1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ
وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاءً ۚ
وَاتَّقُوا اللهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ وَالْأَرْحَامَ ۚ إِنَّ اللهَ كَانَ
عَلَيْكُمْ رَقِيبًا
Ya ayyuha annasuittaqoo rabbakumu allathee khalaqakum min nafsin
wahidatinwakhalaqa minha zawjaha wabaththa minhumarijalan katheeran wanisaan
wattaqoo Allahaallathee tasaaloona bihi wal-arhamainna Allaha kana AAalaykum
raqeeb
Hausa
Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda,
kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu
yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi,
da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
|
Ayah 4:2 الأية
وَآتُوا الْيَتَامَىٰ أَمْوَالَهُمْ ۖ وَلَا تَتَبَدَّلُوا الْخَبِيثَ بِالطَّيِّبِ
ۖ وَلَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَهُمْ إِلَىٰ أَمْوَالِكُمْ ۚ إِنَّهُ كَانَ حُوبًا
كَبِيرًا
Waatoo alyatama amwalahumwala tatabaddaloo alkhabeetha bittayyibiwala ta/kuloo
amwalahum ila amwalikuminnahu kana hooban kabeera
Hausa
Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau.
Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne
mai girma.
|
Ayah 4:3 الأية
وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَىٰ فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم
مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا
تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا
تَعُولُوا
Wa-in khiftum alla tuqsitoo feealyatama fankihoo ma tabalakum mina annisa-i
mathna wathulathawarubaAAa fa-in khiftum alla taAAdiloo fawahidatanaw ma malakat
aymanukum thalika adnaalla taAAooloo
Hausa
Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda
zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da
huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri)
guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi
kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
|
Ayah 4:4 الأية
وَآتُوا النِّسَاءَ صَدُقَاتِهِنَّ نِحْلَةً ۚ فَإِن طِبْنَ لَكُمْ عَن شَيْءٍ
مِّنْهُ نَفْسًا فَكُلُوهُ هَنِيئًا مَّرِيئًا
Waatoo annisaa saduqatihinnanihlatan fa-in tibna lakum AAan shay-in minhunafsan
fakuloohu hanee-an maree-a
Hausa
Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku
wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.
|
Ayah 4:5 الأية
وَلَا تُؤْتُوا السُّفَهَاءَ أَمْوَالَكُمُ الَّتِي جَعَلَ اللهُ لَكُمْ قِيَامًا
وَارْزُقُوهُمْ فِيهَا وَاكْسُوهُمْ وَقُولُوا لَهُمْ قَوْلًا مَّعْرُوفًا
Wala tu/too assufahaaamwalakumu allatee jaAAala Allahu lakum qiyamanwarzuqoohum
feeha waksoohum waqooloo lahumqawlan maAAroofa
Hausa
Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu
tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su,
kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
|
Ayah 4:6 الأية
وَابْتَلُوا الْيَتَامَىٰ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغُوا النِّكَاحَ فَإِنْ آنَسْتُم
مِّنْهُمْ رُشْدًا فَادْفَعُوا إِلَيْهِمْ أَمْوَالَهُمْ ۖ وَلَا تَأْكُلُوهَا
إِسْرَافًا وَبِدَارًا أَن يَكْبَرُوا ۚ وَمَن كَانَ غَنِيًّا فَلْيَسْتَعْفِفْ ۖ
وَمَن كَانَ فَقِيرًا فَلْيَأْكُلْ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِذَا دَفَعْتُمْ إِلَيْهِمْ
أَمْوَالَهُمْ فَأَشْهِدُوا عَلَيْهِمْ ۚ وَكَفَىٰ بِاللهِ حَسِيبًا
Wabtaloo alyatama hattaitha balaghoo annikaha fa-in anastumminhum rushdan
fadfaAAoo ilayhim amwalahum walata/kulooha israfan wabidaran an yakbaroowaman
kana ghaniyyan falyastaAAfif waman kanafaqeeran falya/kul bilmaAAroofi fa-itha
dafaAAtumilayhim amwalahum faashhidoo AAalayhim wakafa billahihaseeba
Hausa
Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da
shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma
da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma
wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu
dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.
|
Ayah 4:7 الأية
لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ وَلِلنِّسَاءِ
نَصِيبٌ مِّمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنْهُ أَوْ
كَثُرَ ۚ نَصِيبًا مَّفْرُوضًا
Lirrijali naseebun mimmataraka alwalidani wal-aqraboona walinnisa-inaseebun
mimma taraka alwalidani wal-aqraboonamimma qalla minhu aw kathura naseeban
mafrooda
Hausa
Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma
mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga
abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.
|
Ayah 4:8 الأية
وَإِذَا حَضَرَ الْقِسْمَةَ أُولُو الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينُ
فَارْزُقُوهُم مِّنْهُ وَقُولُوا لَهُمْ قَوْلًا مَّعْرُوفًا
Wa-itha hadara alqismataoloo alqurba walyatama walmasakeenufarzuqoohum minhu
waqooloo lahum qawlan maAAroofa
Hausa
Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku
azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.
|
Ayah 4:9 الأية
وَلْيَخْشَ الَّذِينَ لَوْ تَرَكُوا مِنْ خَلْفِهِمْ ذُرِّيَّةً ضِعَافًا خَافُوا
عَلَيْهِمْ فَلْيَتَّقُوا اللهَ وَلْيَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا
Walyakhsha allatheena law tarakoo minkhalfihim thurriyyatan diAAafan
khafooAAalayhim falyattaqoo Allaha walyaqooloo qawlan sadeeda
Hausa
Kuma waɗanda suke dã sun bar zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a
kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana
madaidaiciya.
|
Ayah 4:10 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَأْكُلُونَ أَمْوَالَ الْيَتَامَىٰ ظُلْمًا إِنَّمَا يَأْكُلُونَ
فِي بُطُونِهِمْ نَارًا ۖ وَسَيَصْلَوْنَ سَعِيرًا
Inna allatheena ya/kuloona amwalaalyatama thulman innamaya/kuloona fee
butoonihim naran wasayaslawnasaAAeera
Hausa
Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a
cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.
|
Ayah 4:11 الأية
يُوصِيكُمُ اللهُ فِي أَوْلَادِكُمْ ۖ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنثَيَيْنِ ۚ
فَإِن كُنَّ نِسَاءً فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَ ۖ وَإِن
كَانَتْ وَاحِدَةً فَلَهَا النِّصْفُ ۚ وَلِأَبَوَيْهِ لِكُلِّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا
السُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُ وَلَدٌ ۚ فَإِن لَّمْ يَكُن لَّهُ وَلَدٌ
وَوَرِثَهُ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ الثُّلُثُ ۚ فَإِن كَانَ لَهُ إِخْوَةٌ
فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصِي بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۗ
آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ لَا تَدْرُونَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ لَكُمْ نَفْعًا ۚ
فَرِيضَةً مِّنَ اللهِ ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا
Yooseekumu Allahu fee awladikumliththakari mithlu haththialonthayayni fa-in
kunna nisaan fawqa ithnatayni falahunnathulutha ma taraka wa-in kanat
wahidatanfalaha annisfu wali-abawayhi likulli wahidinminhuma assudusu mimma
taraka in kanalahu waladun fa-in lam yakun lahu waladun wawarithahu
abawahufali-ommihi aththuluthu fa-in kana lahu ikhwatunfali-ommihi assudusu min
baAAdi wasiyyatin yooseebiha aw daynin abaokum waabnaokum latadroona ayyuhum
aqrabu lakum nafAAan fareedatan mina Allahiinna Allaha kana AAaleeman hakeema
Hausa
Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu.
Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin
abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma
iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da
ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi
ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga
cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana
da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa
bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani,
a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
|
Ayah 4:12 الأية
وَلَكُمْ نِصْفُ مَا تَرَكَ أَزْوَاجُكُمْ إِن لَّمْ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٌ ۚ فَإِن
كَانَ لَهُنَّ وَلَدٌ فَلَكُمُ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْنَ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ
يُوصِينَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۚ وَلَهُنَّ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْتُمْ إِن لَّمْ
يَكُن لَّكُمْ وَلَدٌ ۚ فَإِن كَانَ لَكُمْ وَلَدٌ فَلَهُنَّ الثُّمُنُ مِمَّا
تَرَكْتُم ۚ مِّن بَعْدِ وَصِيَّةٍ تُوصُونَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۗ وَإِن كَانَ رَجُلٌ
يُورَثُ كَلَالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَلَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ وَاحِدٍ
مِّنْهُمَا السُّدُسُ ۚ فَإِن كَانُوا أَكْثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمْ شُرَكَاءُ فِي
الثُّلُثِ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصَىٰ بِهَا أَوْ دَيْنٍ غَيْرَ مُضَارٍّ ۚ
وَصِيَّةً مِّنَ اللهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَلِيمٌ
Walakum nisfu ma taraka azwajukumin lam yakun lahunna waladun fa-in kana lahunna
waladunfalakumu arrubuAAu mimma tarakna min baAAdi wasiyyatinyooseena biha aw
daynin walahunna arrubuAAumimma taraktum in lam yakun lakum waladun fa-in
kanalakum waladun falahunna aththumunu mimma taraktummin baAAdi wasiyyatin
toosoona biha awdaynin wa-in kana rajulun yoorathu kalalatan awiimraatun walahu
akhun aw okhtun falikulli wahidin minhumaassudusu fa-in kanoo akthara min
thalikafahum shurakao fee aththuluthi min baAAdi wasiyyatinyoosa biha aw daynin
ghayra mudarrin wasiyyatanmina Allahi wallahu AAaleemun haleem
Hausa
Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare
su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga
cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ
kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai
kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya
daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka
yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa
wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa to, kõwane ɗaya daga cikinsu
yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa
daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan
wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga
Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.
|
Ayah 4:13 الأية
تِلْكَ حُدُودُ اللهِ ۚ وَمَن يُطِعِ اللهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ
تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ الْفَوْزُ
الْعَظِيمُ
Tilka hudoodu Allahi waman yutiAAiAllaha warasoolahu yudkhilhu jannatin tajree
min tahtihaal-anharu khalideena feeha wathalikaalfawzu alAAatheem
Hausa
Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai
shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu,
suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.
|
Ayah 4:14 الأية
وَمَن يَعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدْخِلْهُ نَارًا
خَالِدًا فِيهَا وَلَهُ عَذَابٌ مُّهِينٌ
Waman yaAAsi Allahawarasoolahu wayataAAadda hudoodahu yudkhilhu narankhalidan
feeha walahu AAathabun muheen
Hausa
Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda
shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.
|
Ayah 4:15 الأية
وَاللَّاتِي يَأْتِينَ الْفَاحِشَةَ مِن نِّسَائِكُمْ فَاسْتَشْهِدُوا عَلَيْهِنَّ
أَرْبَعَةً مِّنكُمْ ۖ فَإِن شَهِدُوا فَأَمْسِكُوهُنَّ فِي الْبُيُوتِ حَتَّىٰ
يَتَوَفَّاهُنَّ الْمَوْتُ أَوْ يَجْعَلَ اللهُ لَهُنَّ سَبِيلًا
Wallatee ya/teena alfahishatamin nisa-ikum fastashhidoo AAalayhinna
arbaAAatanminkum fa-in shahidoo faamsikoohunna fee albuyooti hattayatawaffahunna
almawtu aw yajAAala Allahu lahunnasabeela
Hausa
Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu
daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har
mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.
|
Ayah 4:16 الأية
وَاللَّذَانِ يَأْتِيَانِهَا مِنكُمْ فَآذُوهُمَا ۖ فَإِن تَابَا وَأَصْلَحَا
فَأَعْرِضُوا عَنْهُمَا ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ تَوَّابًا رَّحِيمًا
Wallathani ya/tiyanihaminkum faathoohuma fa-in taba waaslahafaaAAridoo AAanhuma
inna Allaha kanatawwaban raheema
Hausa
Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan
idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu.
Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai
|
Ayah 4:17 الأية
إِنَّمَا التَّوْبَةُ عَلَى اللهِ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السُّوءَ بِجَهَالَةٍ
ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٍ فَأُولَٰئِكَ يَتُوبُ اللهُ عَلَيْهِمْ ۗ وَكَانَ
اللهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Innama attawbatu AAalaAllahi lillatheena yaAAmaloona assoo-abijahalatin thumma
yatooboona min qareebin faola-ikayatoobu Allahu AAalayhim wakana AllahuAAaleeman
hakeema
Hausa
Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da
jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma
Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 4:18 الأية
وَلَيْسَتِ التَّوْبَةُ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ حَتَّىٰ إِذَا حَضَرَ
أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ إِنِّي تُبْتُ الْآنَ وَلَا الَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمْ
كُفَّارٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا
Walaysati attawbatu lillatheenayaAAmaloona assayyi-ati hatta ithahadara
ahadahumu almawtu qala inneetubtu al-ana wala allatheena yamootoonawahum
kuffarun ola-ika aAAtadna lahum AAathabanaleema
Hausa
Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta
halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga
waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata
azãba mai raɗaɗi
|
Ayah 4:19 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَرِثُوا النِّسَاءَ
كَرْهًا ۖ وَلَا تَعْضُلُوهُنَّ لِتَذْهَبُوا بِبَعْضِ مَا آتَيْتُمُوهُنَّ إِلَّا
أَن يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ ۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِن
كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللهُ فِيهِ
خَيْرًا كَثِيرًا
Ya ayyuha allatheena amanoola yahillu lakum an tarithoo annisaakarhan wala
taAAduloohunna litathhaboobibaAAdi ma ataytumoohunna illa anya/teena
bifahishatin mubayyinatin waAAashiroohunnabilmaAAroofi fa-in karihtumoohunna
faAAasa antakrahoo shay-an wayajAAala Allahu feehi khayran katheera
Hausa
Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma
kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka
zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an
nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya
wani alhẽri mai yawaa cikinsa.
|
Ayah 4:20 الأية
وَإِنْ أَرَدتُّمُ اسْتِبْدَالَ زَوْجٍ مَّكَانَ زَوْجٍ وَآتَيْتُمْ إِحْدَاهُنَّ
قِنطَارًا فَلَا تَأْخُذُوا مِنْهُ شَيْئًا ۚ أَتَأْخُذُونَهُ بُهْتَانًا وَإِثْمًا
مُّبِينًا
Wa-in aradtumu istibdala zawjin makanazawjin waataytum ihdahunna qintaranfala ta/khuthoo
minhu shay-an ata/khuthoonahubuhtanan wa-ithman mubeena
Hausa
Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa
ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da
ƙarya da zunubi bãyyananne?
|
Ayah 4:21 الأية
وَكَيْفَ تَأْخُذُونَهُ وَقَدْ أَفْضَىٰ بَعْضُكُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ وَأَخَذْنَ
مِنكُم مِّيثَاقًا غَلِيظًا
Wakayfa ta/khuthoonahu waqad afdabaAAdukum ila baAAdin waakhathnaminkum
meethaqan ghaleetha
Hausa
Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe,
kuma sun riƙi alkawari mai kauri daga gare ku?
|
Ayah 4:22 الأية
وَلَا تَنكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُم مِّنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۚ
إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَمَقْتًا وَسَاءَ سَبِيلًا
Wala tankihoo ma nakahaabaokum mina annisa-i illa maqad salafa innahu kana
fahishatan wamaqtan wasaasabeela
Hausa
Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige.
Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.
|
Ayah 4:23 الأية
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ
وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي
أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُم مِّنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ
وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُم
بِهِنَّ فَإِن لَّمْ تَكُونُوا دَخَلْتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ
وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَن تَجْمَعُوا بَيْنَ
الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hurrimat AAalaykum ommahatukumwabanatukum waakhawatukum waAAammatukum
wakhalatukumwabanatu al-akhi wabanatu al-okhti waommahatukumuallatee ardaAAnakum
waakhawatukum mina arradaAAatiwaommahatu nisa-ikum waraba-ibukumu allateefee
hujoorikum min nisa-ikumu allateedakhaltum bihinna fa-in lam takoonoo dakhaltum
bihinna falajunaha AAalaykum wahala-ilu abna-ikumuallatheena min aslabikum waan
tajmaAAoobayna al-okhtayni illa ma qad salafa inna Allahakana ghafooran raheema
Hausa
An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da
innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka
shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da
agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da
su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan 'yã'yanku
waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã,
fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:24 الأية
وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۖ كِتَابَ
اللهِ عَلَيْكُمْ ۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَاءَ ذَٰلِكُمْ أَن تَبْتَغُوا
بِأَمْوَالِكُم مُّحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ ۚ فَمَا اسْتَمْتَعْتُم بِهِ
مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا
تَرَاضَيْتُم بِهِ مِن بَعْدِ الْفَرِيضَةِ ۚ إِنَّ اللهَ كَانَ عَلِيمًا
حَكِيمًا
Walmuhsanatu mina annisa-iilla ma malakat aymanukum kitaba AllahiAAalaykum
waohilla lakum ma waraa thalikuman tabtaghoo bi-amwalikum muhsineena ghayra
musafiheenafama istamtaAAtum bihi minhunna faatoohunnaojoorahunna fareedatan
wala junaha AAalaykumfeema taradaytum bihi min baAAdi alfareedatiinna Allaha
kana AAaleeman hakeema
Hausa
Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku
tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan.
Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin
da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar
sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan
farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 4:25 الأية
وَمَن لَّمْ يَسْتَطِعْ مِنكُمْ طَوْلًا أَن يَنكِحَ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ
فَمِن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُم مِّن فَتَيَاتِكُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ۚ وَاللهُ
أَعْلَمُ بِإِيمَانِكُم ۚ بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ ۚ فَانكِحُوهُنَّ بِإِذْنِ
أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ
مُسَافِحَاتٍ وَلَا مُتَّخِذَاتِ أَخْدَانٍ ۚ فَإِذَا أُحْصِنَّ فَإِنْ أَتَيْنَ
بِفَاحِشَةٍ فَعَلَيْهِنَّ نِصْفُ مَا عَلَى الْمُحْصَنَاتِ مِنَ الْعَذَابِ ۚ
ذَٰلِكَ لِمَنْ خَشِيَ الْعَنَتَ مِنكُمْ ۚ وَأَن تَصْبِرُوا خَيْرٌ لَّكُمْ ۗ
وَاللهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Waman lam yastatiAA minkum tawlanan yankiha almuhsanati almu/minatifamin ma
malakat aymanukum min fatayatikumualmu/minati wallahu aAAlamu bi-eemanikumbaAAdukum
min baAAdin fankihoohunnabi-ithni ahlihinna waatoohunna ojoorahunna
bilmaAAroofimuhsanatin ghayra masafihatin walamuttakhithati akhdanin fa-itha
ohsinnafa-in atayna bifahishatin faAAalayhinna nisfu maAAala almuhsanati mina
alAAathabi thalikaliman khashiya alAAanata minkum waan tasbiroo khayrunlakum
wallahu ghafoorun raheem
Hausa
Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya
aura)daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma
Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin
mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun
kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai
kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya
daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku.
Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin
ƙai.
|
Ayah 4:26 الأية
يُرِيدُ اللهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمْ وَيَهْدِيَكُمْ سُنَنَ الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ
وَيَتُوبَ عَلَيْكُمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Yureedu Allahu liyubayyina lakumwayahdiyakum sunana allatheena min qablikum
wayatoobaAAalaykum wallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a
gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.
|
Ayah 4:27 الأية
وَاللهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيْكُمْ وَيُرِيدُ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ
الشَّهَوَاتِ أَن تَمِيلُوا مَيْلًا عَظِيمًا
Wallahu yureedu an yatoobaAAalaykum wayureedu allatheena yattabiAAoona
ashshahawatian tameeloo maylan AAatheem
Hausa
Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna
nufin ku karkata, karkata mai girma.
|
Ayah 4:28 الأية
يُرِيدُ اللهُ أَن يُخَفِّفَ عَنكُمْ ۚ وَخُلِقَ الْإِنسَانُ ضَعِيفًا
Yureedu Allahu an yukhaffifa AAankumwakhuliqa al-insanu daAAeefa
Hausa
Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.
|
Ayah 4:29 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَكُم بَيْنَكُم بِالْبَاطِلِ
إِلَّا أَن تَكُونَ تِجَارَةً عَن تَرَاضٍ مِّنكُمْ ۚ وَلَا تَقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ
ۚ إِنَّ اللهَ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا
Ya ayyuha allatheena amanoola ta/kuloo amwalakum baynakum bilbatiliilla an
takoona tijaratan AAan taradinminkum wala taqtuloo anfusakum inna Allaha
kanabikum raheema
Hausa
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara,
fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada
ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.
|
Ayah 4:30 الأية
وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ عُدْوَانًا وَظُلْمًا فَسَوْفَ نُصْلِيهِ نَارًا ۚ وَكَانَ
ذَٰلِكَ عَلَى اللهِ يَسِيرًا
Waman yafAAal thalika AAudwananwathulman fasawfa nusleehi naran wakanathalika
AAala Allahi yaseera
Hausa
Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma
wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi.
|
Ayah 4:31 الأية
إِن تَجْتَنِبُوا كَبَائِرَ مَا تُنْهَوْنَ عَنْهُ نُكَفِّرْ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ
وَنُدْخِلْكُم مُّدْخَلًا كَرِيمًا
In tajtaniboo kaba-ira matunhawna AAanhu nukaffir AAankum sayyi-atikum
wanudkhilkummudkhalan kareema
Hausa
Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare
mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.
|
Ayah 4:32 الأية
وَلَا تَتَمَنَّوْا مَا فَضَّلَ اللهُ بِهِ بَعْضَكُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ
لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبُوا ۖ وَلِلنِّسَاءِ نَصِيبٌ مِّمَّا
اكْتَسَبْنَ ۚ وَاسْأَلُوا اللهَ مِن فَضْلِهِ ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ بِكُلِّ
شَيْءٍ عَلِيمًا
Wala tatamannaw ma faddalaAllahu bihi baAAdakum AAala baAAdinlirrijali naseebun
mimma iktasaboowalinnisa-i naseebun mimma iktasabnawas-aloo Allaha min fadlihi
inna Allahakana bikulli shay-in AAaleema
Hausa
Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza
suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da
suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga
dukkan kõme, Masani.
|
Ayah 4:33 الأية
وَلِكُلٍّ جَعَلْنَا مَوَالِيَ مِمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ ۚ
وَالَّذِينَ عَقَدَتْ أَيْمَانُكُمْ فَآتُوهُمْ نَصِيبَهُمْ ۚ إِنَّ اللهَ كَانَ
عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدًا
Walikullin jaAAalna mawaliyamimma taraka alwalidani wal-aqraboonawallatheena
AAaqadat aymanukum faatoohumnaseebahum inna Allaha kana AAalakulli shay-in
shaheeda
Hausa
Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta
suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ku bã su rabonsu. Lalle ne,
Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.
|
Ayah 4:34 الأية
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ
بَعْضٍ وَبِمَا أَنفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ۚ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ
حَافِظَاتٌ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللهُ ۚ وَاللَّاتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ
فَعِظُوهُنَّ وَاهْجُرُوهُنَّ فِي الْمَضَاجِعِ وَاضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ
أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ عَلِيًّا
كَبِيرًا
Arrijalu qawwamoonaAAala annisa-i bima faddalaAllahu baAAdahum AAala baAAdin
wabimaanfaqoo min amwalihim fassalihatu qanitatunhafithatun lilghaybi bima
hafithaAllahu wallatee takhafoonanushoozahunna faAAithoohunna wahjuroohunnafee
almadajiAAi wadriboohunna fa-in ataAAnakumfala tabghoo AAalayhinna sabeelan inna
Allaha kanaAAaliyyan kabeera
Hausa
Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi
a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã
mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda
kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin
wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to,
kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.
|
Ayah 4:35 الأية
وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِّنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا
مِّنْ أَهْلِهَا إِن يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللهُ بَيْنَهُمَا ۗ إِنَّ
اللهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا
Wa-in khiftum shiqaqa baynihimafabAAathoo hakaman min ahlihi wahakaman minahliha
in yureeda islahan yuwaffiqiAllahu baynahuma inna Allaha kanaAAaleeman khabeera
Hausa
Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga
mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai
daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.
|
Ayah 4:36 الأية
وَاعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا ۖ وَبِالْوَالِدَيْنِ
إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينِ وَالْجَارِ ذِي
الْقُرْبَىٰ وَالْجَارِ الْجُنُبِ وَالصَّاحِبِ بِالْجَنبِ وَابْنِ السَّبِيلِ
وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۗ إِنَّ اللهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخْتَالًا
فَخُورًا
WaAAbudoo Allaha walatushrikoo bihi shay-an wabilwalidayni ihsananwabithee
alqurba walyatama walmasakeeniwaljari thee alqurba waljarialjunubi wassahibi
biljanbi wabniassabeeli wama malakat aymanukum inna Allahala yuhibbu man kana
mukhtalan fakhoora
Hausa
Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi
kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci
ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin
da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance
mai tãƙama, mai yawan alfahari.
|
Ayah 4:37 الأية
الَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبُخْلِ وَيَكْتُمُونَ مَا
آتَاهُمُ اللهُ مِن فَضْلِهِ ۗ وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا
Allatheena yabkhaloona waya/muroona annasabilbukhli wayaktumoona ma
atahumuAllahu min fadlihi waaAAtadna lilkafireenaAAathaban muheena
Hausa
Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar
abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba
mai walãkantarwa.
|
Ayah 4:38 الأية
وَالَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ رِئَاءَ النَّاسِ وَلَا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ
وَلَا بِالْيَوْمِ الْآخِرِ ۗ وَمَن يَكُنِ الشَّيْطَانُ لَهُ قَرِينًا فَسَاءَ
قَرِينًا
Wallatheena yunfiqoona amwalahumri-aa annasi wala yu/minoona billahiwala
bilyawmi al-akhiri waman yakuni ashshaytanulahu qareenan fasaa qareena
Hausa
Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin
ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya
kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.
|
Ayah 4:39 الأية
وَمَاذَا عَلَيْهِمْ لَوْ آمَنُوا بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَأَنفَقُوا
مِمَّا رَزَقَهُمُ اللهُ ۚ وَكَانَ اللهُ بِهِمْ عَلِيمًا
Wamatha AAalayhim law amanoobillahi walyawmi al-akhiriwaanfaqoo mimma razaqahumu
Allahu wakana Allahubihim AAaleema
Hausa
Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun
ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?
|
Ayah 4:40 الأية
إِنَّ اللهَ لَا يَظْلِمُ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ ۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةً يُضَاعِفْهَا
وَيُؤْتِ مِن لَّدُنْهُ أَجْرًا عَظِيمًا
Inna Allaha la yathlimumithqala tharratin wa-in taku hasanatan yudaAAifhawayu/ti
min ladunhu ajran AAatheema
Hausa
Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri
ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma.
|
Ayah 4:41 الأية
فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ وَجِئْنَا بِكَ عَلَىٰ
هَٰؤُلَاءِ شَهِيدًا
Fakayfa itha ji/na min kulliommatin bishaheedin waji/na bika AAala
haola-ishaheeda
Hausa
To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan
waɗannan, kana mai shaida!
|
Ayah 4:42 الأية
يَوْمَئِذٍ يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَعَصَوُا الرَّسُولَ لَوْ تُسَوَّىٰ بِهِمُ
الْأَرْضُ وَلَا يَكْتُمُونَ اللهَ حَدِيثًا
Yawma-ithin yawaddu allatheenakafaroo waAAasawoo arrasoola law tusawwabihimu al-ardu
wala yaktumoona Allaha hadeetha
Hausa
A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje
ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri.
|
Ayah 4:43 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنتُمْ سُكَارَىٰ
حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ
تَغْتَسِلُوا ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ
مِّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً
فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ
اللهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا
Ya ayyuha allatheena amanoola taqraboo assalata waantum sukarahatta taAAlamoo ma
taqooloona walajunuban illa AAabiree sabeelin hattataghtasiloo wa-in kuntum
marda aw AAala safarin awjaa ahadun minkum mina algha-iti aw lamastumuannisaa
falam tajidoo maan fatayammamoo saAAeedantayyiban famsahoo biwujoohikum
waaydeekuminna Allaha kana AAafuwwan ghafoora
Hausa
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye,
sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare
hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko
kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi
ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da
hannuwanku . Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.
|
Ayah 4:44 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوتُوا نَصِيبًا مِّنَ الْكِتَابِ يَشْتَرُونَ
الضَّلَالَةَ وَيُرِيدُونَ أَن تَضِلُّوا السَّبِيلَ
Alam tara ila allatheena ootoonaseeban mina alkitabi yashtaroona
addalalatawayureedoona an tadilloo assabeel
Hausa
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen
ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?
|
Ayah 4:45 الأية
وَاللهُ أَعْلَمُ بِأَعْدَائِكُمْ ۚ وَكَفَىٰ بِاللهِ وَلِيًّا وَكَفَىٰ
بِاللهِ نَصِيرًا
Wallahu aAAlamu bi-aAAda-ikumwakafa billahi waliyyan wakafa billahinaseera
Hausa
Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma
Yã isa Ya zama Mataimaki.
|
Ayah 4:46 الأية
مِّنَ الَّذِينَ هَادُوا يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ وَيَقُولُونَ
سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا وَاسْمَعْ غَيْرَ مُسْمَعٍ وَرَاعِنَا لَيًّا
بِأَلْسِنَتِهِمْ وَطَعْنًا فِي الدِّينِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ قَالُوا سَمِعْنَا
وَأَطَعْنَا وَاسْمَعْ وَانظُرْنَا لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَأَقْوَمَ وَلَٰكِن
لَّعَنَهُمُ اللهُ بِكُفْرِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُونَ إِلَّا قَلِيلًا
Mina allatheena hadoo yuharrifoonaalkalima AAan mawadiAAihi wayaqooloona
samiAAnawaAAasayna wasmaAA ghayra musmaAAin waraAAinalayyan bi-alsinatihim
wataAAnan fee addeeni walawannahum qaloo samiAAna waataAAna wasmaAAwanthurna
lakana khayranlahum waaqwama walakin laAAanahumu Allahubikufrihim fala
yu/minoona illa qaleela
Hausa
Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga
wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa,
kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da
harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya
kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance
mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda
kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.
|
Ayah 4:47 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ آمِنُوا بِمَا نَزَّلْنَا مُصَدِّقًا
لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبْلِ أَن نَّطْمِسَ وُجُوهًا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰ
أَدْبَارِهَا أَوْ نَلْعَنَهُمْ كَمَا لَعَنَّا أَصْحَابَ السَّبْتِ ۚ وَكَانَ
أَمْرُ اللهِ مَفْعُولًا
Ya ayyuha allatheenaootoo alkitaba aminoo bima nazzalnamusaddiqan lima maAAakum
min qabli an natmisawujoohan fanaruddaha AAala adbarihaaw nalAAanahum kama
laAAanna as-habaassabti wakana amru Allahi mafAAoola
Hausa
Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai
gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an
nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani
masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.
|
Ayah 4:48 الأية
إِنَّ اللهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن
يَشَاءُ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللهِ فَقَدِ افْتَرَىٰ إِثْمًا عَظِيمًا
Inna Allaha la yaghfiru anyushraka bihi wayaghfiru ma doona thalika limanyashao
waman yushrik billahi faqadi iftaraithman AAatheema
Hausa
Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da
yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle
ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.
|
Ayah 4:49 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُم ۚ بَلِ اللهُ يُزَكِّي مَن
يَشَاءُ وَلَا يُظْلَمُونَ فَتِيلًا
Alam tara ila allatheenayuzakkoona anfusahum bali Allahu yuzakkee man yashaowala
yuthlamoona fateela
Hausa
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake
tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.
|
Ayah 4:50 الأية
انظُرْ كَيْفَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللهِ الْكَذِبَ ۖ وَكَفَىٰ بِهِ إِثْمًا
مُّبِينًا
Onthur kayfa yaftaroona AAalaAllahi alkathiba wakafa bihi ithman mubeena
Hausa
Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi
bayyananne.
|
Ayah 4:51 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوتُوا نَصِيبًا مِّنَ الْكِتَابِ يُؤْمِنُونَ
بِالْجِبْتِ وَالطَّاغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا هَٰؤُلَاءِ أَهْدَىٰ
مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا سَبِيلًا
Alam tara ila allatheena ootoonaseeban mina alkitabi yu/minoona
biljibtiwattaghooti wayaqooloona lillatheenakafaroo haola-i ahda mina allatheena
amanoosabeela
Hausa
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da
gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya
shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"?
|
Ayah 4:52 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَعَنَهُمُ اللهُ ۖ وَمَن يَلْعَنِ اللهُ فَلَن تَجِدَ
لَهُ نَصِيرًا
Ola-ika allatheena laAAanahumuAllahu waman yalAAani Allahu falan tajida lahu
naseera
Hausa
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka
sãmi mataimaki a gare shi ba.
|
Ayah 4:53 الأية
أَمْ لَهُمْ نَصِيبٌ مِّنَ الْمُلْكِ فَإِذًا لَّا يُؤْتُونَ النَّاسَ نَقِيرًا
Am lahum naseebun mina almulki fa-ithanla yu/toona annasa naqeera
Hausa
Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin
gurtsun dabino ba.
|
Ayah 4:54 الأية
أَمْ يَحْسُدُونَ النَّاسَ عَلَىٰ مَا آتَاهُمُ اللهُ مِن فَضْلِهِ ۖ فَقَدْ
آتَيْنَا آلَ إِبْرَاهِيمَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَآتَيْنَاهُم مُّلْكًا
عَظِيمًا
Am yahsudoona annasaAAala ma atahumu Allahu min fadlihifaqad atayna ala
ibraheema alkitabawalhikmata waataynahum mulkan AAatheema
Hausa
Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle
ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
|
Ayah 4:55 الأية
فَمِنْهُم مَّنْ آمَنَ بِهِ وَمِنْهُم مَّن صَدَّ عَنْهُ ۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ
سَعِيرًا
Faminhum man amana bihi waminhum man saddaAAanhu wakafa bijahannama saAAeera
Hausa
To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda
ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.
|
Ayah 4:56 الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا سَوْفَ نُصْلِيهِمْ نَارًا كُلَّمَا نَضِجَتْ
جُلُودُهُم بَدَّلْنَاهُمْ جُلُودًا غَيْرَهَا لِيَذُوقُوا الْعَذَابَ ۗ إِنَّ
اللهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمًا
Inna allatheena kafaroo bi-ayatinasawfa nusleehim naran kullama
nadijatjulooduhum baddalnahum juloodan ghayraha liyathooqooalAAathaba inna
Allaha kana AAazeezan hakeema
Hausa
Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe
fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle
ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 4:57 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن
تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ
مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَنُدْخِلُهُمْ ظِلًّا ظَلِيلًا
Wallatheena amanoowaAAamiloo assalihati sanudkhiluhum jannatintajree min tahtiha
al-anharu khalideenafeeha abadan lahum feeha azwajun mutahharatunwanudkhiluhum
thillan thaleela
Hausa
Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su
gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu
a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar
da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
|
Ayah 4:58 الأية
إِنَّ اللهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَىٰ أَهْلِهَا وَإِذَا
حَكَمْتُم بَيْنَ النَّاسِ أَن تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ ۚ إِنَّ اللهَ نِعِمَّا
يَعِظُكُم بِهِ ۗ إِنَّ اللهَ كَانَ سَمِيعًا بَصِيرًا
Inna Allaha ya/murukum an tu-addooal-amanati ila ahliha wa-itha hakamtumbayna
annasi an tahkumoo bilAAadliinna Allaha niAAimma yaAAithukum bihiinna Allaha
kana sameeAAan baseera
Hausa
Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan
kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah
mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji
ne, Mai gani.
|
Ayah 4:59 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي
الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللهِ
وَالرَّسُولِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ ذَٰلِكَ
خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
Ya ayyuha allatheena amanooateeAAoo Allaha waateeAAoo arrasoolawaolee al-amri
minkum fa-in tanazaAAtum fee shay-infaruddoohu ila Allahi warrasooli in
kuntumtu/minoona billahi walyawmi al-akhirithalika khayrun waahsanu ta/weela
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da
ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku
mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da
Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
|
Ayah 4:60 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ
وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ
أُمِرُوا أَن يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا
بَعِيدًا
Alam tara ila allatheenayazAAumoona annahum amanoo bima onzila ilayka wamaonzila
min qablika yureedoona an yatahakamoo ila attaghootiwaqad omiroo an yakfuroo
bihi wayureedu ashshaytanuan yudillahum dalalan baAAeeda
Hausa
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka
saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra
zuwa ga ¦ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma
Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
|
Ayah 4:61 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَىٰ مَا أَنزَلَ اللهُ وَإِلَى الرَّسُولِ
رَأَيْتَ الْمُنَافِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودًا
Wa-itha qeela lahum taAAalawila ma anzala Allahu wa-ila arrasooliraayta
almunafiqeena yasuddoona AAanka sudooda
Hausa
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga
Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
|
Ayah 4:62 الأية
فَكَيْفَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ثُمَّ
جَاءُوكَ يَحْلِفُونَ بِاللهِ إِنْ أَرَدْنَا إِلَّا إِحْسَانًا وَتَوْفِيقًا
Fakayfa itha asabat-hum museebatunbima qaddamat aydeehim thumma jaooka
yahlifoonabillahi in aradna illa ihsananwatawfeeqa
Hausa
To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar
sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba
sai kyautatawa da daidaitãwa."?
|
Ayah 4:63 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ يَعْلَمُ اللهُ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ
وَعِظْهُمْ وَقُل لَّهُمْ فِي أَنفُسِهِمْ قَوْلًا بَلِيغًا
Ola-ika allatheena yaAAlamuAllahu ma fee quloobihim faaAArid AAanhumwaAAithhum
waqul lahum fee anfusihim qawlan baleegha
Hausa
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau
da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin
sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
|
Ayah 4:64 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذْنِ اللهِ ۚ وَلَوْ
أَنَّهُمْ إِذ ظَّلَمُوا أَنفُسَهُمْ جَاءُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللهَ
وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللهَ تَوَّابًا رَّحِيمًا
Wama arsalna min rasoolin illaliyutaAAa bi-ithni Allahi walaw annahum
iththalamoo anfusahum jaooka fastaghfarooAllaha wastaghfara lahumu
arrasoolulawajadoo Allaha tawwaban raheema
Hausa
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã
dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi
gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai
karɓar tũba Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:65 الأية
فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ
ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنفُسِهِمْ حَرَجًا مِّمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا
تَسْلِيمًا
Fala warabbika la yu/minoona hattayuhakkimooka feema shajara baynahum thumma
layajidoo fee anfusihim harajan mimma qadaytawayusallimoo tasleema
Hausa
To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da
hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci
a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
|
Ayah 4:66 الأية
وَلَوْ أَنَّا كَتَبْنَا عَلَيْهِمْ أَنِ اقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ أَوِ اخْرُجُوا مِن
دِيَارِكُم مَّا فَعَلُوهُ إِلَّا قَلِيلٌ مِّنْهُمْ ۖ وَلَوْ أَنَّهُمْ فَعَلُوا
مَا يُوعَظُونَ بِهِ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَأَشَدَّ تَثْبِيتًا
Walaw anna katabna AAalayhimani oqtuloo anfusakum awi okhrujoo min diyarikum
mafaAAaloohu illa qaleelun minhum walaw annahum faAAaloo mayooAAathoona bihi
lakana khayran lahumwaashadda tathbeeta
Hausa
Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita
daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai
lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance
mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.
|
Ayah 4:67 الأية
وَإِذًا لَّآتَيْنَاهُم مِّن لَّدُنَّا أَجْرًا عَظِيمًا
Wa-ithan laataynahummin ladunna ajran AAatheema
Hausa
Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu.
|
Ayah 4:68 الأية
وَلَهَدَيْنَاهُمْ صِرَاطًا مُّسْتَقِيمًا
Walahadaynahum siratanmustaqeema
Hausa
Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.
|
Ayah 4:69 الأية
وَمَن يُطِعِ اللهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَٰئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللهُ
عَلَيْهِم مِّنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ ۚ
وَحَسُنَ أُولَٰئِكَ رَفِيقًا
Waman yutiAAi Allaha warrasoolafaola-ika maAAa allatheena anAAama
AllahuAAalayhim mina annabiyyeena wassiddeeqeenawashshuhada-i
wassaliheenawahasuna ola-ika rafeeqa
Hausa
Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da
waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da
masu shahãda da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.
|
Ayah 4:70 الأية
ذَٰلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللهِ عَلِيمًا
Thalika alfadlu mina Allahiwakafa billahi AAaleema
Hausa
Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani.
|
Ayah 4:71 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا خُذُوا حِذْرَكُمْ فَانفِرُوا ثُبَاتٍ أَوِ
انفِرُوا جَمِيعًا
Ya ayyuha allatheena amanookhuthoo hithrakum fanfiroo thubatinawi infiroo
jameeAAa
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku sa'an nan ku fitar da hari jama'a,
jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.
|
Ayah 4:72 الأية
وَإِنَّ مِنكُمْ لَمَن لَّيُبَطِّئَنَّ فَإِنْ أَصَابَتْكُم مُّصِيبَةٌ قَالَ قَدْ
أَنْعَمَ اللهُ عَلَيَّ إِذْ لَمْ أَكُن مَّعَهُمْ شَهِيدًا
Wa-inna minkum laman layubatti-annafa-in asabatkum museebatun qala qad
anAAamaAllahu AAalayya ith lam akun maAAahum shaheeda
Hausa
Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa . To idan wata masĩfa ta sãme ku,
sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre
da su ba."
|
Ayah 4:73 الأية
وَلَئِنْ أَصَابَكُمْ فَضْلٌ مِّنَ اللهِ لَيَقُولَنَّ كَأَن لَّمْ تَكُن
بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُ مَوَدَّةٌ يَا لَيْتَنِي كُنتُ مَعَهُمْ فَأَفُوزَ فَوْزًا
عَظِيمًا
Wala-in asabakum fadlun minaAllahi layaqoolanna kaan lam takun baynakum
wabaynahumawaddatun ya laytanee kuntu maAAahum faafooza fawzan AAatheema
Hausa
Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa,
kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama
tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!"
|
Ayah 4:74 الأية
فَلْيُقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللهِ الَّذِينَ يَشْرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا
بِالْآخِرَةِ ۚ وَمَن يُقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللهِ فَيُقْتَلْ أَوْ يَغْلِبْ
فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا
Falyuqatil fee sabeeli Allahiallatheena yashroona alhayata addunyabil-akhirati
waman yuqatil fee sabeeli Allahifayuqtal aw yaghlib fasawfa nu/teehi ajran
AAatheema
Hausa
Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin
hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa
ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.
|
Ayah 4:75 الأية
وَمَا لَكُمْ لَا تُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ وَالْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ
الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالْوِلْدَانِ الَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا أَخْرِجْنَا
مِنْ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ الظَّالِمِ أَهْلُهَا وَاجْعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ
وَلِيًّا وَاجْعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ نَصِيرًا
Wama lakum la tuqatiloonafee sabeeli Allahi walmustadAAafeena mina
arrijaliwannisa-i walwildani allatheenayaqooloona rabbana akhrijna min
hathihialqaryati aththalimi ahluhawajAAal lana min ladunka waliyyan wajAAallana
min ladunka naseera
Hausa
Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka
raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu
daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana
majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
|
Ayah 4:76 الأية
الَّذِينَ آمَنُوا يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا
يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ الطَّاغُوتِ فَقَاتِلُوا أَوْلِيَاءَ الشَّيْطَانِ ۖ
إِنَّ كَيْدَ الشَّيْطَانِ كَانَ ضَعِيفًا
Allatheena amanoo yuqatiloonafee sabeeli Allahi wallatheena kafaroo
yuqatiloonafee sabeeli attaghooti faqatiloo awliyaaashshaytani inna kayda
ashshaytanikana daAAeefa
Hausa
Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta
sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle
ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
|
Ayah 4:77 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ قِيلَ لَهُمْ كُفُّوا أَيْدِيَكُمْ وَأَقِيمُوا
الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقِتَالُ إِذَا
فَرِيقٌ مِّنْهُمْ يَخْشَوْنَ النَّاسَ كَخَشْيَةِ اللهِ أَوْ أَشَدَّ خَشْيَةً ۚ
وَقَالُوا رَبَّنَا لِمَ كَتَبْتَ عَلَيْنَا الْقِتَالَ لَوْلَا أَخَّرْتَنَا
إِلَىٰ أَجَلٍ قَرِيبٍ ۗ قُلْ مَتَاعُ الدُّنْيَا قَلِيلٌ وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ
لِّمَنِ اتَّقَىٰ وَلَا تُظْلَمُونَ فَتِيلًا
Alam tara ila allatheena qeelalahum kuffoo aydiyakum waaqeemoo assalatawaatoo
azzakata falamma kutibaAAalayhimu alqitalu itha fareequn minhum yakhshawnaannasa
kakhashyati Allahi aw ashaddakhashyatan waqaloo rabbana lima katabta
AAalaynaalqitala lawla akhkhartana ila ajalinqareebin qul mataAAu addunya
qaleelun wal-akhiratukhayrun limani ittaqa wala tuthlamoonafateela
Hausa
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku
tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi
sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa
mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a
kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin
dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a
zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
|
Ayah 4:78 الأية
أَيْنَمَا تَكُونُوا يُدْرِككُّمُ الْمَوْتُ وَلَوْ كُنتُمْ فِي بُرُوجٍ
مُّشَيَّدَةٍ ۗ وَإِن تُصِبْهُمْ حَسَنَةٌ يَقُولُوا هَٰذِهِ مِنْ عِندِ اللهِ ۖ
وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَقُولُوا هَٰذِهِ مِنْ عِندِكَ ۚ قُلْ كُلٌّ مِّنْ
عِندِ اللهِ ۖ فَمَالِ هَٰؤُلَاءِ الْقَوْمِ لَا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ حَدِيثًا
Aynama takoonoo yudrikkumu almawtuwalaw kuntum fee buroojin mushayyadatin wa-in
tusibhum hasanatunyaqooloo hathihi min AAindi Allahi wa-in tusibhumsayyi-atun
yaqooloo hathihi min AAindika qul kullun minAAindi Allahi famali haola-i
alqawmila yakadoona yafqahoona hadeetha
Hausa
"Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin
gãnuwõyi ingãtattu!"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga
wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka
ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su
kusantar fahimtar magana?
|
Ayah 4:79 الأية
مَّا أَصَابَكَ مِنْ حَسَنَةٍ فَمِنَ اللهِ ۖ وَمَا أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٍ
فَمِن نَّفْسِكَ ۚ وَأَرْسَلْنَاكَ لِلنَّاسِ رَسُولًا ۚ وَكَفَىٰ بِاللهِ
شَهِيدًا
Ma asabaka min hasanatinfamina Allahi wama asabaka min sayyi-atinfamin nafsika
waarsalnaka linnasi rasoolanwakafa billahi shaheedan
Hausa
Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka
daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo,
kuma Allah Yã isa ga zama shaida.
|
Ayah 4:80 الأية
مَّن يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللهَ ۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَا
أَرْسَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا
Man yutiAAi arrasoola faqad ataAAaAllaha waman tawalla fama arsalnakaAAalayhim
hafeetha
Hausa
Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya
bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.
|
Ayah 4:81 الأية
وَيَقُولُونَ طَاعَةٌ فَإِذَا بَرَزُوا مِنْ عِندِكَ بَيَّتَ طَائِفَةٌ مِّنْهُمْ
غَيْرَ الَّذِي تَقُولُ ۖ وَاللهُ يَكْتُبُ مَا يُبَيِّتُونَ ۖ فَأَعْرِضْ
عَنْهُمْ وَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللهِ وَكِيلًا
Wayaqooloona taAAatun fa-ithabarazoo min AAindika bayyata ta-ifatun minhum
ghayra allatheetaqoolu wallahu yaktubu ma yubayyitoonafaaAArid AAanhum
watawakkal AAala Allahiwakafa billahi wakeela
Hausa
Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya
daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na
rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su,
kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli.
|
Ayah 4:82 الأية
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ الْقُرْآنَ ۚ وَلَوْ كَانَ مِنْ عِندِ غَيْرِ اللهِ
لَوَجَدُوا فِيهِ اخْتِلَافًا كَثِيرًا
Afala yatadabbaroona alqur-anawalaw kana min AAindi ghayri Allahi lawajadoo
feehiikhtilafan katheera
Hausa
Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa,
dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa?
|
Ayah 4:83 الأية
وَإِذَا جَاءَهُمْ أَمْرٌ مِّنَ الْأَمْنِ أَوِ الْخَوْفِ أَذَاعُوا بِهِ ۖ وَلَوْ
رَدُّوهُ إِلَى الرَّسُولِ وَإِلَىٰ أُولِي الْأَمْرِ مِنْهُمْ لَعَلِمَهُ
الَّذِينَ يَسْتَنبِطُونَهُ مِنْهُمْ ۗ وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ
وَرَحْمَتُهُ لَاتَّبَعْتُمُ الشَّيْطَانَ إِلَّا قَلِيلًا
Wa-itha jaahum amrun minaal-amni awi alkhawfi athaAAoo bihi walaw raddoohu
ilaarrasooli wa-ila olee al-amri minhum laAAalimahuallatheena yastanbitoonahu
minhum walawla fadluAllahi AAalaykum warahmatuhu lattabaAAtumuashshaytana illa
qaleela
Hausa
Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã
sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne,
waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar
Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.
|
Ayah 4:84 الأية
فَقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفْسَكَ ۚ وَحَرِّضِ
الْمُؤْمِنِينَ ۖ عَسَى اللهُ أَن يَكُفَّ بَأْسَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ وَاللهُ
أَشَدُّ بَأْسًا وَأَشَدُّ تَنكِيلًا
Faqatil fee sabeeli Allahi latukallafu illa nafsaka waharridialmu/mineena AAasa
Allahu an yakuffa ba/sa allatheenakafaroo wallahu ashaddu ba/san waashaddu
tankeela
Hausa
Sabõda haka, ka yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a
kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin
waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin
azabtãwa.
|
Ayah 4:85 الأية
مَّن يَشْفَعْ شَفَاعَةً حَسَنَةً يَكُن لَّهُ نَصِيبٌ مِّنْهَا ۖ وَمَن يَشْفَعْ
شَفَاعَةً سَيِّئَةً يَكُن لَّهُ كِفْلٌ مِّنْهَا ۗ وَكَانَ اللهُ عَلَىٰ كُلِّ
شَيْءٍ مُّقِيتًا
Man yashfaAA shafaAAatan hasanatanyakun lahu naseebun minha waman yashfaAA
shafaAAatansayyi-atan yakun lahu kiflun minha wakana AllahuAAala kulli shay-in
muqeeta
Hausa
Wanda ya yi cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi
cẽto,cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan
dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci.
|
Ayah 4:86 الأية
وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ
إِنَّ اللهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَسِيبًا
Wa-itha huyyeetum bitahiyyatinfahayyoo bi-ahsana minha aw ruddoohainna Allaha
kana AAala kulli shay-in haseeba
Hausa
Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi
kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan
kõme Mai lissãfi.
|
Ayah 4:87 الأية
اللهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ لَيَجْمَعَنَّكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ
لَا رَيْبَ فِيهِ ۗ وَمَنْ أَصْدَقُ مِنَ اللهِ حَدِيثًا
Allahu la ilaha illahuwa layajmaAAannakum ila yawmi alqiyamati larayba feehi
waman asdaqu mina Allahi hadeetha
Hausa
Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra ku har zuwa ga Yinin
¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ãbãri.
|
Ayah 4:88 الأية
فَمَا لَكُمْ فِي الْمُنَافِقِينَ فِئَتَيْنِ وَاللهُ أَرْكَسَهُم بِمَا كَسَبُوا
ۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَهْدُوا مَنْ أَضَلَّ اللهُ ۖ وَمَن يُضْلِلِ اللهُ فَلَن
تَجِدَ لَهُ سَبِيلًا
Fama lakum fee almunafiqeenafi-atayni wallahu arkasahum bima kasabooatureedoona
an tahdoo man adalla Allahu waman yudliliAllahu falan tajida lahu sabeela
Hausa
To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa
Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku
shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi
wata hanya ba zuwa gare shi.
|
Ayah 4:89 الأية
وَدُّوا لَوْ تَكْفُرُونَ كَمَا كَفَرُوا فَتَكُونُونَ سَوَاءً ۖ فَلَا تَتَّخِذُوا
مِنْهُمْ أَوْلِيَاءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُوا فِي سَبِيلِ اللهِ ۚ فَإِن تَوَلَّوْا
فَخُذُوهُمْ وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ وَجَدتُّمُوهُمْ ۖ وَلَا تَتَّخِذُوا مِنْهُمْ
وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Waddoo law takfuroona kama kafaroofatakoonoona sawaan fala tattakhithoo
minhumawliyaa hatta yuhajiroo fee sabeeliAllahi fa-in tawallaw fakhuthoohum
waqtuloohumhaythu wajadtumoohum wala tattakhithoominhum waliyyan wala naseera
Hausa
Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda
haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar
Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka
sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki.
|
Ayah 4:90 الأية
إِلَّا الَّذِينَ يَصِلُونَ إِلَىٰ قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم مِّيثَاقٌ أَوْ
جَاءُوكُمْ حَصِرَتْ صُدُورُهُمْ أَن يُقَاتِلُوكُمْ أَوْ يُقَاتِلُوا قَوْمَهُمْ ۚ
وَلَوْ شَاءَ اللهُ لَسَلَّطَهُمْ عَلَيْكُمْ فَلَقَاتَلُوكُمْ ۚ فَإِنِ
اعْتَزَلُوكُمْ فَلَمْ يُقَاتِلُوكُمْ وَأَلْقَوْا إِلَيْكُمُ السَّلَمَ فَمَا
جَعَلَ اللهُ لَكُمْ عَلَيْهِمْ سَبِيلًا
Illa allatheena yasiloonaila qawmin baynakum wabaynahum meethaqun aw
jaookumhasirat sudooruhum an yuqatilookum awyuqatiloo qawmahum walaw shaa Allahu
lasallatahumAAalaykum falaqatalookum fa-ini iAAtazalookum falam
yuqatilookumwaalqaw ilaykumu assalama fama jaAAala Allahulakum AAalayhim sabeela
Hausa
Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su
akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci
ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su
ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba
su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya
ba, a gare ku, a kansu.
|
Ayah 4:91 الأية
سَتَجِدُونَ آخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأْمَنُوكُمْ وَيَأْمَنُوا قَوْمَهُمْ كُلَّ
مَا رُدُّوا إِلَى الْفِتْنَةِ أُرْكِسُوا فِيهَا ۚ فَإِن لَّمْ يَعْتَزِلُوكُمْ
وَيُلْقُوا إِلَيْكُمُ السَّلَمَ وَيَكُفُّوا أَيْدِيَهُمْ فَخُذُوهُمْ
وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ ثَقِفْتُمُوهُمْ ۚ وَأُولَٰئِكُمْ جَعَلْنَا لَكُمْ
عَلَيْهِمْ سُلْطَانًا مُّبِينًا
Satajidoona akhareena yureedoona anya/manookum waya/manoo qawmahum kulla ma
ruddoo ilaalfitnati orkisoo feeha fa-in lam yaAAtazilookum wayulqooilaykumu
assalama wayakuffoo aydiyahum fakhuthoohumwaqtuloohum haythu thaqiftumoohum
waola-ikumjaAAalna lakum AAalayhim sultanan mubeena
Hausa
Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da
yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su
nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to,
ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya
muku dalĩli bayyanannea kansu.
|
Ayah 4:92 الأية
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَن يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَأً ۚ وَمَن قَتَلَ
مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰ
أَهْلِهِ إِلَّا أَن يَصَّدَّقُوا ۚ فَإِن كَانَ مِن قَوْمٍ عَدُوٍّ لَّكُمْ وَهُوَ
مُؤْمِنٌ فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ ۖ وَإِن كَانَ مِن قَوْمٍ بَيْنَكُمْ
وَبَيْنَهُم مِّيثَاقٌ فَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ وَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ
مُّؤْمِنَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً
مِّنَ اللهِ ۗ وَكَانَ اللهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Wama kana limu/minin anyaqtula mu/minan illa khataan waman qatala
mu/minankhataan fatahreeru raqabatin mu/minatin wadiyatunmusallamatun ila ahlihi
illa an yassaddaqoofa-in kana min qawmin AAaduwwin lakum wahuwa mu/minun
fatahreeruraqabatin mu/minatin wa-in kana min qawmin baynakumwabaynahum
meethaqun fadiyatun musallamatun ilaahlihi watahreeru raqabatin mu/minatin faman
lam yajid fasiyamushahrayni mutatabiAAayni tawbatan mina Allahi wakanaAllahu
AAaleeman hakeema
Hausa
Kuma bã ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma
wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa
diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe)
ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta
wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da
tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta
wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin
tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
|
Ayah 4:93 الأية
وَمَن يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُّتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا
وَغَضِبَ اللهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا
Waman yaqtul mu/minan mutaAAammidan fajazaohujahannamu khalidan feeha waghadiba
AllahuAAalayhi walaAAanahu waaAAadda lahu AAathaban AAatheema
Hausa
Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana
madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya
yi masa tattalin azãba mai girma.
|
Ayah 4:94 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا ضَرَبْتُمْ فِي سَبِيلِ اللهِ
فَتَبَيَّنُوا وَلَا تَقُولُوا لِمَنْ أَلْقَىٰ إِلَيْكُمُ السَّلَامَ لَسْتَ
مُؤْمِنًا تَبْتَغُونَ عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فَعِندَ اللهِ مَغَانِمُ
كَثِيرَةٌ ۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبْلُ فَمَنَّ اللهُ عَلَيْكُمْ
فَتَبَيَّنُوا ۚ إِنَّ اللهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
Ya ayyuha allatheena amanooitha darabtum fee sabeeli Allahifatabayyanoo wala
taqooloo liman alqa ilaykumu assalamalasta mu/minan tabtaghoona AAarada
alhayatiaddunya faAAinda Allahi maghanimukatheeratun kathalika kuntum min qablu
famanna AllahuAAalaykum fatabayyanoo inna Allaha kana bimataAAmaloona khabeera
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi,
to, ku nẽmi bãyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã
Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai
ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an
nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni.Lalle ne Allah Yã
kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
|
Ayah 4:95 الأية
لَّا يَسْتَوِي الْقَاعِدُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ غَيْرُ أُولِي الضَّرَرِ
وَالْمُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۚ فَضَّلَ
اللهُ الْمُجَاهِدِينَ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ عَلَى الْقَاعِدِينَ
دَرَجَةً ۚ وَكُلًّا وَعَدَ اللهُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَفَضَّلَ اللهُ
الْمُجَاهِدِينَ عَلَى الْقَاعِدِينَ أَجْرًا عَظِيمًا
La yastawee alqaAAidoona minaalmu/mineena ghayru olee addarari walmujahidoonafee
sabeeli Allahi bi-amwalihim waanfusihim faddalaAllahu almujahideena
bi-amwalihimwaanfusihim AAala alqaAAideena darajatan wakullanwaAAada Allahu
alhusna wafaddala Allahualmujahideena AAala alqaAAideena ajran AAatheema
Hausa
Mãsu zama daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a
cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã
fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma
dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau . Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu
jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.
|
Ayah 4:96 الأية
دَرَجَاتٍ مِّنْهُ وَمَغْفِرَةً وَرَحْمَةً ۚ وَكَانَ اللهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Darajatin minhu wamaghfiratan warahmatanwakana Allahu ghafooran raheema
Hausa
Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne,
Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:97 الأية
إِنَّ الَّذِينَ تَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ ظَالِمِي أَنفُسِهِمْ قَالُوا فِيمَ
كُنتُمْ ۖ قَالُوا كُنَّا مُسْتَضْعَفِينَ فِي الْأَرْضِ ۚ قَالُوا أَلَمْ تَكُنْ
أَرْضُ اللهِ وَاسِعَةً فَتُهَاجِرُوا فِيهَا ۚ فَأُولَٰئِكَ مَأْوَاهُمْ
جَهَنَّمُ ۖ وَسَاءَتْ مَصِيرًا
Inna allatheena tawaffahumualmala-ikatu thalimee anfusihim qaloofeema kuntum
qaloo kunna mustadAAafeena feeal-ardi qaloo alam takun ardu AllahiwasiAAatan
fatuhajiroo feeha faola-ikama/wahum jahannamu wasaat maseera
Hausa
Lalle ne, waɗanda malã'ĩku suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar
kansu,sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance
waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance
mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makõmarsu Jahannama
ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
|
Ayah 4:98 الأية
إِلَّا الْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالْوِلْدَانِ لَا
يَسْتَطِيعُونَ حِيلَةً وَلَا يَهْتَدُونَ سَبِيلًا
Illa almustadAAafeena mina arrijaliwannisa-i walwildani layastateeAAoona
heelatan wala yahtadoonasabeela
Hausa
Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata
dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya.
|
Ayah 4:99 الأية
فَأُولَٰئِكَ عَسَى اللهُ أَن يَعْفُوَ عَنْهُمْ ۚ وَكَانَ اللهُ عَفُوًّا
غَفُورًا
Faola-ika AAasa Allahuan yaAAfuwa AAanhum wakana Allahu AAafuwwan ghafoora
Hausa
To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã
kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
|
Ayah 4:100 الأية
وَمَن يُهَاجِرْ فِي سَبِيلِ اللهِ يَجِدْ فِي الْأَرْضِ مُرَاغَمًا كَثِيرًا
وَسَعَةً ۚ وَمَن يَخْرُجْ مِن بَيْتِهِ مُهَاجِرًا إِلَى اللهِ وَرَسُولِهِ
ثُمَّ يُدْرِكْهُ الْمَوْتُ فَقَدْ وَقَعَ أَجْرُهُ عَلَى اللهِ ۗ وَكَانَ
اللهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Waman yuhajir fee sabeeli Allahiyajid fee al-ardi muraghaman katheeran
wasaAAatanwaman yakhruj min baytihi muhajiran ila Allahiwarasoolihi thumma
yudrik-hu almawtu faqad waqaAAa ajruhu AAalaAllahi wakana Allahu ghafooran
raheema
Hausa
Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren
jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa
ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa
tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:101 الأية
وَإِذَا ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَقْصُرُوا مِنَ
الصَّلَاةِ إِنْ خِفْتُمْ أَن يَفْتِنَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ إِنَّ
الْكَافِرِينَ كَانُوا لَكُمْ عَدُوًّا مُّبِينًا
Wa-itha darabtum fee al-ardifalaysa AAalaykum junahun an taqsuroo mina
assalatiin khiftum an yaftinakumu allatheena kafaroo inna alkafireenakanoo lakum
AAaduwwan mubeena
Hausa
Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage daga salla
idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun
kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.
|
Ayah 4:102 الأية
وَإِذَا كُنتَ فِيهِمْ فَأَقَمْتَ لَهُمُ الصَّلَاةَ فَلْتَقُمْ طَائِفَةٌ مِّنْهُم
مَّعَكَ وَلْيَأْخُذُوا أَسْلِحَتَهُمْ فَإِذَا سَجَدُوا فَلْيَكُونُوا مِن
وَرَائِكُمْ وَلْتَأْتِ طَائِفَةٌ أُخْرَىٰ لَمْ يُصَلُّوا فَلْيُصَلُّوا مَعَكَ
وَلْيَأْخُذُوا حِذْرَهُمْ وَأَسْلِحَتَهُمْ ۗ وَدَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ
تَغْفُلُونَ عَنْ أَسْلِحَتِكُمْ وَأَمْتِعَتِكُمْ فَيَمِيلُونَ عَلَيْكُم
مَّيْلَةً وَاحِدَةً ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن كَانَ بِكُمْ أَذًى مِّن
مَّطَرٍ أَوْ كُنتُم مَّرْضَىٰ أَن تَضَعُوا أَسْلِحَتَكُمْ ۖ وَخُذُوا حِذْرَكُمْ
ۗ إِنَّ اللهَ أَعَدَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا
Wa-itha kunta feehim faaqamta lahumuassalata faltaqum ta-ifatun minhummaAAaka
walya/khuthoo aslihatahum fa-ithasajadoo falyakoonoo min wara-ikum walta/ti
ta-ifatunokhra lam yusalloo falyusalloo maAAakawalya/khuthoo hithrahum
waaslihatahumwadda allatheena kafaroo law taghfuloona AAan
aslihatikumwaamtiAAatikum fayameeloona AAalaykum maylatan wahidatanwala junaha
AAalaykum in kana bikum athanmin matarin aw kuntum marda an tadaAAoo
aslihatakumwakhuthoo hithrakum inna AllahaaAAadda lilkafireena AAathaban muheena
Hausa
Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya
daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan
sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta)
waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su
riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna
shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma
bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa
kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle
ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa.
|
Ayah 4:103 الأية
فَإِذَا قَضَيْتُمُ الصَّلَاةَ فَاذْكُرُوا اللهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَىٰ
جُنُوبِكُمْ ۚ فَإِذَا اطْمَأْنَنتُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ ۚ إِنَّ الصَّلَاةَ
كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا
Fa-itha qadaytumu assalatafathkuroo Allaha qiyaman waquAAoodanwaAAala junoobikum
fa-itha itma/nantumfaaqeemoo assalata inna assalatakanat AAala almu/mineena
kitaban mawqoota
Hausa
Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan
sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã
kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.
|
Ayah 4:104 الأية
وَلَا تَهِنُوا فِي ابْتِغَاءِ الْقَوْمِ ۖ إِن تَكُونُوا تَأْلَمُونَ فَإِنَّهُمْ
يَأْلَمُونَ كَمَا تَأْلَمُونَ ۖ وَتَرْجُونَ مِنَ اللهِ مَا لَا يَرْجُونَ ۗ
وَكَانَ اللهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Wala tahinoo fee ibtigha-ialqawmi in takoonoo ta/lamoona fa-innahum ya/lamoona
kamata/lamoona watarjoona mina Allahi ma layarjoona wakana Allahu AAaleeman
hakeema
Hausa
Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to,
lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga
Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
|
Ayah 4:105 الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِتَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ
بِمَا أَرَاكَ اللهُ ۚ وَلَا تَكُن لِّلْخَائِنِينَ خَصِيمًا
Inna anzalna ilayka alkitababilhaqqi litahkuma bayna annasibima araka Allahu
wala takun lilkha-ineenakhaseema
Hausa
Lalle ne, Mũ, Mun saukar , zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci
a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma
dõmin mãsu yaudara.
|
Ayah 4:106 الأية
وَاسْتَغْفِرِ اللهَ ۖ إِنَّ اللهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Wastaghfiri Allaha inna Allahakana ghafooran raheema
Hausa
Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:107 الأية
وَلَا تُجَادِلْ عَنِ الَّذِينَ يَخْتَانُونَ أَنفُسَهُمْ ۚ إِنَّ اللهَ لَا
يُحِبُّ مَن كَانَ خَوَّانًا أَثِيمًا
Wala tujadil AAani allatheenayakhtanoona anfusahum inna Allaha la yuhibbuman
kana khawwanan atheema
Hausa
Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne
Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi.
|
Ayah 4:108 الأية
يَسْتَخْفُونَ مِنَ النَّاسِ وَلَا يَسْتَخْفُونَ مِنَ اللهِ وَهُوَ مَعَهُمْ
إِذْ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرْضَىٰ مِنَ الْقَوْلِ ۚ وَكَانَ اللهُ بِمَا
يَعْمَلُونَ مُحِيطًا
Yastakhfoona mina annasi walayastakhfoona mina Allahi wahuwa maAAahum
ithyubayyitoona ma la yarda mina alqawli wakanaAllahu bima yaAAmaloona muheeta
Hausa
Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi
Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi
daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
|
Ayah 4:109 الأية
هَا أَنتُمْ هَٰؤُلَاءِ جَادَلْتُمْ عَنْهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فَمَن
يُجَادِلُ اللهَ عَنْهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيْهِمْ
وَكِيلًا
Haantum haola-i jadaltumAAanhum fee alhayati addunya famanyujadilu Allaha
AAanhum yawma alqiyamati amman yakoonu AAalayhim wakeela
Hausa
Gã ku, yã waɗannan ! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya)a cikin rãyuwar
dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa
wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?
|
Ayah 4:110 الأية
وَمَن يَعْمَلْ سُوءًا أَوْ يَظْلِمْ نَفْسَهُ ثُمَّ يَسْتَغْفِرِ اللهَ يَجِدِ
اللهَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Waman yaAAmal soo-an aw yathlimnafsahu thumma yastaghfiri Allaha yajidi
Allahaghafooran raheema
Hausa
Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah
gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 4:111 الأية
وَمَن يَكْسِبْ إِثْمًا فَإِنَّمَا يَكْسِبُهُ عَلَىٰ نَفْسِهِ ۚ وَكَانَ اللهُ
عَلِيمًا حَكِيمًا
Waman yaksib ithman fa-innamayaksibuhu AAala nafsihi wakana AllahuAAaleeman
hakeema
Hausa
Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma
Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
|
Ayah 4:112 الأية
وَمَن يَكْسِبْ خَطِيئَةً أَوْ إِثْمًا ثُمَّ يَرْمِ بِهِ بَرِيئًا فَقَدِ
احْتَمَلَ بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Waman yaksib khatee-atan aw ithmanthumma yarmi bihi baree-an faqadi ihtamala
buhtananwa-ithman mubeena
Hausa
Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani
barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
|
Ayah 4:113 الأية
وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكَ وَرَحْمَتُهُ لَهَمَّت طَّائِفَةٌ مِّنْهُمْ أَن
يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّا أَنفُسَهُمْ ۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيْءٍ ۚ
وَأَنزَلَ اللهُ عَلَيْكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمْ تَكُن
تَعْلَمُ ۚ وَكَانَ فَضْلُ اللهِ عَلَيْكَ عَظِيمًا
Walawla fadlu AllahiAAalayka warahmatuhu lahammat ta-ifatun minhum anyudillooka
wama yudilloona illaanfusahum wama yadurroonaka min shay-in waanzalaAllahu
AAalayka alkitaba walhikmatawaAAallamaka ma lam takun taAAlamu wakana
fadluAllahi AAalayka AAatheema
Hausa
Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya
daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma
bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka,
kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã
kasance mai girma a gare ka.
|
Ayah 4:114 الأية
لَّا خَيْرَ فِي كَثِيرٍ مِّن نَّجْوَاهُمْ إِلَّا مَنْ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوْ
مَعْرُوفٍ أَوْ إِصْلَاحٍ بَيْنَ النَّاسِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ ابْتِغَاءَ
مَرْضَاتِ اللهِ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا
La khayra fee katheerin min najwahumilla man amara bisadaqatin aw maAAroofin aw
islahinbayna annasi waman yafAAal thalika ibtighaamardati Allahi fasawfa
nu/teehi ajran AAatheema
Hausa
Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da
wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata
haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
|
Ayah 4:115 الأية
وَمَن يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَىٰ وَيَتَّبِعْ
غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ ۖ
وَسَاءَتْ مَصِيرًا
Waman yushaqiqi arrasoolamin baAAdi ma tabayyana lahu alhuda wayattabiAAghayra
sabeeli almu/mineena nuwallihi ma tawallawanuslihi jahannama wasaat maseera
Hausa
Kuma wanda ya sãɓã wa Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi
wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi
da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
|
Ayah 4:116 الأية
إِنَّ اللهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن
يَشَاءُ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا
Inna Allaha la yaghfiru anyushraka bihi wayaghfiru ma doona thalika limanyashao
waman yushrik billahi faqad dalladalalan baAAeeda
Hausa
Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake
bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne
ya ɓace ɓata mai nĩsa.
|
Ayah 4:117 الأية
إِن يَدْعُونَ مِن دُونِهِ إِلَّا إِنَاثًا وَإِن يَدْعُونَ إِلَّا شَيْطَانًا
مَّرِيدًا
In yadAAoona min doonihi illa inathanwa-in yadAAoona illa shaytanan mareeda
Hausa
Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai
tsaurin kai.
|
Ayah 4:118 الأية
لَّعَنَهُ اللهُ ۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنْ عِبَادِكَ نَصِيبًا مَّفْرُوضًا
LaAAanahu Allahu waqalalaattakhithanna min AAibadika naseebanmafrooda
Hausa
Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke , daga
bãyinKa.
|
Ayah 4:119 الأية
وَلَأُضِلَّنَّهُمْ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمْ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُبَتِّكُنَّ آذَانَ
الْأَنْعَامِ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللهِ ۚ وَمَن يَتَّخِذِ
الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِّن دُونِ اللهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُّبِينًا
Walaodillannahum walaomanniyannahumwalaamurannahum falayubattikunna athana
al-anAAamiwalaamurannahum falayughayyirunna khalqa Allahiwaman yattakhithi
ashshaytana waliyyan mindooni Allahi faqad khasira khusranan mubeena
Hausa
"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle
ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su
dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin
Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.
|
|