da shabbansa baki daya. Bayan haka, azumin Rajab sunna ne daga cikin sunnonin da Annabi (SAW) ya kwadaitar da yin sa, kamar yadda ya tabbata a hadisin Mujibatul Bahiliyya.
Amma kafin mu shiga cikin wannan maudu’i, zan so ’yan uwa su fahimci wasu abubuwa kamar haka:
Sunnar Annabi (SAW) tana nufin duk wani abu da aka jingina shi ga annabi (SAW), magana ce ko aiki, ko tabbatar da wani aiki da wani daga cikin sahabbansa ya yi ta hanyar yaba masa ko yin shiru a kai.
Akwai sunnonin da ambatonsu ke zuwa karara kamar falalar yawaita azumin Sha’aban da na Litinin da Alhamis da sauransu, akwai kuma sunnonin da ambatonsu ke zuwa a dunkule kamar azumtar watanni masu alfarma.
Wato watannin Zul-kida da Zul- Hajji da Muharram da kuma Rajab, kamar yadda Imam Ahmad ya kawo a Musnad da Abu Dawud da Ibnu Majah da Baihaki.
Idan muka dubi gabar karshe wato azumtar watanni masu alfarma za mu ga Hadisin ya tabbata da isanadi ingantacce kuma Alhafiz Ibnu Hajar ya tabbatar da ingancinsa a “Tabyinul Ajab” cewa: “Wani mutum ya zo wurin Annabi SAW), ya ce ya Rasululluhi ni ne mutumin da na zo maka shekarar da ta wuce (Annabi (SAW) bai gane shi ba), sai (SAW) ya ce na ga ka canja duk ka rame? Sai ya ce: “Ya Rasulullahi tunda na zo wurinka ban kara cin abinci da rana ba, domin ina ta yin Azumi. Sai Annabi (SAW) ya ce amma ka ba kanka wahala, ka azumci Ramadan, bayansa kuma a kowane wata ka yi azumi daya. Sai mutumin ya ce Ya Rasulullahi ka kara min ina da karfin da zan yi fiye da haka. Sai Annabi (SAW) ya ce bayan ka azumci watan Ramadan, to a kowane wata sai ka azumci ranaku biyu. Sai ya kara cewa Ya Rasulullahi a kara min ina da karfi. Sai Annabi (SAW) ya ce ka azumci ranaku masu alfarma sai ka bar shi haka. Annabi (SAW) yana nuni da hannunsa idan ya dunkule su sai ya bude. Wannan Hadisi hasanun ne kamar yadda Ibnu Hajar ya kawo a littafinsa Tabiyunil Ajab).
Sayyid Sabik ya fada a Fikhus-Sunnah kan azumtar watanni masu alfarma, cewa: “ana so a yawaita azumi a cikinsu sai ya kafa hujja da Hadisin Bahili wanda muka ambata a baya, sannan ya ce azumin watan Rajab ba ya da wata falala da ta wuce wannan inganci bisa bayani mabayyani. Shi dai Rajab yana cikin watanni masu alfarma.” (Fikihun Hadisi).
A cikin wannan Hadisi na Bahili za a iya fahimtar abubuwa kamar haka:
Yadda sahabbai suke tasirantuwa da zama da Annabi (SAW), domin shi wannan Sahabi ya zo wurin Annabi (SAW) ne a shekarar farko da ya kwankwadi madarar imani, zuciyarsa ta tsarkaka tunda ya je wurin Annabi (SAW) bai kara cin abinci da rana ba, sai ya lazimci yin azumi.
Yadda Annabi (SAW) yake tausasa wa al’umma, domin ya ga yadda wannan sahabi ya canja har bai gan shi ba, shi ya sa ya hana shi wannan azumi.
Hani karara bisa azumin da zai galabaitar da mutum ya wahalar da shi.
Umarni da kwadaitarwa bisa azumin da mutum zai iya bayan na Ramadan:
Yin azumi yana danganta da irin yanayin mutum ne, wanda zai iya da yawa domin yana da lafiya da karfin yi, wanda kuma ba zai iya ba, shari’a ta yi masa rangwame.
Annabi (SAW) ya umarci da ya azumci Ramadan da watanni masu alfarma idan muka hada za mu ga a shekara zai iya yin azumin wata hudu.
Akwai hujja kan azumtar Rajab gaba dayansa ga mai iko cikin wannan Hadisi, domin Annabi (SAW) cewa ya yi da shi ka azumci watanni masu alfarma kamar yadda ya tabbata a Hadisin, tunda babu wani nassi ingantacce da ya fito karara ya hana azumin watan Rajab. Ba wannan hadisi kadai ne ya yi magana kan falala da hujjar azumtar Rajab ba, a’a akwai hadisin korama da gida da ke magana kan gidan da Allah Ya tanadar wa masu azumtar Rajab da sauransu, duk da cewa akwai wadanda ba su inganta ba a cikin hadisan kamar yadda Alhafiz Ibnu Hajar Al’askalani ya fada cikin Tabiyinul Ajab sai dai akwai tsokaci a nan, tsokacin kuwa shi ne, shi Hadisi Da’if ana aiki da shi wajen ayyukan neman falala (kamar a zumin Rajab din), ko tabbatar da matsayi da daraja ga wani daga bayin Allah, ko kwadaitarwa kan wani lamari da shari’a take umarni ko tsoratarwa, kai aikata wani abu da ta yi hani da shi. Wannan magana malaman Hadisi sun hadu a kan haka kamar yadda Imam Nawawi ya kawo cikin littafinsa Ibahatul kiyam.
Daga malaman da suka tabbatar da haka akwai Imamu Ahlus Sunna Ahmad Ibnu Hambali da Imam Ibnu Sayyidi-Nas da Imam Al-irakiy da Shaihul Islam Zakariyyal Ansari da Imam Shakkhawi da Alhafiz Ibnu Hajar Al-Askalani da Imam Ibnu Humam Al-Hanafiy da Imam Ibnu Adiy da Imam Khadib Albagadadi da sauransu.
Fadakarwa:
Ya kamata mu san cewa azumin Rajab da ake ce wa azumin tsofaffi ba ana nufin sai tsoho ba ne zai yi, azumin Rajab na duk Musulmi ne mai son alheri da falala, shi wannan suna ya samo asali ne domin ’ya’yan Hausawa sun taso sun ga iyayensu da kakanninsu suna yi, sai suka sa masa wannan suna, kamar yadda suke kiran azmin Ramadan da azumin duk gari. Ai ka ga a garin akwai wadanda ba Musulmi ba, a Musulmin ma akwai wadanda shari’a ta yi musu rangwame kamar marasa lafiya da tsofaffi da masu jinin haila ko na biki da masu shayarwa ko goyon ciki idan azumin zai wahalar da su ko ba za su iya ba.
Lallai ya kamata kamar yadda muke azumtar watan Rajab mu rika azumtar Sha’aban haka ko fiye da shi, domin ya tabbata a hadisin Buhari da Muslim cewa Nana A’isha ta ce: “Annabi (SAW) yana azumtar kusan dukkan Sha’aban,” amma sai ka ga ’yan uwa suna rafkana ana gama Rajab sai a daina. A’a haka ba daidai ba ne.
Hakan nan akwai azumi da yawa da ya tabbata daga Ma’aiki (SAW) kamar azumin ranar Litinin da Alhamis da azumin ranakun 13 da 14 da 15 na kowane wata da azumtar kwanaki shida a Shawwal da kwanaki 10 na Muharram da na ranar Tasu’a da Ashura, da azumin Annabi Dawud (AS), wato yau ka yi, gobe ka sha da azumin gwauraye wato wadanda ba su samu damar yin aure ba da sauransu.
Domin Annabi (Alaihis Salam) ya ce: “Wanda ya azumci wani yini domin neman yardar Ubangiji, Allah (SWT) zai nesanta fuskarsa daga wutar Jahannama na tsawon shekara daya.”
Allah Ya ba mu dacewa, Ya karbi dukkan ibadunmu don alfarmar shugaban masu azumi (SAW).
Wassalamu alaikum warahamatullah.
Auwal Zakari Ayagi
Shugaban kungiyar Al’azmiyya Islamic Foundation, Kano
08090987314
Email: alzamiyya@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 1268; topic series: 7; forum: MediaHausa; associated: 7- /*}