Topic: Matsayin gemu a Musulunci (4)
Timeline: 2012-03-27 19:11:12
Matsayin gemu a Musulunci (4)
A Rubuce Da Ahmad Muhammad
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Ga ci gaban tsokaci kan matsayin gemu:
Bari kuma mu duba wadansu amsoshin tambayoyi dangane da sha’anin aske gemu domin mu kara ganin irin muhimmancin da ke tare da shi, musamman don kara natsuwa cewa tsayar da shi wani hukunci ne mai zaman kansa a addini, wanda yake wajibi. Allah Ya yi mana gam-da-katar wajen aiwatar da umurnin addini, kamar yadda Allah Yake so kuma Ya yarda, ta fuskar bin sunnar ManzonSa, sallallaahu alaihi wasallam.
Tambaya: Ina aiki a wani kamfani, shugabana, wanda kan bari in je kowace sallah a masallaci, ya umurce ni da in rage gemuna (ba in aske shi ba) ko kuma in bar aikin. Mane ne hukuncin rage gemun nawa?
Amsa: Godiya ta tabbata ga Allah. Farko dai aske gemu haram ne, kamar yadda datse shi ko rage shi yake haram, saboda hujja wadda ta nuna wajibcin kyale shi da barin shi ya bunkasa. A Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah (5/133) an ce, “Aske gemu haram ne saboda sahihan hadisai da rahotanni da aka ruwaito dangane da haka. Sannan kuma da gama-garin ma’anar da ke kunshe a ciki, wadda ke nuna haramcin kamantuwa da kafirai. Hada da hadisin dan Umar, wanda ya ce Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam ya ce, “Ku yi bamban da mushrikai, ku bar gemunku ya yadu, kuma ku rage gashin baki.” Ibn Hazam ya ruwaito cewa ijma’in malamai ya nuna datse gashin baki da barin gemu ya yadu wajibi ne. Sai ya kawo hadisin da ya gabata da kuma na Zaydu dan Arkam, inda Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, ya ce, “Wanda duk bai datse gashin bakinsa ba, ba ya cikinmu.” Hadisi sahihi inji Attirmiziy. An fada a littafin Alfuroo’, kamar yadda “sahabbanmu – Hambalawa – suka bayyana, wannan na nunin cewa haram ne.”
Bayan wancan hadisi na la’ana ta kamantuwa da ta gabata da kuma shaida a kan hadisin da aka ruwaito, akwai kuma wata shaidar daga hadisin Abiy Hurairata, Allah Ya yarda da shi, daga wajen Ibnu Asaakir (1/166) da kuma Ibnu Maajah (1903).
Wata shaidar kuma ta uku a jerin, ta fito ne daga hadisin Ibnu Umar, Allah Ya yarda da su, cikin Juz’inis Shaamuukhiy (17).
Malam (Albaaniy, a sharhin da yake wa wancan hadisi da su Bukhariy suka ruwaito) ya ci gaba da cewa: “Yana daga abin da babu shakka a cikinsa – ga wanda dabi’ar dan Adamtakarsa ta kubuta (daga zargi) kuma tsayuwarsa (a kan bin dokar addini) ta yi kyau, cewa kowane dalili daga wadannan dalilai (hadisai) guda hudu, yana isa wajen tabbatar da wajibcin yalwata gemu da kuma haramcin aske shi. To bare kuma in an hade dalilan dukansu?
Haka nan da wannan ne Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce, “kuma askewar gemu ya haramta”, haka maganar take a littafin Alkawaakibul Daraariy (2/101/1). Kuma Ibnu Asaakir ya ruwaito (2/101/13) daga Umar dan Abdul’aziiz cewa aske gemu muthlah (kwaikwayo, kamanci) ne, kuma sai ya ce “lallai Ma’aiki, sallallaahu alaihi wasallam, ya yi hani da muthlah.”
Malam ya ce, “Lallai na kasance na yalwata zance a cikin wannan mas’ala (ta aske gemu) a cikin mukaloli na Mujalla, wadda matasa suka taimaka wajen watsa ta a tsawon adadinta 41 daga shekarar farko. Sannan masu tsarkakakkiya zuciya daga cikin masoya sunnah kuma masu jihadi cikin daukaka ta suka ci gaba da watsa ta a cikin wasika mai taken “Gemu a mahangar addini (Musulunci)” wadda wani kamfanin dab’i na Musulunci da ke Baghdad ya rika bugawa ana watsa ta.
“A ciki, lallai na ambaci nassoshin malamai dangane da haramcin askewar, wanda kuma aka cirato daga malaman mazhabobin nan guda hudu. Duk wanda yake da sha’awar ya fadada bincike da ganin bayani, sai ya koma wa wannan mukala.
“Kada ka rudu, ya dan uwa, dangane da yawan wadanda suke saba wa wannan mas’ala, ta aske gemu, duk da yake a cikinsu akwai wani sashe na wadanda ke da nasaba da ilmi (wato malamai). Yadda al’amari yake shi ne duk ilmin da ba a moruwa da shi wajen yin aiki da abin da ya zo daga wajen Ma’aikin Alllah, sallallaahu alaihi wasallam, na shiriya da haske, to jahilci ya fi alheri da shi (wato gara jahili da malamin da ba ya aiki da ilminsa), musamman ma idan ya wuce gona-da-iri da ilmin wajen danganta tawili a kan nassi wanda yake karara a bayyane, babu wata sarkakiya game da shi. Ya maida shi ta fuskar wargi da wauta wajen biye wa maganganun wadansu da kan ce, (wai) “Ai yalwata gemu ba ya cikin kowane al’amari na addini, sai dai wani sha’ani ne daga sha’anonin duniya, wanda musulmi yake da zabi a cikinsa.”
“Suna fadin irin wannan zance alhalin suna sane cewa yalwata (tsayar da) gemu yana daga cikin fitra (dabi’a ta dan Adamtaka), kamar yadda Ma’aiki, sallallaahu alaihi wasallam, ya ce a ruwayar Muslim da waninsa. Ita kuwa fitra ba ta karbar musaya a shari’a, kamar yadda Mai girma da buwaya Ya ce, “…Fitrar (halittar) Allah ke nan da Ya dora (halitta) mutane a kan ta, kuma babu canji (musanyawa) ga (tsarin) halittar Allah. Wannan shi ne addini tabbatacce, madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba san haka ba.” (Surar Ruum – 30). Ya Allah Ka tabbatar da mu da tabbataccen zancenKa a cikin rayuwar duniya da lahira.] Nan zancen malam game da sharhin hadisin la’anar kamanci ya kare.
A karkashin wannan zance na kamantuwa da mata dai, ba boyayyen abu ba ne cewa askewar gemu ga maza, wanda (shi gemun) Allah Ya dauke wa mata (dabi’antuwa da shi), shi ne mafi girman kamantuwa da su (matan). Kuma yana yiwuwa ya kasance, daga abin da muka gangaro da shi na daga dalilai da hujjoji, wadanda aka jaraba da wannan al’amari (na aske gemu) su gane gaskiya su koma mata. Muna rokon Allah Ya yi mana rangwame da kuma su, game da kauce wa duk abin da ba Ya so kuma Bai yarda da shi ba.” Wannan shi ne karshen bayanin da ke cikin littafi Adaabuz Zufaaf.
Daga irin bayanan da suka gabata, muna iya cewa, in dai mutum ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, zai yarda da hukunci ya koma hanyar gaskiya. Babban al’amari ma dai shi ne wajen izgilanci da wadansu kan yi wa wadanda suka tsayar da gemu. Ba a wasa da kowane irin nau’i na umurni ko hani a Musulunci, domin yin haka yana iya kai mutum ga barin da’irar Musuluncin baki daya, musamman ma dai idan akwai ilmi a kan haka. Allah Ya kiyashe mu da fadawa tarkon da ba za mu iya fita ba.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya ya ce, “Bayanin kur’ani da hadisi da haduwar malamai ya nuna cewa an umurci mu yi bamban da kafirai wato an hana mu yi kama da su – a magana ta bai daya – saboda kamantuwa da su a bayyane yana iya sanya mu yi kama da su a dabi’a, kuma sai mu rika yin munanan ayyuka, har ma in aka yi rashin sa’a, sai abin (koyin) ya kasance a cikin kudurce-kudurce na imani. Wannan kuwa yana tsatso soyayya da kuma sa abokantaka ta cikin zuciya – kamar yadda soyayyar cikin zuciya kan haifar da kamantuwa ta bayyane.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1330; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}