Topic: Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (1)
Timeline: 2012-06-19 02:33:16
Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (1)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Gabatarwa: Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka ganin an fara shirye-shiryen tafiya aikin Hajjin bana da kuma yadda mutane da dama suke zuwa aikin Hajjin ba tare da sanin hukunce-hukuncensa ba, ya sa muke gabatar da wannan rubutu daga littafin Fatawoyin Aikin Hajji Da Umara Da Ziyara A Kan Koyarwar Alkur’ani Da Sunnah Bisa Fahimtar Magabata Na kwarai na Sheikh Abdulwahhab Abdullah na Majlisin Ahlus Sunnah Wal- Jama’ah, Masallacin Ibnu Taimiyyah da ke Sharada Phase II, Kano.
Muna fata wadannan fatawoyi za su taimaka ga masu niyyar zuwa aikin Hajji ta yadda za a samu bambanci tsakanin zuwa aikin Hajji a matsayinsa na ibada da kuma zuwa yawon bude ido da jama’a da dama ke yi.
Allah Ya taimake mu, amin.
Tambaya ta 1: Mene ne ma’anar Hajji?
Amsa: Ma’anar Hajji a harshen Larabci shi ne nufin wani abu. Amma a shari’ance shi ne nufin ziyarar dakin Allah (Ka’aba), bisa girmamawa da aikata wasu kebantattun ayyuka (na ibada) a kebantaccen zamani, kuma a wani kebantaccen wuri.
Tambaya ta 2: Mene ne falalar aikin Hajji?
Amsa: Aikin Hajji yana da falala da yawa. Kadan daga ciki shi ne: Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Aikin Umra zuwa wata Umrar, yana kankare zunuban da ke tsakaninsu. Haka kuma Hajji mabrur, ba ya da sakamako sai aljanna.” Sahihul Buhari: Kitabul Umrati, Babu Wujubil Umrati Wa Fadliha, Hadisi na 1773, da Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Fadlil Hajji Wal Umrati, Hadisi na 1349.
Haka kuma an karbo daga Ma’iz ya ce: “Anc tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: Wadanne ayyuka ne suka fi falala? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yin imani da Allah Shi kadai da yin yaki domin daukaka addinin Allah, sannan Hajjin da ya kubuta daga sabo. Fiffikon da ke tsakanin Hajji mabrur da sauran ayyuka kuma, kamar fiffikon da ke tsakanin mahudar rana ce da mafadarta.” Sahīh at-Targhib wat-Tarhīb na Munzirī, tahkikin Sheikh Albani (2/1103).
Hajju mabrur shi ne Hajjin da ya kubuta daga sabo.
A duba littafin Taudhihul Ahkam: na Sheikh Bassam, Juz’i na uku, shafi na 255.
Sharudansa kuma su ne kamar haka:
1. Ya zama an yi shi da ikhlasi.
2. Da dukiya ta halal.
3. Ya zama aikin da zai nuna ibada ake yi ba son zuciya ba.
4. Da nisantar aikata dukkan laifuf*****a a cikinsa.
A duba littafin Fathu Zil Jalali Wal Ikram: Na Sheikh Usaimin, Juz’i na 3, shafi na 322-323.
A cikin wani hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Umar (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mai yaki fisabilillahi da mai aikin Hajji da mai Umra dukkanninsu tawagar (bakin) Allah ne. Allah ne Ya kira su, kuma suka amsa maSa, kuma suka roke shi, Ya ba su (abin da suka roke shi). Sahih at-Targhib wat-Tarhib (2/1108) da Sahih Ibnu Hibban Bi Tartibi Ibn Balban: Tahkikin Shu’aib Arna’ud (9/3692)
Haka kuma, an karbo daga Nana Ā’isha (RA) ta ce: “Na ce wa Manzon Allah (SAW): Shin ko jihadi ya wajaba a kan mata? Sai ya ce: Na’am, mata suna jihadi, sai dai babu kisa a cikinsa; shi ne aikin Hajji da Umra. Sunan Ibnu Majah: Kitabul Manasik, Babul Hajju Jihadun Nisa’i, hadisi na 2901, kuma Sheikh Albani ya inganta shi da wannan isnadin, sannan Imam Buhari ya ruwaito ma’anarsa a cikin Kitabul Jihad, Babin Jihadin Nisa’i, hadisi na 2875
Tambaya ta 3: Yaushe aikin Hajji yake wajaba a kan mutum?
Amsa: Aikin Hajji yana wajaba ne a kan mutum idan Allah Ya ba shi iko. Iko shi ne: dukiya da lafiya da amincin hanya da guzuri. Saboda Ubangiji Yana cewa: “Hakkin Allah ne a kan mutane su hajjanci dakin (Ka’aba), ga wanda yake da ikon zuwa…” Al-Imran: aya ta 977.
Tambaya ta 4: Shin wajibi ne ga wanda Allah Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji ya gaggauta tafiya ko kuwa zai iya jinkirtawa zuwa wani lokaci?
Amsa: Hakika wanda Ubangiji (SWT) Ya ba shi damar aikin Hajji, wajibi ne ya gaggauta tafiya matukar babu wani uzuri da zai hana shi. Kuma koda yake an samu sabanin malamai a kan haka, amma wannan shi ne abin da mafi rinjayen malamai suka tafi a kai. Daga cikin sahabbai da suka tafi a kan haka akwai Abdullahi Ibnu Abbas da Abdullahi Ibnu Umar (RA). Haka ma Imam Malik da Imam Ahmad da Imam Abu Hanifa da Abu Yusuf duk matsayinsu ke nan. Koda yake Imam Malik yana da fatawoyi guda biyu a kai, amma wannan ita ce mafi rinjaye. Duba al-Mukni Sharh Kabīr na Ibn kudama Al-Makdisy tahkikin Abu Muhsin Atturki, 8/50-52.
Dalili kuwa shi ne fadinSa (SWT) cewa: “Ku yi gaggauwa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku…” Al-Imran: aya ta 133 da kuma fadinsSa (SWT) cewa: “Kuma ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri…” Ma’ida: aya ta 48.
Kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Abbas (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya yi nufin tafiya Hajji, to, ya gaggauta. Hakika rashin lafiya zai iya samunsa, ko dabbar ta bata, ko kuma wata bukata ta bijiro masa.”
A cikin wata ruwayar, Abdullahi Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Ku gaggauta zuwa Hajji (na farilla); hakika daya daga cikinku bai san me zai bijiro masa ba. Duk wadannan hanyoyi guda biyu Ahmad Shakir ya raunana su. Ya ce a cikin isnadin Hadisin akwai Isma’il Ibnu Khalifa Abu-Isra’il wanda da’ifi ne, ba a kafa hujja da Hadisinsa, domin ya kasance dan Shi’an mai tsattsauran ra’ayi. A cikin littafin at-Takrib, Ibnu Hajar ya ce: Sudukun ne yana da mummunar hadda (su’ul hifz). A cikin isnadin ruwaya ta biyu, akwai Mahram Abu Safwan wanda majhuli ne. Abu Zur’ah ya ce ba a san shi ba. Duba Musnad na Imam Ahmad, tahkikin Ahmad Muhammad Shakir (1833 da 1834). Amma duk da haka, Sheikh Albani ya ce Hadisin hasanun ne ida aka hada hanyoyinsa, kuma za a iya kafa hujja da shi. Duba Sunan Ibn Majah: Kitabul Manasik, Babul Khuruji Ilal Hajji, hadisi na 2883 da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, babi na biyar, hadisi na 1732 da kuma Irwa’ul Ghalil: Juz’i na hudu, shafi na 168, hadisi na 990. Haka kuma Hadisin ya zo a cikin Mishkatul Masabih: Juz’i na biyu, shafi na 772, Hadisi na 2523 da kuma Sahih Targhib (1111). Kuma Sheikh Albani ya inganta shi, a cikin Kitabul Hajji.
Wadannan ayoyi da hadisai da muka kawo su ne suke wajabta gaggauta zuwa Hajji, musamman a lafazinsu, ta yadda ya zo da umarni tare da kwadaitarwa.
**{Legacy activities, comments etc counter: 660; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}