Topic: Hukuncin Bikin Ranar Masoya Na Duniya (Valentine's Day) A Musulunci
Timeline: 2012-05-13 05:49:45
Hukuncin Bikin Ranar Masoya Na Duniya (Valentine's Day) A Musulunci
A Rubuce Da Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmaan
Hukuncin Bikin Ranar Masoya Na Duniya (Valentine's Day) A Musulunci
Gabatarwa:
Kowace al’umma na da bukukuwan addini wadanda ta ke takama da su, kuma su ke maimaituwa gare ta, lokaci zuwa lokaci.
Irin wadannan bukukuwa hanya ce ta gane dabi’ar al’umma, kuma alamomi na fahimtar abubuwan da suka kebanci kowace al’umma.
Misali wadanda ba Musulmi ba suna da bikin Alhamis din da aka ce an saukar da maa’idah da sabuwar shekara, da kirsimati, da godiya, da hutu, da sauransu.
Haka kuma, Zoroastrians na da bikin Mahrajaan da Nauruuz, su kuma Baatiniyyah na da Eidul Ghadeer.
Musulmi na da bukukuwa guda biyu a cikin shekara, kuma suna da guda dayaa kowane mako.
Bukukuwan Musulmi na shekara-shekara su ne: ranar salla }arama da ranar sallar layya. Bikin mako-mako kuwa, shi ne ranar Juma’a.
A wajen Musulmi, bukukuwan addini na daga cikin Shari’a, kuma nau’in ibada ce da a ke kusantar Allah (Mai girma da ]aukaka) da su.
Magabata a cikin al’ummar Musulmai sun riki al’amarin bukukuwan addini da matukar muhimmanci, kuma sun dauki matakan ganin cewa ba su rudu da kowane irin bikin al’ada ko na addini da ya shahara a cikin wadanda ba musulmi ba, ballantana su yi tarayya da su. Ta haka, sai suka kubuta daga kamanceceniya da kafirai, kuma suka tsare akidar Musulunci da kyawawan al’adunsa daga kisisiniyar kafirai.
Amma a yau, abubuwa sun canza! Munanan akidu da gurbatattun al’adun dake gangarowa cikin Musulmi daga }asashen kafirai sun sanya wa]ansu Musulmi, musamman `yan boko a cikin matasa, maza da mata, suna ba bukukuwan kafirai muhimmanci, wani lokaci ma, suna zakewa wajen yin tarayya da wadanda ba musulmi ba a cikin bukukuwan su a addini.
Daga cikin irin wadannan bukukuwan addini da suka gangaro wa Musulmi daga wadanda ba Musulmi ba, akwai bikin murnar zagayowar ranar Valentine (Valentine’s day), wato ranar nuna tsananin soyayya da kauna ga masoyi, ko kuma, kamar yadda a ke kiransa da larabci” عيد الحب”"
***
TARIHIN BIKIN RANAR MASOYA (RANAR VALENTINE)
Asalin bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke kan addinin maguzanci fiye da karni goma sha bakwai da ya wuce. An ce bikin ya samo asali ne daga akidar Romawa cewa wai wata macen kyarkeci ta taba shayar da Romulus, wanda ya assasa garin Rome nono, kuma hakan ya ba shi }arfin gaske da kuma hikima ta musamman.
Romawa sun rika yin gagarumin bikin murnar zagayowar wannan rana a tsakiyar wata Febreru na kowace shekara.
A lokacin bikin, ana yanka kare da akuya, a inda kartin matasa, majiya karfi za su shafe jikinsu da jinin, sannan, su wanke jinin da madara. Daga nan, sai su jagoranci faretin zagaya gari a kan tituna, suna rike da fatun da za su bugi duk wanda ya fado masu. Matan Romawa suna fada wa wadannan matasa don a buge su, kuma hakan yana faranta masu rai saboda imanin da suka yi cewa yana maganin matsalar rashin haihuwa.
An ce Valentine sunan wani malamin kiristoci ne wanda ya mutu a dalilin cutarwar Claudius, shugaban Gothic a shekarar 296 CE. A shekarar 350 CE an gina coci a wurin da ya mutu, domin a rika tunawa da shi. Da Romawa suka shiga cikin kiristanci, sun ci gaba da bikin soyayya, illa iyaka, sun canza shi daga bikin soyayyar ruhi irin na muguzanci zuwa bikin shahidan soyayya don tunawa da Valentine, kasancewar, a cewar su, ya yada kauna da soyayya da zaman lafiya, abin da kuma ya kai shi ga rasa ransa.
A wani kaulin kuma, an ce bikin ranar Valentine ya samo asali ne daga lokacin da Romawa suka shiga cikin kiristanci. Sarkin Rome, Claudius II ya sanya dokar hana sojoji yin aure a karni na uku bisa hujjar cewa aure zai shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga yaki.
Valentine ya bijire wa wannan doka, kuma ya ci gaba da daura wa sojoji aure a boye. Da sarkin ya gano, sai ya jefa shi cikin kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa.Yana cikin kurkuku ne ya kamu da ciwon son `yar sarkin, amma a boye, duk da cewa haramun ne ya so wata mace ko kuma ya yi aure, a matsayinsa na babban malamin kirista, kasancewar dokokin kiristanci sun hana. An ce daga baya, sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar kiristanci, ya bauta wa gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi daya daga cikin makusantansa kuma ya aurar masa da `yarsa.
Kasancewar Valentine ya ki yarda da haka, an kashe shi a ranar 14 ga Febreru 270 CE, a daren 15 ga watan Febrerun da aka saba yin bikin Lupercalis. Daga nan aka canza sunan bikin ya koma ranar tunawa da Valentine, ko dai saboda dagewar da ya yi a kan kiristanci, ko kuma saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka fa]a cikin soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.
Daga nan, sai Pope, shugaban kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da ranar 14 ga Febreru 270 CE a matsayin ranar bikin soyayya, kuma ya shar’anta wa duk kan kiristoci murnar zagayowar wannan rana a kowace shekara.
Da ma Allah (Ma]aukaki) Ya ba da labarin yadda kiristoci ke daukar malamansu a matsayin abin bauta, da yadda su ke bin abubuwan da suka halatta ko suka haramta masu sau da kafa, ba tare da neman dalili a cikin littafinsu ba.
ABUBUWAN DA A KE YI A RANAR VALENTINE
1. Bayyanar da farin ciki da jin dadi a wannan rana, kamar yadda a ke yi asauran manyan bukukuwa.
2. Musanyar jajayen fulawa, wadanda ke alamta soyayya, wato soyayyar ruhi irin ta maguzawa ko kuma tsantsar soyayya irin ta kiristoci
3. Aika wa da katin gaisuwa, wato, greeting cards. A jikin wadansu katin, akan samu hoton ubangijin soyayya na Romawa a siffar wani yaro mai fikafikai guda biyu, da ke rike da baka da kibiya.
4. Rubuta kalmomin soyayya da amfani da lafuzzan da ke motsar da sha’awa ajikin katin. A wani lokaci a kan rubuta ‘be my Valentine’, wato ka zamanto tsantsar masoyina a wannan rana. Haka kuma a halin yanzu, a kan aika da sakonnin batsa da rashin kamun kai ta hanyar wayar tafi da gidanka.
5. Musanyar kyaututtukan da suka hada da fulawa da alawa, a tskananin ma’aura ko samari da `yan mata
6. A wadansu kasashen, ana shirya kasaitaccen biki (party) ta yadda maza d amata za su cakude da juna, a yi rawa, a yi anashuwa tare, wani lokaci kuma, a hada da masha’a.
ABUBUWAN LURA DANGANE DA RANAR VALENTINE
Asalin bikin ranar Valentine daga Romawa ne wadanda ke bin akidar maguzanci. A wajensu, biki ne da ke nuna soyayyar da su ke wa gunkinsu mai suna ubangijin soyayya.
Tarihin wannan biki a wajen Romawa ya kunshi tatsuniya da surkullen da duk wani mai hankali zai karyata, ballantana kuma Musulmin da ya san abin da ya ke yi. Hatta ma a wajen kiristoci, akwai sabani mai yawan gaskea tsakanin malamansu dangane da gaskiyar alakar Valentine da wannan biki.
Biki ne da ya kunshi kamanceceniya da mushrikan Romawa da kuma tarayya da kiristoci. Yin kamanceceniya da kafirai ko tarayya da su a cikin addininsu ko akidarsu ko ibadarsu ko wata al’ada da ta kebanta da su, haramun ne kamar yadda manyan malaman musulunci suka bayyana irin su Sheikhul Islam Ibn ta Taimiyyah, da Ibnul Kayyim, Da Azzahabi, da Ibnul Turkumani. Dss (Allah ya jikan su da rahama).
MATSAYIN BIKIN RANAR VALENTINE A MUSULUNCI
Manyan malaman Musulunci na wannan zamani irin su Sheikh Ibnul Uthaimin, da Sheikh Ibnu Jibrin dss, haka nan majalisar koli ta malaman Saudiyya duk sun haramata wannan biki bisa madogara ta shari’a wadda an nuni zuwa gareta a baya, wato tarayya da kafurai a bukuwan da suka kebanta da su. Baya ga kamanceceniyar da wannan zai haifar ta wannan bangare tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba, wanda duk wannan Allah da ma’aikinsa sun hana, baya ga abubuwa da dama day a kunsa na keta alfarmar shari’ar musulunci, Sannan ga fasadi mai tarin yawa da wannan biki ya kunsa wanda har sai da ta kai kasar Italiya (Inda babbar fadar kiristanci ta duniya take a yau Vatican) ta taba haramta shi saboda munin abin da yake faruwa a ciki.
MATSAYIN MUSULMI GAME DA RANAR VALENTINE
Ya kamata kowane Musulmi ya daukar wa kansa wannan matsayi:
• Kin yin wannan biki ko tarayya a cikinsa ko halartar wurin da a ke yi
• Kin taimaka wa kafirai da sauran kangararrun Musulmi ta kowace irin hanya wajen samun nasarar wannan bamagujen biki, kamar ba da kyauta ko karbar kyauta, ko buga katin gaisuwa, ko ba da aron wani abu da ya mallaka, ko sayar masu da wani abu da zai taimaka masu wajen gudanar da wannan sakarci.
• Yin inkari gare su, da bayyana kyama ga abin da ake yi a wannan rana.
• Kin yin gaisuwar taya murna ko amsa irin wannan gaisuwa idan aka yimasa
• Yin nasiha ga Musulmin da ke irin wannan bamagujen biki, gwargwadon iko, matukar akwai maslaha.
Allah ya kare mana imaninmu, ya kuma kiyaye mu daga kamanceceniya da kafurai, ya sa mu rika alfahari da addinmu wanda babu kamarsa.
***
An rairayo wannan kasida daga rubutu ko fassarar:
Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmaan (abellodogarawa@gmail.com) Sashen Kayar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria. Mai taken:
Hukuncin Bikin Ranar Valentine a Musulunci
Allah ya saka masa da alheri.
**{Legacy activities, comments etc counter: 4262; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}