Topic: Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (2)
Timeline: 2012-08-24 02:04:00
A Rubuce Da Malam Abdurrahman Ibrahim Idris
Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (2)
Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da aminici su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, yau za mu gabatar da vangare na biyu na laccar Ramadan da Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi da Qungiyar MSS suka shirya a makon farko na azumin bana. Wakilinmu Salihu Maqera ya halarci laccar kuma shi ya rubuta ta don amfanin makaranta wannan jarida. Bismillah: Muna farin ciki da aka samu wasu ’yan uwa suka tsaya don ganin an ci gaba da gudanar da wannan lacca ta azumi. Domin mafi alherin aiki, wanda aka tabbata a kai. Ko yaya aka yi, ya fi a ce ba a yi ba.
Alal haqiqa wannan maudu’i da aka ba mu, malami na gaba ya riga ya tsefe haqqinsa. Illa iyaka wani vangare zan xauka don a tafi yi aiki da wannan lacca da ya bayar.
Ramadan yana da tasiri qwarai da gaske wajen inganta tarbiyyar al’umma.
In an ce al’umma ana nufin jam’i ne na mutum, mutane da yawa su ne al’umma. Idan muka dubi Alqur’ani Mai girma, duk inda kalmar mutum ta zo, sai a ga an jingina ta da wani abu wanda yake ba mai kyau ba.
“Innal insana khuliqa halu’an. Iza massahu sharru jazu’an. Wa iza massahu khairu manu’an. Illal musallin…” Da “Wal asari innal insana lafi khusrin. Illallal lazina amanu wa amilus salihati, wa tawasau bil haqqi, wa tawasau bis sabari.” Duk ayar da za ka xauko a cikin Alqur’ani in ta ambaci kalmar mutum, za ka ga Allah da Ya halicce shi kawai ne Ya san shi.
To idan aka ce mutum, ana nufin kansa da abin da kai yake xauke da shi da cikinsa da abin da cikin yake xauke da shi da farjinsa da abin da farjin yake xauke da shi, sai kuma maxaukai wato hannuwa da qafa.
To, matuqar ba ka xauki maganin waxannan abubuwa gaba xaya ba, to, lallai ba za ka samu gyara tarbiyyar mutum ba.
Idan ka xauki gyara tarbiyyar cikinsa wajen sama masa abin da zai ci ya sha, in ka samu wannan ka gyara wani vangare ne na mutum, sauran vangarorin da ba ka gyara su ba, in ka ba su xan lokaci kaxan wannan da ka gyara za su lalata shi. Wannan shi ne babbar matsalar da muke samu wajen tarbiyyar al’umarmu, ba ma xaukar tarbiyyar nan a matsayin mutum gaba xayansa. Kullum sai mu xauki wani gefe muna tarbiyyantarwa mu bar wani gefe, gefen da muka barin kuma yana iya ruguza xaya gefen.
In mun xauki kan mutum alal misali, yana da Al’aqalul Mufakkira, wato hankalin da aikinsa kawai tunani ne. To dole a tanadi abubuwan da za su saita wannan tunani na hankali, ya yi daidai da shari’a da yadda Allah Yake so.
Yana kuma da Al’aqalul Hafiza, hankali mai kiyaye abubuwa, duk abin da ya rarumo a duniya, wanan hankalin zai kiyaye masa ya ajiye masa shi. Shi ya sa in ka zauna tsam, sai ka tuno abin da ka yi kana da shekara uku a duniya ba ka manta ba. Ko ka tuno wani abin da maqwabcinku ya yi kana da shekara uku, ko kuma wani lokacin da kake firamare ya yi ta dukanka, ko wani ya yi maka kyauta. To Al’aqalul Hafiza ita take kula da waxannan abubuwa.
Sannan akwai kuma Al’aqalul Mukhayyala, wadda kullum aikinta ta riqa kallo maka abubuwa tana suranta su tana xaukar hotonsu.
To, waxannan dukkansu akwai tarbiyoyi da aka tanada dominsu, ya zamo an tarbiyyantar da xaukacin kan mutum ya zamo yana da duk abin ake buqata.
Matuqar aka ce an xauki wani vangare ba a xauki wani ba, to sai an samu matsala.
Malami na gaba ya tavo abubuwan da suke tarbiyyantar da wannan tunani da ke cikin qwaqwalwar mutum. Alal misali Annabi (SAW) ya ce: “Duk mutumin da bai bar maganar zur ba, ba ruwan Allah da barin cinsa da shansa.” Ka ga ci da sha, wani azumi ne da ya shafi ciki kawai. To don ka bar ci da sha daga fitowar Alfijir zuwa faxuwar rana, akwai abubuwa da yawa da za a karanta maka cewa ba ruwan Allah da barin ci da shanka, kuma ba azumi ka yi ba.
Don haka an haxa waxannan batutuwa biyu ne, don mu san mene ne azumi kuma wane ne mutum, don mu san yaya za mu ci gajiyar tarbiyyar da azumin ke koyarwa.
Abubuwan da suka shafi raxa da zunxe da yi da mutane da qarya da annamimaci da riya da sauransu, duk in mutum bai guje su a wannan wata ba, to ba azumi ya yi ba, ya yi azumi ne na ciki kawai bai yi na tunaninsa ba.
Ya kamata duk mai azumi ya zauna ya hana tunaninsa daga tunato masa abubuwan banza na vata mutane. Kada Hafizar nan ta ajiye masa abubwan banza da za su riqa gurvata masa ibadarsa. Kada Mukhayyalar nan ta qirqiro masa wasu hotuna na banza ta ajiye masa a gaba yana gani, su vata masa azumi ba tare da ya sani ba.
Saboda haka, Allah Ya ce: “Azumi Nawa ne, kuma Ni zan saka a kansa.” Yadda mutum yake na Allah ne, wanda ban da Allah da Ya halicce shi, ba wanda ya san shi, haka azumi yake na Allah ne.
In ban da Allah da Ya ce a yi azumi, ba wanda ya san abin da ke ciki na gyara xan Adam. Don haka ba wani wata da aka tanada don gyara tarbiyyar xan Adam irinsa.
Babban abin da ke vata mutum shi ne ransa, “Annafsu.” Wani mawaqi yana cewa: “Wa khalifunnafsa wasshaixana wa asihuma….” Ma’ana ranka da kake da shi da Shaixan ya zamo koyaushe sava musu kake yi. In suka ce ga abin da suke so ka ce, ba ka so. Duk abin da suka ce ba sa so, ka ce shi kake so. Sai in ka ga abin nan ya zo daidai da shari’a, Allah Ya ce, a yi, Annabi (SAW) ya ce, a yi.
Kuma halin rai da Shaixan shi ne, in suka ga ba za ka faxa ta hagu ba, sai su dawo maka ta dama, yadda Allah Ya ce, Annabi (SAW) ya ce, amma ka yi su fiye da yadda shari’a ta ce, wai kai mai qoqari.
Saboda haka dole ne a sava wa rai a sava wa Shaixan.
Abu na uku wanda ake sava masa a samu zaman lafiya a cikin azumi shi ne, jama’ar nan da kake tare da su. Hira cikin jama’a yana daga cikin abin da yake gurvata azumin mutane da yawa. Azumi wani wata ne da ake son mutum ya kevance kansa ya shagala da kansa, ya koyi tarbiyya tagari a cikin wannan wata. Ka ga ya samu makaranta ke nan cikin zuciyarsa. Wannan qwaqwalwa Hafiza abin da ya samu cikin azumi na alheri ko bayan azumi sai ya zamo shi kaxai ne abin da ta xauka. Amma in kana hulxa da hira da mutane, sai nasu abubuwan su riqa shigo maka, in sun shigo ba za a samu ingantacciyar tarbiyya ba.
Abu na gaba in an kiyaye kai, dole a kiyaye ciki. A gaskiya ba wai ci da sha a qoshi kawai ake nufi ba.
Na farko ana so a azumin nan ka tarbiyyanci kanka da cin halal. Wata ne guda xaya, in a sauran watanni ka yi karume-karume, duk abin da za ka sa a bakinka ko za ka kawo wa iyalinka a wanan wata ka tabbatar halal ne. Tarbiyya ce ake so a gina maka na cin halal. Ba abinci ne yake qosar da mutane ba, kuma ba kyaun abinci ne ke sa daxin abinci a bakin mutane ba, halal ce. Za ka ci miyan kuka ka ji daxi, wani zai ci kaza ko xawisu, farfesunsu, amma wallahi hankalinsa bai kwanta ba. Kuma ya ci fiye da qima bai ji ya qoshi ba.
Ka tabbatar duk abin da za ka ci a wanan wata halal ne, kuxin nan ka san asalinsa, ka san yadda ya shigo, abin da ka saya ka san irin cinikin da ka yi, ba ciniki ne don kana buqatar abu ka saya ka ce sa min gyara, ka sa shi dole don kunyarka dole ya sa maka gyara, to wannan gyara sai ya gurvata maka abinci! A yi ciniki na kirki, a tabbatar abubuwan da ake ci a wannan wata na Ramadan halal ne. mutum ya ga tarbiyyarsa ta canja wajen cin sad a ciyar da gidansa. Wannan yana da matuqar muhimmanci.
**{Legacy activities, comments etc counter: 496; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}