Topic: Shugaba Jonathan : Kyan Alkawari ...: Dimokuradiyya Tsantsa
Timeline: 2010-11-18 16:05:05
]Shugaba Jonathan : Kyan Alkawari ...: Dimokuradiyya Tsantsa
A Rubuce Da Shehu Mustapha Chaji
Da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya amfani shawarwarin da mafi yawan ’yan Najeriya suka ba shi na kin shiga zaben shekara ta 2011 a matsayin dan takara da kasar ba ta shiga halin rudani da tsaka-mai-wuya da ta sami kanta a ciki a yanzu ba.Tun kafin ma ya fito karara ya nuna aniyarsa ta tsayawa takara, kawunan ’yan kasa ya rabu tsakanin ’yan Kudu da Arewa.
A shekarar 1999 da sojoji za su mika ragamar mulki ga farar hula, ’yan siyasa a lokacin suka amince su ba wa ’yan Kudancin Najeriya damar su fitar da shugaban kasa daga sashin. Saboda su huce fushin abin da da gwamnatin tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ta jefa kasar saboda rushe zaben 12 ga watan Juni na shekara ta 1993 inda ake kyautata zaton marigayi Cif M.K.O Abiola ne ya lashe zaben.
A zaben na 1999 Cif Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP da Cif Olu Falae na APP/AD kadai suka tsaya takarar neman shugabancin kasa. Yadda jam’iyyar PDP ta tsara karba karba tsakanin Kudanci da Arewacin Najeriya a matsayin doka. Shi ne sashin Kudu za su yi shekaru takwas sannan Arewaci su ma su dana har na tsawon shekaru takwas.
Bayan rasuwar Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar ’aduwa ne, aka rantsar da mataimakinsa Dokta Goodluck Jonathan a matsayin Shugaban kasa. Sabanin tunanin mafi yawan ’yan Najeriya inda suka zaci Jonathan zai mayar da hankali a kan alkawuran da gwamnatinsu ta dauka kamar kudurori bakwai, sai kawai ya fito karara ya nuna cewa kundun tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar tsayawa takara, duk da masu kira a kan kar ya tsaya takara sun fito sun yi nuni da cewa a gabansa aka tsara daftari tsarin shugabancin jam’iyya a lokacin yana mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.
Idan muka yi waiwaye,wanda masu iya magana ke cewa adon tafiya, a shekarar ta 1976 da aka kashe marigayi Janar Murtala Muhammad lokacin Janar Olusegun Obasanjo ne ya gaje shi. Duk da cewa tsarin mulkin kasa ya ba shi dama na iya kwabe kakinsa ya shiga takara, bai yi haka ba, saboda mutuntaka. Haka a shekarar 1999 da Janar Abdulsalam Abubakar zai mika mulki ga farar hula, shi ma bai nuna zalama da karanta ba, ko ya fake da zancen tsarin mulkin kasa ya ba shi dama ya tsaya takara ba.
Shi ya sa masu nazari kan siyasar Najeriya ke ganin cewa shi ma shugaba Jonathan, duk da dokar kasa ta ba shi damar tsayawa takara, amma tunda akwai doka da ta gitta, shi ma ya kamata ya hakura da takara ya mayar da hankali wajen gudanar da ingantattcen zabe.
Wasu ’yan Najeriya na ganin bai ma kamata shugaba Jonathan ya nemi takara ba, tunda su a ganin su, babu wasu ayyuka na cigaba da inganta rayuwar talaka da za a ce kai tsaye talakawa sun amfana da shi.
’Yan Arewacin Najeriya na korafin cewa shugaba Jonathan na dakile ayyukan da za su kai yankin su ga cigaba kamar yin kafar angulu a kan maganar yashe kogin Neja, da dakatar da aiki titunan jiragen kasa da cire ’yan yankin daga muhimman mukamai yana maye su da wasu daga yankin da ya fito ko zuwa wani bangaren. Sannan-uwa uba rawar da suke zargin sa da takawa wajen kare kungiyar MEND da ta dauki alhakin kai tagwayen hare-hare a birnin Abuja, duk da sun fito sun yi ikirarin haka. Sannan tsohon madugun kungiyar MEND, a hirar da tashar talabijin ta Aljazira ta yi da shi ya ce, wani na hannun daman shugaba Jonathan ya nemi ya yi wa kuniyar MEND bayanin cewa su ce babu hannunsu a harin sannan ya ce wasu ’yan Arewa ne ke bayan harin. A takaice wasu ’yan Arewa na ganin mulkin shugaba Jonathan ya fi karkata zuwa wani bangare na kasar sannan bai dauki dukkan al’ummar Najeriya a matsayin jama’ar saba.
Har yanzu lokaci bai kure ba, Shugaba Jonathan ya girmama kundin tsarin mulkin jam’iyyarsa ta PDP, cewa mulki za ya koma Arewa a zaben 2011 don za ta tsayar da dan takara daga Arewa. Najeriya kasa ce mai tarin kabilu da addinai da ra’ayoyi mabambanta, saboda haka tsarin karba-karba tsari ne da ke taimakawa wajen dunkulewan kasar a matsayin al’umma daya. In kuma har ya dage sai ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP, sai ayyukansa a fannin cigaban kasa su fitar da shi.
’Yan Najeriya na ganin abin da ya fi dacewa shi ne, Shugaba Jonathan ya hakura da takara zuwa nan gaba don ya sami damar gudanar da zabe da mafi yawan ’yan Najeriya za su amince da shi. Ko ba komai dattijantaka da mutumntaka na cika ne in babba ya kasance mai cika alkawari. ’Yan jam’iyyarsa ta PDP na da dama ko su amince masa ya tsaya takara ko kuma su nemi ya girmama tsarin karba-karba da suke kan ta tun shekarar 1999.
Shehu Mustapha Chaji shehuchaji@yahoo.com 08038222575
Dimokuradiyya tsantsa
Daga Buhari Daure Daura, Jihar Katsina
Duk mai bibiyar harkokin siyasa a Nijeriya, ya san yadda maganar karba-karba ta cika ko’ina har aka manta da muhimman abubuwan da suka shafi kasa ta fuskar ci gaba, kamar talauci da ilimi da rashin tsaro da sauransu, duk da cewa laifin shugabanni da masu fada a ji a PDP na Arewacin kasar nan ne.
PDP ba ta mayar da hankali ba wajen ganin an gamsar da mabiya, musamman ‘ya’yan jam’iyyar a nan Arewa. Shi ya sa babu dan takarar da ya kai shugaban Jonathan kima da kwarjini a PDP a jajiberin zaben 2011.
A sherkara ta 1990 mutanen Kudu sun tada kayar baya, musamman ganin cewa sai an mayar da mulki hannunsu, don a share masu hawaye game da gwagwarmayar da suka sha a zaben da aka soke na 12 ga watan Yuni. Bayan mutuwar Janar Sani Abacha, Shugaba Janar Abdulsalamu Abubakar, tare da hadin kan wasu manyan ‘yan siyasa da jami’an Arewa suka ba da goyon bayan ya dare kan karagar mulkin kasa. Ya ba da mulki ga mutanen Kudu musamman Yarabawa.
Bayan an kafa jam’iyyun PDP da AD da APP daga baya ta rikida ta zama ANPP, duk suka amince da cewa a bar wa Kudu kuma Kirista. PDP ta gabatar da Cif Olusegun Obasanjo a matsayin dan takararta, APP da AD suka yi hadin gwiwa suka gabatar da Cif Olu Falae a matsayin da takararsu. Zaben shekara ta 1999 ya zama kamar wani gwajin dimokuradiyya, inda aka bar wa Kudu su ci gajiyar. Bisa yarjejeniyar cewa nan gaba za a dawo da mulki Arewa domin a ci gaba da dinke barakar da ke neman bullowa tsakanin kabilu da mutane masu addinai mabambanta.
Kafin zaben shekara ta2007,PDP ta amince da tsarin karba-karba. Bayan shekaru takwas a ba dan Arewa shugabanci, Kudu maso Yamma sun ci moriyar wannan yarjejeniya, ga shi Arewa na nema su rasa wannan dama, a rasuwar marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa wanda bai cike shekaru hudu cif-cif ba.
Hakan ya sa wasu daga Arewa suka yi fatan mulki ya kara shekaru hudu a Arewa a zaben shekara ta 2011 mai zuwa, amma hakan na da kamar wuya, don buri da son kai da kwadayin wasu ‘yan siyasa daga Arewa.
Wani abin mamaki game da kasar nan shi ne ko an ki ko an so, karba-karba ya zama tsarin rayuwar kasar, don ba wanda ya taba tsayawa takara ya dauko kanensa ko dan uwansa ko dan jiharsa ko kabilarsa a mastayin mataimakinsa. Shin me ya sa ake kewaya shugabancin kungiyoyin kwadago da kungiyoyin dalibai na kasa a tsakanin ‘yan Arewa da Kudu? Ko bayan wannnan zaben, duk wanda ya ci zai ba dan wata kabila ko dan wani addini.
Duk da cewa a lokacin da Kakakin Majalisar Tarayya, Alhaji Salisu Buhari, aka maye gurbinsa da wani dan Arewa Alhaji Ghali Umar Na’abba. Sannan da aka sauke Shugaban Majalisar Cif Ebans Enwerem da Dokta Chuba Okadibgo da Chief Anyim Pius Ayim da Chief Adolphus Wabara da Cif Ken Nnamani duk dan Kudu maso Gabas yake hawa a madadin dan uwansa. Kai ko a lokacin da aka cire mace ta farko da ta zama Kakakin Majalisar Patricia Etteh ai dan uwanta aka dauko daga Kudu maso Yamma watau kakakin yanzu Alhaji Dimeji Bankole.
Wannan abin bai tsaya a kan zababbu ba, ko masu jan ragamar PDP sun fuskanci irin wannan tukin. A lokacin da aka sauke Yarima bincent Ogulafor dan uwansa aka ba shugabancin jam’iyyar watau sabon ciyaman na PDP Cif Okwesilizie Nwodo, kuma mataimakin Yarima bai zama Sarki ba. Rai ya yi halinsa, ya tabbatar da Jonathan ya gaji Umaru. Don haka kundin tsarin mulki ya tanada, idan ma ana son yin wani gyara a kundin za a iya yi, ba a ci gaba da cece-kuce, ana ta yin dimokuradiyya a cikin duhu ba.
Sannan a wani bangaren duk da cewa maganar karba-karba abu ne da ya shafi shugabancin jam’iyya, kowa na damar yin tsokaci, musamman ‘ya’yan jam’iyya na da damar yin tsokaci game da abin da ya shafi uwar gijiyarsu. Don idan rashin lafiya ya kama uwar, za su nemo mata magani, Hausawa kan ce shure-shure ba ya hana mutuwa.
Hakan ba zai hana ‘yan Arewa tofa albarkacin bakinsu ba, game da wanda suke son ya jagaroancin jam’iyyar a zaben 2011. Kowa ya sani ‘yan Arewa na da ra’ayin sai dan Arewa,wannan ra’ayin sai dan Arewa na wasu tsiraru ne wadanda ba sa son ci gaban kasar. Sai dai duk lokacin da iskar zabe ta fara kadawa sai su rika maganar Arewa ko Musulunci, bayan Arewan nan ta fi ko’ina talauci da koma baya ta kowane fanni.
Jami’o’i nawa da Farfesoshi nawa ne a Arewa? Kamfanoni nawa suke aiki? Asibitoci nawa ake samun magunguna? dakunan karatu nawa za ka iske littattafan karatu? Idan dai da gaske ’yan Arewa suna son mulki ya koma Arewa, akwai dama! Ai mutum ake yi ba jam’iyya ba, me zai hana a fito da mutum daya tsakanin Janar Aliyu Gusau da Alhaji Atiku Abubakar da Janar Babangida da Janar Buhari da Malam Shekarau, idan mulki bai dawo Arewa ba.
Yin haka ba tare da tsarin karba-karba, shi ne dimokuradiyya tsantsa, tun da Shugaba Jonathan yana da damar tsayawa takara a matsayinsa na dan kasa. Lokaci ne da ya kamata mu tabbatar da cewa siyasa ba sarauta ba ce. Manya na son ‘ya’ya su gaje su, sai a fake da ‘yancin Arewa ko Musulunci. Har yanzu akan hau dawakan kara a Arewa. Hausawa kan ce shure-shure ba ya hana mutuwa!
[Buhari Daure Daura, Jihar Katsina.
buharidaure@ymail.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 2347; topic series: 6; forum: MediaHausa; legacy score: 10; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 6- /*}