Prev  

5. Surah Al-Mâ'idah سورة المائدة

  Next  



1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَوْفُوا بِالْعُقُودِ ۚ أُحِلَّتْ لَكُم بَهِيمَةُ الْأَنْعَامِ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ غَيْرَ مُحِلِّي الصَّيْدِ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۗ إِنَّ اللهَ يَحْكُمُ مَا يُرِيدُ
Ya ayyuha allatheena amanooawfoo bilAAuqoodi ohillat lakum baheematu al-anAAamiilla ma yutla AAalaykum ghayra muhilleeassaydi waantum hurumun inna Allahayahkumu ma yureed

Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dăɗi făce abin da ake karantăwa a kanku, bă kună măsu halattar da farauta ba alhăli kuwa kună măsu harama. Lalle ne, Allah Yană hukunta abin da yake nufi.

Ayah  5:2  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُحِلُّوا شَعَائِرَ اللهِ وَلَا الشَّهْرَ الْحَرَامَ وَلَا الْهَدْيَ وَلَا الْقَلَائِدَ وَلَا آمِّينَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّن رَّبِّهِمْ وَرِضْوَانًا ۚ وَإِذَا حَلَلْتُمْ فَاصْطَادُوا ۚ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ أَن صَدُّوكُمْ عَنِ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ أَن تَعْتَدُوا ۘ وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا اللهَ ۖ إِنَّ اللهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Ya ayyuha allatheena amanoola tuhilloo shaAAa-ira Allahi walaashshahra alharama wala alhadya walaalqala-ida wala ammeena albayta alharamayabtaghoona fadlan min rabbihim waridwananwa-itha halaltum fastadoo walayajrimannakum shanaanu qawmin an saddookum AAanialmasjidi alharami an taAAtadoo wataAAawanooAAala albirri wattaqwa wala taAAawanooAAala al-ithmi walAAudwani wattaqooAllaha inna Allaha shadeedu alAAiqab

Hausa
 
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmăni! kada ku halattar da ayyukan ibădar Allah game da hajji, kuma da wată mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rătayar raƙuman hadaya, kuma da măsu nufin ¦ăki mai alfarma, sună neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutăne ta ɗauke ku, dőmin sun kange ku daga Masallăci Mai alfarma, ga ku yi zălunci. Kuma ku taimaki jună a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zălunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.

Ayah  5:3  الأية
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى النُّصُبِ وَأَن تَسْتَقْسِمُوا بِالْأَزْلَامِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ الْيَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ ۚ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا ۚ فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِّإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hurrimat AAalaykumu almaytatu waddamuwalahmu alkhinzeeri wama ohilla lighayri Allahibihi walmunkhaniqatu walmawqoothatu walmutaraddiyatuwannateehatu wama akala assabuAAuilla ma thakkaytum wama thubihaAAala annusubi waan tastaqsimoo bil-azlamithalikum fisqun alyawma ya-isa allatheena kafaroomin deenikum fala takhshawhum wakhshawni alyawmaakmaltu lakum deenakum waatmamtu AAalaykum niAAmatee waradeetulakumu al-islama deenan famani idturra fee makhmasatinghayra mutajanifin li-ithmin fa-inna Allahaghafoorun raheem

Hausa
 
An haramta muku mũshe da jini da năman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da măƙararriya da jefaffiya da mai gangarőwa da sőkakkiya, da abin da măsu dăgi suka ci, făce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na căca wannan făsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kăfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabőda haka kada ku ji tsőronsu kuma ku ji tsőroNa. A yau Nă kammală muku addininku, Kuma Nă cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nă yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bă yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  5:4  الأية
يَسْأَلُونَكَ مَاذَا أُحِلَّ لَهُمْ ۖ قُلْ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ ۙ وَمَا عَلَّمْتُم مِّنَ الْجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ اللهُ ۖ فَكُلُوا مِمَّا أَمْسَكْنَ عَلَيْكُمْ وَاذْكُرُوا اسْمَ اللهِ عَلَيْهِ ۖ وَاتَّقُوا اللهَ ۚ إِنَّ اللهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Yas-aloonaka matha ohilla lahumqul ohilla lakumu attayyibatu wamaAAallamtum mina aljawarihi mukallibeenatuAAallimoonahunna mimma AAallamakumu Allahufakuloo mimma amsakna AAalaykum wathkurooisma Allahi AAalayhi wattaqoo Allaha innaAllaha sareeAAu alhisab

Hausa
 
Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa măsu dăɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga măsu yin mĩki, kună măsu sakinsu daga hannuwanku, kună sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabőda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawă ne.

Ayah  5:5  الأية
الْيَوْمَ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ ۖ وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْ ۖ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ إِذَا آتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِي أَخْدَانٍ ۗ وَمَن يَكْفُرْ بِالْإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Alyawma ohilla lakumu attayyibatuwataAAamu allatheena ootoo alkitaba hillunlakum wataAAamukum hillun lahum walmuhsanatumina almu/minati walmuhsanatu minaallatheena ootoo alkitaba min qablikum itha ataytumoohunnaojoorahunna muhsineena ghayra musafiheenawala muttakhithee akhdanin waman yakfur bil-eemanifaqad habita AAamaluhu wahuwa fee al-akhiratimina alkhasireen

Hausa
 
A yau an halatta muku abũbuwa măsu dăɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littăfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mătă măsu kămun kai daga muminai da mătă 'yă'ya daga waɗanda aka bai wa Littăfi a gabăninku idan kun je musu da sadăkőkinsu, kuna măsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bă măsu riƙon abőkai ba. Kuma wanda ya kăfirta da ĩmăni to, lalle ne aikinsa yă ɓăci, kuma shĩ, a cikin Lăhira, yană daga măsu hasăra.

Ayah  5:6  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ ۚ وَإِن كُنتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُم مِّنْهُ ۚ مَا يُرِيدُ اللهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُم مِّنْ حَرَجٍ وَلَٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooitha qumtum ila assalati faghsiloowujoohakum waaydiyakum ila almarafiqi wamsahoobiruoosikum waarjulakum ila alkaAAbayni wa-in kuntumjunuban fattahharoo wa-in kuntum marda awAAala safarin aw jaa ahadun minkum mina algha-itiaw lamastumu annisaa falam tajidoo maanfatayammamoo saAAeedan tayyiban famsahoobiwujoohikum waaydeekum minhu ma yureedu AllahuliyajAAala AAalaykum min harajin walakin yureeduliyutahhirakum waliyutimma niAAmatahu AAalaykumlaAAallakum tashkuroon

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni ! idan kun tăshi zuwa ga salla, to, ku wanke fuskőkinku da hannuwanku zuwa ga magincirőri, kuma ku yi shăfa ga kănunku, kuma ku (wanke) ƙafăfunku zuwa idănun săwu biyu. Kuma idan kun kasance măsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kő kuwa a kan tafiya, kő kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kăshi, kő kuka yi shăfayyar jună da mătă, sa'an nan ba ku sămi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shăfa ga fuskőkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bă Ya nufi dőmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yană nufi dőmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammăninku kună gődewa.

Ayah  5:7  الأية
وَاذْكُرُوا نِعْمَةَ اللهِ عَلَيْكُمْ وَمِيثَاقَهُ الَّذِي وَاثَقَكُم بِهِ إِذْ قُلْتُمْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ وَاتَّقُوا اللهَ ۚ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Wathkuroo niAAmata AllahiAAalaykum wameethaqahu allathee wathaqakumbihi ith qultum samiAAna waataAAna wattaqooAllaha inna Allaha AAaleemun bithati assudoor

Hausa
 
Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lőkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗă'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata."

Ayah  5:8  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ لِلَّهِ شُهَدَاءَ بِالْقِسْطِ ۖ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلَىٰ أَلَّا تَعْدِلُوا ۚ اعْدِلُوا هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللهَ ۚ إِنَّ اللهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
Ya ayyuha allatheena amanookoonoo qawwameena lillahi shuhadaa bilqistiwala yajrimannakum shanaanu qawmin AAala allataAAdiloo iAAdiloo huwa aqrabu littaqwa wattaqooAllaha inna Allaha khabeerun bima taAAmaloon

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku kasance măsu tsayin daka dőmin Allah măsu shaida da ădalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bă ză ku yi ădalci ba. Ku yi ădalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatăwa.

Ayah  5:9  الأية
وَعَدَ اللهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۙ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ
WaAAada Allahu allatheena amanoowaAAamiloo assalihati lahum maghfiratunwaajrun AAatheem

Hausa
 
Allah Yă yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sună da wata găfara da lăda mai girma.

Ayah  5:10  الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Wallatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina ola-ika as-habualjaheem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta, kuma suka ƙaryată, game da ăyőyinMu, waɗannan su ne abőkan wuta.

Ayah  5:11  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا نِعْمَتَ اللهِ عَلَيْكُمْ إِذْ هَمَّ قَوْمٌ أَن يَبْسُطُوا إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ فَكَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ ۖ وَاتَّقُوا اللهَ ۚ وَعَلَى اللهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooothkuroo niAAmata Allahi AAalaykum ith hammaqawmun an yabsutoo ilaykum aydiyahum fakaffa aydiyahumAAankum wattaqoo Allaha waAAala Allahifalyatawakkali almu/minoon

Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lőkacin da wasu mutăne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.

Ayah  5:12  الأية
وَلَقَدْ أَخَذَ اللهُ مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَبَعَثْنَا مِنْهُمُ اثْنَيْ عَشَرَ نَقِيبًا ۖ وَقَالَ اللهُ إِنِّي مَعَكُمْ ۖ لَئِنْ أَقَمْتُمُ الصَّلَاةَ وَآتَيْتُمُ الزَّكَاةَ وَآمَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرْتُمُوهُمْ وَأَقْرَضْتُمُ اللهَ قَرْضًا حَسَنًا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَلَأُدْخِلَنَّكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ فَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَٰلِكَ مِنكُمْ فَقَدْ ضَلَّ سَوَاءَ السَّبِيلِ
Walaqad akhatha Allahu meethaqabanee isra-eela wabaAAathna minhumu ithnay AAasharanaqeeban waqala Allahu innee maAAakum la-inaqamtumu assalata waataytumu azzakatawaamantum birusulee waAAazzartumoohum waaqradtumuAllaha qardan hasanan laokaffiranna AAankumsayyi-atikum walaodkhilannakum jannatin tajree mintahtiha al-anharu faman kafara baAAda thalikaminkum faqad dalla sawaa assabeel

Hausa
 
Kuma lalle Allah Yă riƙi alkawarin Banĩ lsră' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gőma shă biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Ină tăre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun băyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Ină kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Ină shigar da ku gidăjen Aljanna (waɗanda) ƙőramu sană gudăna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kăfirta a băyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yă ɓace daga tsakar hanya."

Ayah  5:13  الأية
فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَاقَهُمْ لَعَنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً ۖ يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ ۙ وَنَسُوا حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا بِهِ ۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَائِنَةٍ مِّنْهُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۖ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ ۚ إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Fabima naqdihim meethaqahumlaAAannahum wajaAAalna quloobahum qasiyatanyuharrifoona alkalima AAan mawadiAAihi wanasoo haththanmimma thukkiroo bihi wala tazalu tattaliAAuAAala kha-inatin minhum illa qaleelan minhumfaAAfu AAanhum wasfah inna Allahayuhibbu almuhsineen

Hausa
 
To, sabőda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukătansu ƙeƙasassu, sună karkatar da magana daga wurărenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunătar da su da shi, kuma bă ză ka gushe ba kana tsinkăyar yaudara daga gare su făce kaɗan daga gare su. To, ka yăfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yană son măsu kyautatăwa.

Ayah  5:14  الأية
وَمِنَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّا نَصَارَىٰ أَخَذْنَا مِيثَاقَهُمْ فَنَسُوا حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا بِهِ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ ۚ وَسَوْفَ يُنَبِّئُهُمُ اللهُ بِمَا كَانُوا يَصْنَعُونَ
Wamina allatheena qaloo innanasara akhathna meethaqahumfanasoo haththan mimma thukkiroobihi faaghrayna baynahumu alAAadawata walbaghdaaila yawmi alqiyamati wasawfa yunabbi-ohumu Allahubima kanoo yasnaAAoon

Hausa
 
Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasăra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunătar da su da shi, sai Muka shushuta adăwa da ƙeta a tsakăninsu har ya zuwa ga Rănar ˇiyăma. Kuma Allah zai bă su lăbari da abin da suka kasance sună sană'antawa.

Ayah  5:15  الأية
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيرًا مِّمَّا كُنتُمْ تُخْفُونَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَعْفُو عَن كَثِيرٍ ۚ قَدْ جَاءَكُم مِّنَ اللهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُّبِينٌ
Ya ahla alkitabi qad jaakumrasooluna yubayyinu lakum katheeran mimma kuntumtukhfoona mina alkitabi wayaAAfoo AAan katheerin qad jaakummina Allahi noorun wakitabun mubeen

Hausa
 
Yă Mutănen littăfi! Lalle ne, ManzonMu yă je muku, yană bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kună ɓőyewa daga Littăfi, kuma yană rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa,wani haske da wani Littafi mai bayyanăwa yă je muku daga Allah.

Ayah  5:16  الأية
يَهْدِي بِهِ اللهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلَامِ وَيُخْرِجُهُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Yahdee bihi Allahu mani ittabaAAa ridwanahusubula assalami wayukhrijuhum mina aththulumatiila annoori bi-ithnihi wayahdeehim ilasiratin mustaqeem

Hausa
 
Dashĩ, Allah Yană shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyőyin aminci, kuma Yană fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yană shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.

Ayah  5:17  الأية
لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ ۚ قُلْ فَمَن يَمْلِكُ مِنَ اللهِ شَيْئًا إِنْ أَرَادَ أَن يُهْلِكَ الْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ۗ وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Laqad kafara allatheena qalooinna Allaha huwa almaseehu ibnu maryama qul famanyamliku mina Allahi shay-an in arada an yuhlikaalmaseeha ibna maryama waommahu waman fee al-ardijameeAAan walillahi mulku assamawatiwal-ardi wama baynahuma yakhluqu mayashao wallahu AAala kulli shay-inqadeer

Hausa
 
Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kăfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yă nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabă ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu, Yană halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kőme, Mai ĩkon yi ne.

Ayah  5:18  الأية
وَقَالَتِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَىٰ نَحْنُ أَبْنَاءُ اللهِ وَأَحِبَّاؤُهُ ۚ قُلْ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُم ۖ بَلْ أَنتُم بَشَرٌ مِّمَّنْ خَلَقَ ۚ يَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ ۚ وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ
Waqalati alyahoodu wannasaranahnu abnao Allahi waahibbaohuqul falima yuAAaththibukum bithunoobikum bal antumbasharun mimman khalaqa yaghfiru liman yashao wayuAAaththibuman yashao walillahi mulku assamawatiwal-ardi wama baynahuma wa-ilayhialmaseer

Hausa
 
Kuma Yahudu da Nasăra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masőyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azăba da zunubanku? Ă'a ku mutăne ne daga waɗanda Ya halitta, Yană găfartăwa ga wanda Yake so, kuma Yană azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakăninsu kuma zuwa gare shi makomă take."

Ayah  5:19  الأية
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلَىٰ فَتْرَةٍ مِّنَ الرُّسُلِ أَن تَقُولُوا مَا جَاءَنَا مِن بَشِيرٍ وَلَا نَذِيرٍ ۖ فَقَدْ جَاءَكُم بَشِيرٌ وَنَذِيرٌ ۗ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Ya ahla alkitabi qad jaakumrasooluna yubayyinu lakum AAala fatratin mina arrusulian taqooloo ma jaana min basheerin walanatheerin faqad jaakum basheerun wanatheerunwallahu AAala kulli shay-in qadeer

Hausa
 
Yă Mutănen Littăfi! Lalle ManzonMu yă je muku yană bayyana muku, a kan lőkacin fatara daga manzanni, dőmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushăra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai băyar da bushăra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kőme, Mai ĩkon yi.

Ayah  5:20  الأية
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللهِ عَلَيْكُمْ إِذْ جَعَلَ فِيكُمْ أَنبِيَاءَ وَجَعَلَكُم مُّلُوكًا وَآتَاكُم مَّا لَمْ يُؤْتِ أَحَدًا مِّنَ الْعَالَمِينَ
Wa-ith qala moosaliqawmihi ya qawmi othkuroo niAAmata AllahiAAalaykum ith jaAAala feekum anbiyaa wajaAAalakummulookan waatakum ma lam yu/ti ahadanmina alAAalameen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Musa ya ce wa mutănensa: "Yă ku mutănena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dőmin Yă sanya annabăwa a cikinku, kuma Yă sanya ku sarăkuna, kuma Yă bă ku abin da bai bai wa kőwa ba daga tălikai."

Ayah  5:21  الأية
يَا قَوْمِ ادْخُلُوا الْأَرْضَ الْمُقَدَّسَةَ الَّتِي كَتَبَ اللهُ لَكُمْ وَلَا تَرْتَدُّوا عَلَىٰ أَدْبَارِكُمْ فَتَنقَلِبُوا خَاسِرِينَ
Ya qawmi odkhuloo al-ardaalmuqaddasata allatee kataba Allahu lakum walatartaddoo AAala adbarikum fatanqaliboo khasireen

Hausa
 
"Yă mutănena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabőda ku, kuma kada ku kőma da băya, har ku juya kună măsu hasara."

Ayah  5:22  الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِنَّ فِيهَا قَوْمًا جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا حَتَّىٰ يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِن يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِنَّا دَاخِلُونَ
Qaloo ya moosa innafeeha qawman jabbareena wa-inna lannadkhulaha hatta yakhrujoo minhafa-in yakhrujoo minha fa-inna dakhiloon

Hausa
 
Suka ce: "Ya Musă! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutăne măsu ƙarfi kuma lalle ne bă ză mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."

Ayah  5:23  الأية
قَالَ رَجُلَانِ مِنَ الَّذِينَ يَخَافُونَ أَنْعَمَ اللهُ عَلَيْهِمَا ادْخُلُوا عَلَيْهِمُ الْبَابَ فَإِذَا دَخَلْتُمُوهُ فَإِنَّكُمْ غَالِبُونَ ۚ وَعَلَى اللهِ فَتَوَكَّلُوا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Qala rajulani mina allatheenayakhafoona anAAama Allahu AAalayhimaodkhuloo AAalayhimu albaba fa-itha dakhaltumoohufa-innakum ghaliboona waAAala Allahifatawakkaloo in kuntum mu/mineen

Hausa
 
Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsőron Allah, Allah Yă yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙőfar, dőmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, măsu rinjăya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."

Ayah  5:24  الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا أَبَدًا مَّا دَامُوا فِيهَا ۖ فَاذْهَبْ أَنتَ وَرَبُّكَ فَقَاتِلَا إِنَّا هَاهُنَا قَاعِدُونَ
Qaloo ya moosa innalan nadkhulaha abadan ma damoo feehafa-ithhab anta warabbuka faqatila innahahuna qaAAidoon

Hausa
 
Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bă za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dőmin ku yi yăƙi. Lalle ne mu, mună a nan zaune."

Ayah  5:25  الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي لَا أَمْلِكُ إِلَّا نَفْسِي وَأَخِي ۖ فَافْرُقْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ
Qala rabbi innee la amliku illanafsee waakhee fafruq baynana wabayna alqawmi alfasiqeen

Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijina! Lalle ne nĩ, bă ni mallakar kőwa făce kaina da ɗan'uwăna, sai Ka rarrabe a tsakăninmu da tsakănin mutăne făsiƙai."

Ayah  5:26  الأية
قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيْهِمْ ۛ أَرْبَعِينَ سَنَةً ۛ يَتِيهُونَ فِي الْأَرْضِ ۚ فَلَا تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ
Qala fa-innaha muharramatunAAalayhim arbaAAeena sanatan yateehoona fee al-ardi falata/sa AAala alqawmi alfasiqeen

Hausa
 
(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtăwa ce a gare su, shekara arba'in, sună yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabőda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutăne făsiƙai."

Ayah  5:27  الأية
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ابْنَيْ آدَمَ بِالْحَقِّ إِذْ قَرَّبَا قُرْبَانًا فَتُقُبِّلَ مِنْ أَحَدِهِمَا وَلَمْ يُتَقَبَّلْ مِنَ الْآخَرِ قَالَ لَأَقْتُلَنَّكَ ۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ
Watlu AAalayhim nabaa ibnay adamabilhaqqi ith qarraba qurbananfatuqubbila min ahadihima walam yutaqabbal mina al-akhariqala laaqtulannaka qala innama yataqabbaluAllahu mina almuttaqeen

Hausa
 
Kuma karantă musu lăbărin ɗiya biyu na Ădamu, da gaskiya, a lőkacin da suka băyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓă daga măsu taƙawa ne."

Ayah  5:28  الأية
لَئِن بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقْتُلَنِي مَا أَنَا بِبَاسِطٍ يَدِيَ إِلَيْكَ لِأَقْتُلَكَ ۖ إِنِّي أَخَافُ اللهَ رَبَّ الْعَالَمِينَ
La-in basatta ilayya yadakalitaqtulanee ma ana bibasitin yadiyailayka li-aqtulaka innee akhafu Allaha rabba alAAalameen

Hausa
 
"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dőmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dőmin in kashe ka. Lalle ne nĩ ină tsőron Allah Ubangijin tălikai.

Ayah  5:29  الأية
إِنِّي أُرِيدُ أَن تَبُوءَ بِإِثْمِي وَإِثْمِكَ فَتَكُونَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ ۚ وَذَٰلِكَ جَزَاءُ الظَّالِمِينَ
Innee oreedu an taboo-a bi-ithmee wa-ithmikafatakoona min as-habi annari wathalikajazao aththalimeen

Hausa
 
"Lalle ne nĩ ină nufin ka kőma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abőkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzălumai."

Ayah  5:30  الأية
فَطَوَّعَتْ لَهُ نَفْسُهُ قَتْلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُ فَأَصْبَحَ مِنَ الْخَاسِرِينَ
FatawwaAAat lahu nafsuhu qatlaakheehi faqatalahu faasbaha mina alkhasireen

Hausa
 
Sai ransa ya ƙawătar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga măsu hasăra.

Ayah  5:31  الأية
فَبَعَثَ اللهُ غُرَابًا يَبْحَثُ فِي الْأَرْضِ لِيُرِيَهُ كَيْفَ يُوَارِي سَوْءَةَ أَخِيهِ ۚ قَالَ يَا وَيْلَتَا أَعَجَزْتُ أَنْ أَكُونَ مِثْلَ هَٰذَا الْغُرَابِ فَأُوَارِيَ سَوْءَةَ أَخِي ۖ فَأَصْبَحَ مِنَ النَّادِمِينَ
FabaAAatha Allahu ghuraban yabhathufee al-ardi liyuriyahu kayfa yuwaree saw-ataakheehi qala ya waylata aAAajaztu an akoonamithla hatha alghurabi faowariya saw-ataakhee faasbaha mina annadimeen

Hausa
 
Sai Allah Ya aiki wani hankăka, yană tőno a cikin ƙasa dőmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe găwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitőna! Nă kăsa in kasance kamar wannan hankăka dőmin in turbuɗe găwar ɗan'uwana?" Sai ya wăyi gari daga măsu nadămă.

Ayah  5:32  الأية
مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعًا وَمَنْ أَحْيَاهَا فَكَأَنَّمَا أَحْيَا النَّاسَ جَمِيعًا ۚ وَلَقَدْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِالْبَيِّنَاتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم بَعْدَ ذَٰلِكَ فِي الْأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ
Min ajli thalika katabna AAalabanee isra-eela annahu man qatala nafsan bighayri nafsinaw fasadin fee al-ardi fakaannama qatala annasajameeAAan waman ahyaha fakaannama ahyaannasa jameeAAan walaqad jaat-hum rusulunabilbayyinati thumma inna katheeran minhum baAAda thalikafee al-ardi lamusrifoon

Hausa
 
Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsră'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bă da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yă kashe mutăne duka ne, kuma wanda ya răya rai, to, kamar yă răyar da mutăne ne gabă ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjőji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, măsu yawa daga gare su, a băyan wannan, haƙĩƙa, măsuɓarna ne a cikin ƙasa.

Ayah  5:33  الأية
إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ ۚ ذَٰلِكَ لَهُمْ خِزْيٌ فِي الدُّنْيَا ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Innama jazao allatheenayuhariboona Allaha warasoolahu wayasAAawna feeal-ardi fasadan an yuqattaloo aw yusallabooaw tuqattaAAa aydeehim waarjuluhum min khilafin awyunfaw mina al-ardi thalika lahum khizyun fee addunyawalahum fee al-akhirati AAathabun AAatheem

Hausa
 
Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yăƙin Allah da Manzonsa, kuma sună aiki a cikin ƙasa dőmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kő kuwa a kakkătse hannuwansu da ƙafăfunsu daga săɓăni, ko kuwa a kőre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin răyuwar duniya, kuma a Lăhira sună da wata azăba mai girma.

Ayah  5:34  الأية
إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا مِن قَبْلِ أَن تَقْدِرُوا عَلَيْهِمْ ۖ فَاعْلَمُوا أَنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Illa allatheena taboomin qabli an taqdiroo AAalayhim faAAlamoo anna Allahaghafoorun raheem

Hausa
 
Făce fa waɗanda suka tuba tun a gabănin ku sămi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  5:35  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooittaqoo Allaha wabtaghoo ilayhi alwaseelata wajahidoofee sabeelihi laAAallakum tuflihoon

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihădi a cikin hanyarsa, tsammăninku, za ku ci nasara.

Ayah  5:36  الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُ مَعَهُ لِيَفْتَدُوا بِهِ مِنْ عَذَابِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنْهُمْ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Inna allatheena kafaroo law annalahum ma fee al-ardi jameeAAan wamithlahu maAAahuliyaftadoo bihi min AAathabi yawmi alqiyamati matuqubbila minhum walahum AAathabun aleem

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka kăfirta, lalle dă sună da abin da ke a cikin ƙasa gabă ɗaya da misălinsa tăre da shi, dőmin su yi fansa da shi daga azăbar Rănar ˇiyăma, bă a karɓarsa daga gare su, kuma sună da azăba mai raɗadi.

Ayah  5:37  الأية
يُرِيدُونَ أَن يَخْرُجُوا مِنَ النَّارِ وَمَا هُم بِخَارِجِينَ مِنْهَا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ
Yureedoona an yakhrujoo mina annariwama hum bikharijeena minha walahum AAathabunmuqeem

Hausa
 
Sună nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama măsu fita daga gare ta ba, kuma sună da azăba zaunanniya.

Ayah  5:38  الأية
وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءً بِمَا كَسَبَا نَكَالًا مِّنَ اللهِ ۗ وَاللهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Wassariqu wassariqatufaqtaAAoo aydiyahuma jazaan bimakasaba nakalan mina Allahi wallahuAAazeezun hakeem

Hausa
 
Kuma ɓarăwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azăba daga Allah. Kuma Allah Mabuwăyi ne, Mai hikima.

Ayah  5:39  الأية
فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Faman taba min baAAdi thulmihiwaaslaha fa-inna Allaha yatoobu AAalayhiinna Allaha ghafoorun raheem

Hausa
 
To, wanda ya tuba a băyan zăluncinsa, kuma ya gyăra (halinsa), to, lalle ne Allah Yană karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  5:40  الأية
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ ۗ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Alam taAAlam anna Allaha lahu mulku assamawatiwal-ardi yuAAaththibu man yashaowayaghfiru liman yashao wallahu AAalakulli shay-in qadeer

Hausa
 
Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yană azăbtar da wanda Yake so, kuma Yană yin găfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kőme, Mai ĩkon yi ne?

Ayah  5:41  الأية
يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ لَا يَحْزُنكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ مِنَ الَّذِينَ قَالُوا آمَنَّا بِأَفْوَاهِهِمْ وَلَمْ تُؤْمِن قُلُوبُهُمْ ۛ وَمِنَ الَّذِينَ هَادُوا ۛ سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ سَمَّاعُونَ لِقَوْمٍ آخَرِينَ لَمْ يَأْتُوكَ ۖ يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ مِن بَعْدِ مَوَاضِعِهِ ۖ يَقُولُونَ إِنْ أُوتِيتُمْ هَٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمْ تُؤْتَوْهُ فَاحْذَرُوا ۚ وَمَن يُرِدِ اللهُ فِتْنَتَهُ فَلَن تَمْلِكَ لَهُ مِنَ اللهِ شَيْئًا ۚ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَمْ يُرِدِ اللهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمْ ۚ لَهُمْ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Ya ayyuha arrasoolu layahzunka allatheena yusariAAoona fee alkufrimina allatheena qaloo amanna bi-afwahihimwalam tu/min quloobuhum wamina allatheena hadoosammaAAoona lilkathibi sammaAAoona liqawmin akhareenalam ya/tooka yuharrifoona alkalima min baAAdi mawadiAAihiyaqooloona in ooteetum hatha fakhuthoohu wa-in lamtu/tawhu fahtharoo waman yuridi Allahufitnatahu falan tamlika lahu mina Allahi shay-an ola-ikaallatheena lam yuridi Allahu an yutahhiraquloobahum lahum fee addunya khizyun walahum feeal-akhirati AAathabun AAatheem

Hausa
 
Yă kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kăfirci su ɓăta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmăni" da băkunansu, alhăli zukatansu ba su yi ĩmănin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) măsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sună karkatar da zance daga băyan wurarensa, sună cewa: "Idan an bă ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bă ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bă ză ka mallaka masa kőme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukătansu ba. Sună da kunya a cikin duniya, kuma sună da wata azăba mai girma a cikin 1ăhira.

Ayah  5:42  الأية
سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ أَكَّالُونَ لِلسُّحْتِ ۚ فَإِن جَاءُوكَ فَاحْكُم بَيْنَهُمْ أَوْ أَعْرِضْ عَنْهُمْ ۖ وَإِن تُعْرِضْ عَنْهُمْ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيْئًا ۖ وَإِنْ حَكَمْتَ فَاحْكُم بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ ۚ إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ
SammaAAoona lilkathibi akkaloonalissuhti fa-in jaooka fahkumbaynahum aw aAArid AAanhum wa-in tuAArid AAanhumfalan yadurrooka shay-an wa-in hakamta fahkumbaynahum bilqisti inna Allaha yuhibbualmuqsiteen

Hausa
 
Măsu yawan saurăre ga ƙarya ne, măsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakăninsu kő ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bă ză su cuce ka da kőme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakăninsu da ădalci. Lalle ne, Allah Yană son măsu ădalci.

Ayah  5:43  الأية
وَكَيْفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ التَّوْرَاةُ فِيهَا حُكْمُ اللهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوْنَ مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا أُولَٰئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ
Wakayfa yuhakkimoonaka waAAindahumu attawratufeeha hukmu Allahi thumma yatawallawna minbaAAdi thalika wama ola-ika bilmu/mineen

Hausa
 
Kuma yăya suke gabătar da kai ga hukunci, alhăli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sună karkacewa a băyan wannan? waɗannan bă muminai ba ne!

Ayah  5:44  الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا التَّوْرَاةَ فِيهَا هُدًى وَنُورٌ ۚ يَحْكُمُ بِهَا النَّبِيُّونَ الَّذِينَ أَسْلَمُوا لِلَّذِينَ هَادُوا وَالرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ بِمَا اسْتُحْفِظُوا مِن كِتَابِ اللهِ وَكَانُوا عَلَيْهِ شُهَدَاءَ ۚ فَلَا تَخْشَوُا النَّاسَ وَاخْشَوْنِ وَلَا تَشْتَرُوا بِآيَاتِي ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ
Inna anzalna attawratafeeha hudan wanoorun yahkumu biha annabiyyoonaallatheena aslamoo lillatheena hadoo warrabbaniyyoonawal-ahbaru bima istuhfithoomin kitabi Allahi wakanoo AAalayhi shuhadaafala takhshawoo annasa wakhshawniwala tashtaroo bi-ayatee thamanan qaleelanwaman lam yahkum bima anzala Allahu faola-ikahumu alkafiroon

Hausa
 
Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabăwa waɗanda suke sun sallamă, sună yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mălaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littăfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, măsu bă da shaida. To, kada ku ji tsőron mutăne kuma ku ji tsőroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ăyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.

Ayah  5:45  الأية
وَكَتَبْنَا عَلَيْهِمْ فِيهَا أَنَّ النَّفْسَ بِالنَّفْسِ وَالْعَيْنَ بِالْعَيْنِ وَالْأَنفَ بِالْأَنفِ وَالْأُذُنَ بِالْأُذُنِ وَالسِّنَّ بِالسِّنِّ وَالْجُرُوحَ قِصَاصٌ ۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِ فَهُوَ كَفَّارَةٌ لَّهُ ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
Wakatabna AAalayhim feeha annaannafsa binnafsi walAAayna bilAAayniwal-anfa bil-anfi walothuna bilothuniwassinna bissinni waljurooha qisasunfaman tasaddaqa bihi fahuwa kaffaratun lahu wamanlam yahkum bima anzala Allahu faola-ikahumu aththalimoon

Hausa
 
Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (ană kashe) rai sabőda rai, kuma (ană ɗebe) idő sabőda idő, kuma (ana katse) hanci sabőda hanci, kuma kunne sabőda kunne kuma haƙori sabőda haƙőri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffăra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzălumai.

Ayah  5:46  الأية
وَقَفَّيْنَا عَلَىٰ آثَارِهِم بِعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ ۖ وَآتَيْنَاهُ الْإِنجِيلَ فِيهِ هُدًى وَنُورٌ وَمُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ
Waqaffayna AAala atharihimbiAAeesa ibni maryama musaddiqan lima baynayadayhi mina attawrati waataynahual-injeela feehi hudan wanoorun wamusaddiqan limabayna yadayhi mina attawrati wahudan wamawAAithatanlilmuttaqeen

Hausa
 
Kuma Muka biyar a kan gurăbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yănă mai gaskatăwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bă shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yană mai gaskatăwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga măsu taƙawa.

Ayah  5:47  الأية
وَلْيَحْكُمْ أَهْلُ الْإِنجِيلِ بِمَا أَنزَلَ اللهُ فِيهِ ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
Walyahkum ahlu al-injeeli bimaanzala Allahu feehi waman lam yahkum bimaanzala Allahu faola-ika humu alfasiqoon

Hausa
 
Kuma sai mutănen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne făsiƙai.

Ayah  5:48  الأية
وَأَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ الْكِتَابِ وَمُهَيْمِنًا عَلَيْهِ ۖ فَاحْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللهُ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ عَمَّا جَاءَكَ مِنَ الْحَقِّ ۚ لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجًا ۚ وَلَوْ شَاءَ اللهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُمْ ۖ فَاسْتَبِقُوا الْخَيْرَاتِ ۚ إِلَى اللهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Waanzalna ilayka alkitaba bilhaqqimusaddiqan lima bayna yadayhi mina alkitabiwamuhayminan AAalayhi fahkum baynahum bimaanzala Allahu wala tattabiAA ahwaahum AAammajaaka mina alhaqqi likullin jaAAalna minkumshirAAatan waminhajan walaw shaa AllahulajaAAalakum ommatan wahidatan walakin liyabluwakumfeema atakum fastabiqoo alkhayratiila Allahi marjiAAukum jameeAAan fayunabbi-okum bimakuntum feehi takhtalifoon

Hausa
 
Kuma Mun saukar da Littăfi zuwa gare ka da gaskiya, yană mai gaskatăwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littăfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartăwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakăninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyőyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya . Ga kőwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dă Allah Yă so, dă Yă sanya ku al'umma guda, kuma amma dőmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bă ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makőmarku take gabă ɗaya. Sa'an nan Ya bă ku lăbări ga abin da kuka kasance kună săɓăwa a cikinsa.

Ayah  5:49  الأية
وَأَنِ احْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللهُ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ وَاحْذَرْهُمْ أَن يَفْتِنُوكَ عَن بَعْضِ مَا أَنزَلَ اللهُ إِلَيْكَ ۖ فَإِن تَوَلَّوْا فَاعْلَمْ أَنَّمَا يُرِيدُ اللهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعْضِ ذُنُوبِهِمْ ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ لَفَاسِقُونَ
Waani ohkum baynahum bimaanzala Allahu wala tattabiAA ahwaahum wahtharhuman yaftinooka AAan baAAdi ma anzala Allahuilayka fa-in tawallaw faAAlam annama yureedu Allahuan yuseebahum bibaAAdi thunoobihim wa-innakatheeran mina annasi lafasiqoon

Hausa
 
Kuma ka yi hukunci a tsakăninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyőyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga săshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya băya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya săme su da masĩfa ne sabőda săshen zunubansu. Kuma lalle ne, măsu yawa daga mutăne, haƙĩƙa, făsiƙai ne.

Ayah  5:50  الأية
أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ ۚ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللهِ حُكْمًا لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ
Afahukma aljahiliyyatiyabghoona waman ahsanu mina Allahu hukmanliqawmin yooqinoon

Hausa
 
Shin, hukuncin Jăhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabőda mutăne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmăni)?

Ayah  5:51  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tattakhithoo alyahooda wannasaraawliyaa baAAduhum awliyao baAAdinwaman yatawallahum minkum fa-innahu minhum inna Allaha layahdee alqawma aththalimeen

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasăra majiɓinta. Săshensu majiɓinci ne ga săshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yană daga gare su. Lalle Allah bă Ya shiryar da mutăne azzălumai.

Ayah  5:52  الأية
فَتَرَى الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يُسَارِعُونَ فِيهِمْ يَقُولُونَ نَخْشَىٰ أَن تُصِيبَنَا دَائِرَةٌ ۚ فَعَسَى اللهُ أَن يَأْتِيَ بِالْفَتْحِ أَوْ أَمْرٍ مِّنْ عِندِهِ فَيُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا أَسَرُّوا فِي أَنفُسِهِمْ نَادِمِينَ
Fatara allatheena feequloobihim maradun yusariAAoona feehim yaqooloonanakhsha an tuseebana da-iratun faAAasaAllahu an ya/tiya bilfathi aw amrin minAAindihi fayusbihoo AAala ma asarroofee anfusihim nadimeen

Hausa
 
Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sună tseren gaugawa a cikinsu, sună cewa: "Mună tsőron kada wata masĩfa ta săme mu." To, akwai tsammănin Allah Ya zo da buɗi, kő kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wăyi gari a kan abin da suka ɓőye a cikin zukatansu, sună măsu nadămă.

Ayah  5:53  الأية
وَيَقُولُ الَّذِينَ آمَنُوا أَهَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ أَقْسَمُوا بِاللهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ ۙ إِنَّهُمْ لَمَعَكُمْ ۚ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فَأَصْبَحُوا خَاسِرِينَ
Wayaqoolu allatheena amanoo ahaola-iallatheena aqsamoo billahi jahda aymanihiminnahum lamaAAakum habitat aAAmaluhum faasbahookhasireen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni sună cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyăkar rantsuwőyinsu, cewa su, lalle sună tăre da ku?" Ayyukansu sun ɓăci, sabőda haka suka wăyi gari sună măsu hasăra.

Ayah  5:54  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَن يَرْتَدَّ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَائِمٍ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ اللهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooman yartadda minkum AAan deenihi fasawfa ya/tee Allahubiqawmin yuhibbuhum wayuhibboonahu athillatinAAala almu/mineena aAAizzatin AAala alkafireenayujahidoona fee sabeeli Allahi wala yakhafoonalawmata la-imin thalika fadlu Allahiyu/teehi man yashao wallahu wasiAAunAAaleem

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutăne, Yană son su kuma sună son Sa, măsu tawălu'i a kan muminai măsu izza a kan kăfurai. Sună yin, jihădi a cikin hanyar Allah, kuma bă su tsőron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yană băyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.

Ayah  5:55  الأية
إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُوا الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ
Innama waliyyukumu Allahuwarasooluhu wallatheena amanoo allatheenayuqeemoona assalata wayu/toona azzakatawahum rakiAAoon

Hausa
 
Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmăni,waɗanda suke sună tsayar da salla kuma sună băyar da zakka kuma sună ruku'i,

Ayah  5:56  الأية
وَمَن يَتَوَلَّ اللهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آمَنُوا فَإِنَّ حِزْبَ اللهِ هُمُ الْغَالِبُونَ
Waman yatawalla Allaha warasoolahu wallatheenaamanoo fa-inna hizba Allahi humu alghaliboon

Hausa
 
Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmăni, to, ƙungiyar Allah sune măsu rinjăya.

Ayah  5:57  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَكُمْ هُزُوًا وَلَعِبًا مِّنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ وَالْكُفَّارَ أَوْلِيَاءَ ۚ وَاتَّقُوا اللهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tattakhithoo allatheena ittakhathoodeenakum huzuwan walaAAiban mina allatheena ootoo alkitabamin qablikum walkuffara awliyaa wattaqooAllaha in kuntum mu/mineen

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wăsa, daga waɗanda aka bai wa Littăfi daga gabăninku da kăfirai, masőya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.

Ayah  5:58  الأية
وَإِذَا نَادَيْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ اتَّخَذُوهَا هُزُوًا وَلَعِبًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْقِلُونَ
Wa-itha nadaytum ila assalatiittakhathooha huzuwan walaAAiban thalikabi-annahum qawmun la yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wăsa. Wannan dőmin lalle ne su, mutăne ne (waɗanda) bă su hankalta.

Ayah  5:59  الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ هَلْ تَنقِمُونَ مِنَّا إِلَّا أَنْ آمَنَّا بِاللهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلُ وَأَنَّ أَكْثَرَكُمْ فَاسِقُونَ
Qul ya ahla alkitabi haltanqimoona minna illa an amanna billahiwama onzila ilayna wama onzila min qabluwaanna aktharakum fasiqoon

Hausa
 
Ka ce: "Ya Mutănen Littăfi! Shin, kună ganin wani laifi daga gare mu? Făce dai dőmin mun yi ĩmăni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabăni, kuma dőmin mafi yawanku făsiƙai ne."

Ayah  5:60  الأية
قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ اللهِ ۚ مَن لَّعَنَهُ اللهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ الْقِرَدَةَ وَالْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ الطَّاغُوتَ ۚ أُولَٰئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ عَن سَوَاءِ السَّبِيلِ
Qul hal onabbi-okum bisharrin min thalikamathoobatan AAinda Allahi man laAAanahu Allahuwaghadiba AAalayhi wajaAAala minhumu alqiradata walkhanazeerawaAAabada attaghooti ola-ika sharrun makananwaadallu AAan sawa-i assabeel

Hausa
 
Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dőmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ăguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."

Ayah  5:61  الأية
وَإِذَا جَاءُوكُمْ قَالُوا آمَنَّا وَقَد دَّخَلُوا بِالْكُفْرِ وَهُمْ قَدْ خَرَجُوا بِهِ ۚ وَاللهُ أَعْلَمُ بِمَا كَانُوا يَكْتُمُونَ
Wa-itha jaookum qaloo amannawaqad dakhaloo bilkufri wahum qad kharajoo bihi wallahuaAAlamu bima kanoo yaktumoon

Hausa
 
Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmăni." Alhăli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kăfirci,kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sună ɓőyewa.

Ayah  5:62  الأية
وَتَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يُسَارِعُونَ فِي الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Watara katheeran minhum yusariAAoonafee al-ithmi walAAudwani waaklihimu assuhtalabi/sa ma kanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma kana ganin măsu yawa daga gare su, sună tseren gaugawa a cikin zunubi da zălunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatăwa.

Ayah  5:63  الأية
لَوْلَا يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ عَن قَوْلِهِمُ الْإِثْمَ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَصْنَعُونَ
Lawla yanhahumu arrabbaniyyoonawal-ahbaru AAan qawlihimu al-ithmawaaklihimu assuhta labi/sa ma kanooyasnaAAoon

Hausa
 
Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hană su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sună sană'antăwa.

Ayah  5:64  الأية
وَقَالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ ۚ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُوا بِمَا قَالُوا ۘ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَاءُ ۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَانًا وَكُفْرًا ۚ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ ۚ كُلَّمَا أَوْقَدُوا نَارًا لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا اللهُ ۚ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا ۚ وَاللهُ لَا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ
Waqalati alyahoodu yadu Allahimaghloolatun ghullat aydeehim waluAAinoo bima qaloobal yadahu mabsootatani yunfiqu kayfa yashaowalayazeedanna katheeran minhum ma onzila ilayka minrabbika tughyanan wakufran waalqaynabaynahumu alAAadawata walbaghdaa ilayawmi alqiyamati kullama awqadoo naran lilharbiatfaaha Allahu wayasAAawna fee al-ardifasadan wallahu la yuhibbualmufsideen

Hausa
 
Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabőda abin da suka faɗa. Ă'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yană ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yană ƙăra wa măsu yawa daga gare su, girman kai da kăfirci. Kuma Mun jefa a tsakăninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rănar ˇiyăma, kő da yaushe suka hura wata wuta dőmin yăƙi, sai Allah Ya bice ta. Sună aiki a cikin ƙasa dőmin ɓarna, alhăli kuwa Allah bă Ya son măsu fasădi.

Ayah  5:65  الأية
وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْكِتَابِ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَكَفَّرْنَا عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلَأَدْخَلْنَاهُمْ جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Walaw anna ahla alkitabi amanoowattaqaw lakaffarna AAanhum sayyi-atihimwalaadkhalnahum jannati annaAAeem

Hausa
 
Kuma dă dai lalle Mutănen Littăfi sun yi ĩmăni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dă Mun kankare miyăgun ayyukansu daga gare su, kuma dă Mun shigar da su gidăjen Aljannar Ni'ima.

Ayah  5:66  الأية
وَلَوْ أَنَّهُمْ أَقَامُوا التَّوْرَاةَ وَالْإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِم مِّن رَّبِّهِمْ لَأَكَلُوا مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِم ۚ مِّنْهُمْ أُمَّةٌ مُّقْتَصِدَةٌ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ سَاءَ مَا يَعْمَلُونَ
Walaw annahum aqamoo attawratawal-injeela wama onzila ilayhim min rabbihimlaakaloo min fawqihim wamin tahti arjulihim minhum ommatunmuqtasidatun wakatheerun minhum saa mayaAAmaloon

Hausa
 
Kuma dă dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dă sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafăfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaităwa kuma măsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yă munana.

Ayah  5:67  الأية
يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ۖ وَإِن لَّمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ ۚ وَاللهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ ۗ إِنَّ اللهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ
Ya ayyuha arrasooluballigh ma onzila ilayka min rabbika wa-in lam tafAAal famaballaghta risalatahu wallahu yaAAsimukamina annasi inna Allaha la yahdeealqawma alkafireen

Hausa
 
Yă kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yană tsare ka daga mutăne. Lalle ne, Allah bă Ya shiryar da mutăne kăfirai.

Ayah  5:68  الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَسْتُمْ عَلَىٰ شَيْءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُوا التَّوْرَاةَ وَالْإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ ۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَانًا وَكُفْرًا ۖ فَلَا تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ
Qul ya ahla alkitabi lastumAAala shay-in hatta tuqeemoo attawratawal-injeela wama onzila ilaykum min rabbikumwalayazeedanna katheeran minhum ma onzila ilayka minrabbika tughyanan wakufran fala ta/sa AAalaalqawmi alkafireen

Hausa
 
Ka ce: "Yă ku Mutănen Littăfi! Ba ku zama a kan kőme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yană ƙara wa măsu yawa daga gare su girman kai da kăfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutăne kăfirai.

Ayah  5:69  الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئُونَ وَالنَّصَارَىٰ مَنْ آمَنَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Inna allatheena amanoo wallatheenahadoo wassabi-oona wannasaraman amana billahi walyawmi al-akhiriwaAAamila salihan fala khawfun AAalayhim walahum yahzanoon

Hausa
 
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmăni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasăra, wanda ya yi ĩmăni da Allahda Rănar Lăhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, băbu tsőro a kansu, kuma bă su zamo sună baƙin ciki ba.

Ayah  5:70  الأية
لَقَدْ أَخَذْنَا مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَأَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ رُسُلًا ۖ كُلَّمَا جَاءَهُمْ رَسُولٌ بِمَا لَا تَهْوَىٰ أَنفُسُهُمْ فَرِيقًا كَذَّبُوا وَفَرِيقًا يَقْتُلُونَ
Laqad akhathna meethaqabanee isra-eela waarsalna ilayhim rusulan kullamajaahum rasoolun bima la tahwaanfusuhum fareeqan kaththaboo wafareeqan yaqtuloon

Hausa
 
Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isră'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da răyukansu bă su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sună kashewa,

Ayah  5:71  الأية
وَحَسِبُوا أَلَّا تَكُونَ فِتْنَةٌ فَعَمُوا وَصَمُّوا ثُمَّ تَابَ اللهُ عَلَيْهِمْ ثُمَّ عَمُوا وَصَمُّوا كَثِيرٌ مِّنْهُمْ ۚ وَاللهُ بَصِيرٌ بِمَا يَعْمَلُونَ
Wahasiboo alla takoonafitnatun faAAamoo wasammoo thumma taba AllahuAAalayhim thumma AAamoo wasammoo katheerun minhum wallahubaseerun bima yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bă ză ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta măsu yawa daga gare su, alhăli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatăwa.

Ayah  5:72  الأية
لَقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ ۖ وَقَالَ الْمَسِيحُ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اعْبُدُوا اللهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ ۖ إِنَّهُ مَن يُشْرِكْ بِاللهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ
Laqad kafara allatheena qalooinna Allaha huwa almaseehu ibnu maryama waqalaalmaseehu ya banee isra-eela oAAbudoo Allaharabbee warabbakum innahu man yushrik billahi faqadharrama Allahu AAalayhi aljannata wama/wahuannaru wama liththalimeenamin ansar

Hausa
 
Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kăfirta. Alhăli kuwa Masĩhu yă ce: "Yă Banĩ Isră'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yă haramta masa Aljanna. Kuma băbu wasu mataimaka ga azzălumai.

Ayah  5:73  الأية
لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللهَ ثَالِثُ ثَلَاثَةٍ ۘ وَمَا مِنْ إِلَٰهٍ إِلَّا إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۚ وَإِن لَّمْ يَنتَهُوا عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Laqad kafara allatheena qalooinna Allaha thalithu thalathatin wamamin ilahin illa ilahun wahidun wa-inlam yantahoo AAamma yaqooloona layamassanna allatheenakafaroo minhum AAathabun aleem

Hausa
 
Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kăfirta, kuma babu wani abin bautăwa făce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azăba mai raɗaɗi tănă shăfar waɗanda suka kăfirta daga gare su.

Ayah  5:74  الأية
أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى اللهِ وَيَسْتَغْفِرُونَهُ ۚ وَاللهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Afala yatooboona ila Allahiwayastaghfiroonahu wallahu ghafoorun raheem

Hausa
 
shin fă, bă su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi găfara, alhăli kuwa Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai?

Ayah  5:75  الأية
مَّا الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ وَأُمُّهُ صِدِّيقَةٌ ۖ كَانَا يَأْكُلَانِ الطَّعَامَ ۗ انظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ الْآيَاتِ ثُمَّ انظُرْ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Ma almaseehu ibnu maryama illarasoolun qad khalat min qablihi arrusulu waommuhu siddeeqatunkana ya/kulani attaAAamaonthur kayfa nubayyinu lahumu al-ayatithumma onthur anna yu/fakoon

Hausa
 
Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba făce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabăninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sună cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ăyőyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.

Ayah  5:76  الأية
قُلْ أَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا ۚ وَاللهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Qul ataAAbudoona min dooni Allahi mala yamliku lakum darran wala nafAAan wallahuhuwa assameeAAu alAAaleem

Hausa
 
Ka ce: "Ashe kună bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabőda ku kuma haka wani amfani alhăli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"

Ayah  5:77  الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ غَيْرَ الْحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُوا أَهْوَاءَ قَوْمٍ قَدْ ضَلُّوا مِن قَبْلُ وَأَضَلُّوا كَثِيرًا وَضَلُّوا عَن سَوَاءِ السَّبِيلِ
Qul ya ahla alkitabi lataghloo fee deenikum ghayra alhaqqi wala tattabiAAooahwaa qawmin qad dalloo min qablu waadallookatheeran wadalloo AAan sawa-i assabeel

Hausa
 
Ka ce: "Yă ku Mutanen Littăfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bă gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyőyin waɗansu mutăne waɗanda suka riga suka ɓace a gabăni, kuma suka ɓatar da wasu măsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya."

Ayah  5:78  الأية
لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَوا وَّكَانُوا يَعْتَدُونَ
LuAAina allatheena kafaroo min baneeisra-eela AAala lisani dawoodawaAAeesa ibni maryama thalika bima AAasawwakanoo yaAAtadoon

Hausa
 
An la'ani waɗanda suka kăfirta daga Banĩ Isră'ĩla a kan harshen Dăwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabőda săɓăwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi .

Ayah  5:79  الأية
كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَن مُّنكَرٍ فَعَلُوهُ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ
Kanoo la yatanahawnaAAan munkarin faAAaloohu labi/sa ma kanooyafAAaloon

Hausa
 
Sun kasance bă su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesună aikatăwa yă munana.

Ayah  5:80  الأية
تَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يَتَوَلَّوْنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ لَبِئْسَ مَا قَدَّمَتْ لَهُمْ أَنفُسُهُمْ أَن سَخِطَ اللهُ عَلَيْهِمْ وَفِي الْعَذَابِ هُمْ خَالِدُونَ
Tara katheeran minhum yatawallawnaallatheena kafaroo labi/sa ma qaddamat lahumanfusuhum an sakhita Allahu AAalayhim wafee alAAathabihum khalidoon

Hausa
 
Kana ganin măsu yawa daga gare su, sună jiɓintar waɗanda suka kăfirta. Haƙĩƙa tir da abin da răyukansu suka gabătar sabőda su, watau Allah Yă yi fushi da su, kuma a cikin azăba su măsu dawwama ne

Ayah  5:81  الأية
وَلَوْ كَانُوا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَالنَّبِيِّ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مَا اتَّخَذُوهُمْ أَوْلِيَاءَ وَلَٰكِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُمْ فَاسِقُونَ
Walaw kanoo yu/minoona billahiwannabiyyi wama onzila ilayhi ma ittakhathoohumawliyaa walakinna katheeran minhum fasiqoon

Hausa
 
Kuma dă sun kasance sună ĩmăni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dă ba su riƙe su masőya ba. Kuma amma măsu yawa daga gare su, făsiƙai ne.

Ayah  5:82  الأية
لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ النَّاسِ عَدَاوَةً لِّلَّذِينَ آمَنُوا الْيَهُودَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا ۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقْرَبَهُم مَّوَدَّةً لِّلَّذِينَ آمَنُوا الَّذِينَ قَالُوا إِنَّا نَصَارَىٰ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنْهُمْ قِسِّيسِينَ وَرُهْبَانًا وَأَنَّهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
Latajidanna ashadda annasiAAadawatan lillatheena amanoo alyahooda wallatheenaashrakoo walatajidanna aqrabahum mawaddatan lillatheena amanooallatheena qaloo inna nasara thalikabi-anna minhum qisseeseena waruhbanan waannahum layastakbiroon

Hausa
 
Lalle ne kana sămun mafiya tsananin mutăne a adăwa ga waɗanda suka yi ĩmăni,Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kană sămun mafiya kusantarsu a sőyayya ga waɗanda suka yi ĩmăni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasăra." Wancan kuwa sabőda akwai ˇissawa da ruhubănăwa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bă su yin girman kai.

Ayah  5:83  الأية
وَإِذَا سَمِعُوا مَا أُنزِلَ إِلَى الرَّسُولِ تَرَىٰ أَعْيُنَهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ مِمَّا عَرَفُوا مِنَ الْحَقِّ ۖ يَقُولُونَ رَبَّنَا آمَنَّا فَاكْتُبْنَا مَعَ الشَّاهِدِينَ
Wa-itha samiAAoo ma onzila ilaarrasooli tara aAAyunahum tafeedu mina addamAAimimma AAarafoo mina alhaqqi yaqooloona rabbanaamanna faktubna maAAa ashshahideen

Hausa
 
Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kană ganin idanunsu sună zubar da hawăye, sabőda abin da suka sani daga gaskiya, sună cewa: "Yă Ubangijinmu! Mun yi ĩmăni,sai ka rubuta mu tăre da măsu shaida.

Ayah  5:84  الأية
وَمَا لَنَا لَا نُؤْمِنُ بِاللهِ وَمَا جَاءَنَا مِنَ الْحَقِّ وَنَطْمَعُ أَن يُدْخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ الْقَوْمِ الصَّالِحِينَ
Wama lana la nu/minu billahiwama jaana mina alhaqqi wanatmaAAuan yudkhilana rabbuna maAAa alqawmi assaliheen

Hausa
 
"Kuma mene ne yake gare mu, bă ză mu yi ĩmăni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma mună gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tăre da mutăne sălihai?"

Ayah  5:85  الأية
فَأَثَابَهُمُ اللهُ بِمَا قَالُوا جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ جَزَاءُ الْمُحْسِنِينَ
Faathabahumu Allahu bimaqaloo jannatin tajree min tahtihaal-anharu khalideena feeha wathalikajazao almuhsineen

Hausa
 
Sabőda haka, Allah Yă săkă musu, dőmin abin da suka faɗa da gidăjen Aljanna (waɗanda) ƙőramu sună gudăna a ƙarƙashinsu, sună madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon măsu kyautatăwa.

Ayah  5:86  الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Wallatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina ola-ika as-habualjaheem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta kuma suka ƙaryata game da ăyőyinMu, waɗancan ne abőkan Wuta.

Ayah  5:87  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُحَرِّمُوا طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللهُ لَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوا ۚ إِنَّ اللهَ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tuharrimoo tayyibati ma ahallaAllahu lakum wala taAAtadoo inna Allaha layuhibbu almuAAtadeen

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku haramta abubuwa măsu dăɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bă Ya son măsu ƙetare haddi.

Ayah  5:88  الأية
وَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللهُ حَلَالًا طَيِّبًا ۚ وَاتَّقُوا اللهَ الَّذِي أَنتُم بِهِ مُؤْمِنُونَ
Wakuloo mimma razaqakumu Allahuhalalan tayyiban wattaqoo Allahaallathee antum bihi mu/minoon

Hausa
 
Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, măsu ĩmăni ne da shi.

Ayah  5:89  الأية
لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ الْأَيْمَانَ ۖ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
La yu-akhithukumu Allahubillaghwi fee aymanikum walakin yu-akhithukumbima AAaqqadtumu al-aymana fakaffaratuhu itAAamuAAasharati masakeena min awsati ma tutAAimoonaahleekum aw kiswatuhum aw tahreeru raqabatin faman lamyajid fasiyamu thalathati ayyamin thalikakaffaratu aymanikum itha halaftum wahfathooaymanakum kathalika yubayyinu Allahu lakum ayatihilaAAallakum tashkuroon

Hausa
 
Allah bă Ya kămă ku sabőda yăsassa a cikin rantsuwőyinku, kuma amma Yană kămă ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwőyi (a kansa). To, kaffărarsa ita ce ciyar da miskĩni gőma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyălanku, kő kuwa tufătar da su, kő kuwa 'yantăwar wuya. Sa'an nan wanda bai sămu ba, sai azumin kwăna uku. wannan ne kaffărar rantsuwőyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyăye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ăyoyinsa, tsammăninku kună gődewa.

Ayah  5:90  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooinnama alkhamru walmaysiru wal-ansabuwal-azlamu rijsun min AAamali ashshaytanifajtaniboohu laAAallakum tuflihoon

Hausa
 
Ya ku waɗanda suka yi ĩmăni! Abin sani kawai, giya da căca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.

Ayah  5:91  الأية
إِنَّمَا يُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُوقِعَ بَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ فِي الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَن ذِكْرِ اللهِ وَعَنِ الصَّلَاةِ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّنتَهُونَ
Innama yureedu ashshaytanuan yooqiAAa baynakumu alAAadawata walbaghdaafee alkhamri walmaysiri wayasuddakum AAan thikriAllahi waAAani assalati fahal antummuntahoon

Hausa
 
Abin sani kawaĩ Shaiɗan yană nufin ya aukar da adăwa da ƙeta a tsakăninku, a cikin giya da căca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku măsu hanuwa ne?

Ayah  5:92  الأية
وَأَطِيعُوا اللهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَاحْذَرُوا ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَاعْلَمُوا أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
WaateeAAoo Allaha waateeAAooarrasoola wahtharoo fa-in tawallaytum faAAlamooannama AAala rasoolina albalaghualmubeen

Hausa
 
Ku yi ɗă'a ga Allah, kuma ku yi ɗă'a ga Manzo, kuma ku kiyăye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.

Ayah  5:93  الأية
لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوا إِذَا مَا اتَّقَوا وَّآمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ثُمَّ اتَّقَوا وَّآمَنُوا ثُمَّ اتَّقَوا وَّأَحْسَنُوا ۗ وَاللهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Laysa AAala allatheena amanoowaAAamiloo assalihati junahun feemataAAimoo itha ma ittaqaw waamanoowaAAamiloo assalihati thumma ittaqaw waamanoothumma ittaqaw waahsanoo wallahu yuhibbualmuhsineen

Hausa
 
Băbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmăni,sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son măsu kyautatăwa.

Ayah  5:94  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَيَبْلُوَنَّكُمُ اللهُ بِشَيْءٍ مِّنَ الصَّيْدِ تَنَالُهُ أَيْدِيكُمْ وَرِمَاحُكُمْ لِيَعْلَمَ اللهُ مَن يَخَافُهُ بِالْغَيْبِ ۚ فَمَنِ اعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanoolayabluwannakumu Allahu bishay-in mina assayditanaluhu aydeekum warimahukum liyaAAlama Allahuman yakhafuhu bilghaybi famani iAAtadabaAAda thalika falahu AAathabun aleem

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da măsunku sună sămun sa dőmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a băyan wannan, to, yană da azăba mai raɗaɗi.

Ayah  5:95  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْتُلُوا الصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۚ وَمَن قَتَلَهُ مِنكُم مُّتَعَمِّدًا فَجَزَاءٌ مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ النَّعَمِ يَحْكُمُ بِهِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْيًا بَالِغَ الْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّارَةٌ طَعَامُ مَسَاكِينَ أَوْ عَدْلُ ذَٰلِكَ صِيَامًا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِ ۗ عَفَا اللهُ عَمَّا سَلَفَ ۚ وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ اللهُ مِنْهُ ۗ وَاللهُ عَزِيزٌ ذُو انتِقَامٍ
Ya ayyuha allatheena amanoola taqtuloo assayda waantum hurumunwaman qatalahu minkum mutaAAammidan fajazaon mithlu maqatala mina annaAAami yahkumu bihi thawaAAadlin minkum hadyan baligha alkaAAbati aw kaffaratuntaAAamu masakeena aw AAadlu thalika siyamanliyathooqa wabala amrihi AAafa AllahuAAamma salafa waman AAada fayantaqimu Allahuminhu wallahu AAazeezun thoo intiqam

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku kashe farauta alhăli kună măsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yană mai ganganci, sai sakamako misălin abin da ya kashe, daga dabbőbin ni'ima, ma'abuta ădalci biyu daga cikinku sună yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffăra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dőmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yă yafe laifi daga abin da ya gabăta. Kuma wanda ya kőma, to, Allah zai yi azăbar rămuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwăyi ne, ma'abũcin azabăr rămuwa.

Ayah  5:96  الأية
أُحِلَّ لَكُمْ صَيْدُ الْبَحْرِ وَطَعَامُهُ مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِلسَّيَّارَةِ ۖ وَحُرِّمَ عَلَيْكُمْ صَيْدُ الْبَرِّ مَا دُمْتُمْ حُرُمًا ۗ وَاتَّقُوا اللهَ الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Ohilla lakum saydu albahriwataAAamuhu mataAAan lakum walissayyaratiwahurrima AAalaykum saydu albarri ma dumtum hurumanwattaqoo Allaha allathee ilayhi tuhsharoon

Hausa
 
An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dőmin jin dăɗi a gare ku, kuma dőmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama măsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tăra ku.

Ayah  5:97  الأية
جَعَلَ اللهُ الْكَعْبَةَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ قِيَامًا لِّلنَّاسِ وَالشَّهْرَ الْحَرَامَ وَالْهَدْيَ وَالْقَلَائِدَ ۚ ذَٰلِكَ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَأَنَّ اللهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
JaAAala Allahu alkaAAbata albayta alharamaqiyaman linnasi washshahra alharamawalhadya walqala-ida thalikalitaAAlamoo anna Allaha yaAAlamu ma fee assamawatiwama fee al-ardi waanna Allaha bikullishay-in AAaleem

Hausa
 
Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yă sanya wată Mai alfarma da hadaya da rătayőyin Allah Yă san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kőme, Masani ne.

Ayah  5:98  الأية
اعْلَمُوا أَنَّ اللهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ وَأَنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
IAAlamoo anna Allaha shadeedu alAAiqabiwaanna Allaha ghafoorun raheem

Hausa
 
Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  5:99  الأية
مَّا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ ۗ وَاللهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا تَكْتُمُونَ
Ma AAala arrasooli illaalbalaghu wallahu yaAAlamu matubdoona wama taktumoon

Hausa
 
Băbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yană sanin abin da kuke bayyanăwa da abin da kuke ɓőyewa.

Ayah  5:100  الأية
قُل لَّا يَسْتَوِي الْخَبِيثُ وَالطَّيِّبُ وَلَوْ أَعْجَبَكَ كَثْرَةُ الْخَبِيثِ ۚ فَاتَّقُوا اللهَ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Qul la yastawee alkhabeethu wattayyibuwalaw aAAjabaka kathratu alkhabeethi fattaqoo Allahaya olee al-albabi laAAallakum tuflihoon

Hausa
 
Ka ce: "Mummuna da mai kyau bă su daidaita, kuma kő dă yawan mummuan yă bă ka sha'awa. Sabőda haka ku bi Allah da taƙawa, yă ma'abuta hankula ko la'alla ză ku ci nasara."

Ayah  5:101  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَسْأَلُوا عَنْ أَشْيَاءَ إِن تُبْدَ لَكُمْ تَسُؤْكُمْ وَإِن تَسْأَلُوا عَنْهَا حِينَ يُنَزَّلُ الْقُرْآنُ تُبْدَ لَكُمْ عَفَا اللهُ عَنْهَا ۗ وَاللهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanoola tas-aloo AAan ashyaa in tubda lakum tasu/kumwa-in tas-aloo AAanha heena yunazzalu alqur-anutubda lakum AAafa Allahu AAanha wallahughafoorun haleem

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓăta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lőkacin da ake saukar da Alƙur'ăni, ză a bayyana maku. Allah Yă yăfe laifi daga gare su, Allah Mai găfara ne, Mai haƙuri.

Ayah  5:102  الأية
قَدْ سَأَلَهَا قَوْمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ثُمَّ أَصْبَحُوا بِهَا كَافِرِينَ
Qad saalaha qawmun min qablikumthumma asbahoo biha kafireen

Hausa
 
Lalle ne wasu mutăne sun tambaye su daga gabăninku, sa'an nan kuma suka wăyi gari da su sană kăfirai.

Ayah  5:103  الأية
مَا جَعَلَ اللهُ مِن بَحِيرَةٍ وَلَا سَائِبَةٍ وَلَا وَصِيلَةٍ وَلَا حَامٍ ۙ وَلَٰكِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يَفْتَرُونَ عَلَى اللهِ الْكَذِبَ ۖ وَأَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ
Ma jaAAala Allahu min baheeratinwala sa-ibatin wala waseelatin walahamin walakinna allatheena kafarooyaftaroona AAala Allahi alkathibawaaktharuhum la yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka să'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hămi, amma waɗanda suka kăfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bă su hankalta.

Ayah  5:104  الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَىٰ مَا أَنزَلَ اللهُ وَإِلَى الرَّسُولِ قَالُوا حَسْبُنَا مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا ۚ أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ
Wa-itha qeela lahum taAAalawila ma anzala Allahu wa-ila arrasooliqaloo hasbuna ma wajadnaAAalayhi abaana awa law kana abaohumla yaAAlamoona shay-an wala yahtadoon

Hausa
 
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kő dă ubanninsu sun kasance bă su sanin kőme kuma bă su shiryuwa?

Ayah  5:105  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا عَلَيْكُمْ أَنفُسَكُمْ ۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا اهْتَدَيْتُمْ ۚ إِلَى اللهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooAAalaykum anfusakum la yadurrukum man dallaitha ihtadaytum ila Allahi marjiAAukumjameeAAan fayunabbi-okum bima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku lazimci răyukanku, wanda ya ɓace bă zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makőmarku take gabă ɗaya. Sa'an nan Ya bă ku lăbari ga abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah  5:106  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا شَهَادَةُ بَيْنِكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ حِينَ الْوَصِيَّةِ اثْنَانِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ أَوْ آخَرَانِ مِنْ غَيْرِكُمْ إِنْ أَنتُمْ ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَأَصَابَتْكُم مُّصِيبَةُ الْمَوْتِ ۚ تَحْبِسُونَهُمَا مِن بَعْدِ الصَّلَاةِ فَيُقْسِمَانِ بِاللهِ إِنِ ارْتَبْتُمْ لَا نَشْتَرِي بِهِ ثَمَنًا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ ۙ وَلَا نَكْتُمُ شَهَادَةَ اللهِ إِنَّا إِذًا لَّمِنَ الْآثِمِينَ
Ya ayyuha allatheena amanooshahadatu baynikum itha hadara ahadakumualmawtu heena alwasiyyati ithnani thawaAAadlin minkum aw akharani min ghayrikum in antum darabtumfee al-ardi faasabatkum museebatu almawti tahbisoonahumamin baAAdi assalati fayuqsimani billahiini irtabtum la nashtaree bihi thamanan walaw kana thaqurba wala naktumu shahadata Allahiinna ithan lamina al-athimeen

Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Shaidar tsakăninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lőkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ădalci daga gare ku, kő kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta săme ku. Kună tsare su daga băyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bă mu sayen kuɗi da shi, kő dă ya kasance ma'abucin zumunta kuma bă mu ɓőye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lőkacin, haƙĩƙa, mună daga măsu zunubi."

Ayah  5:107  الأية
فَإِنْ عُثِرَ عَلَىٰ أَنَّهُمَا اسْتَحَقَّا إِثْمًا فَآخَرَانِ يَقُومَانِ مَقَامَهُمَا مِنَ الَّذِينَ اسْتَحَقَّ عَلَيْهِمُ الْأَوْلَيَانِ فَيُقْسِمَانِ بِاللهِ لَشَهَادَتُنَا أَحَقُّ مِن شَهَادَتِهِمَا وَمَا اعْتَدَيْنَا إِنَّا إِذًا لَّمِنَ الظَّالِمِينَ
Fa-in AAuthira AAala annahumaistahaqqa ithman faakharani yaqoomanimaqamahuma mina allatheena istahaqqaAAalayhimu al-awlayani fayuqsimani billahilashahadatuna ahaqqu min shahadatihimawama iAAtadayna inna ithan lamina aththalimeen

Hausa
 
To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutăne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zălunci ba. Lalle mu, a lőkacin haƙĩƙa, mună daga azzălumai."

Ayah  5:108  الأية
ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يَأْتُوا بِالشَّهَادَةِ عَلَىٰ وَجْهِهَا أَوْ يَخَافُوا أَن تُرَدَّ أَيْمَانٌ بَعْدَ أَيْمَانِهِمْ ۗ وَاتَّقُوا اللهَ وَاسْمَعُوا ۗ وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Thalika adna an ya/too bishshahadatiAAala wajhiha aw yakhafoo an turadda aymanunbaAAda aymanihim wattaqoo Allaha wasmaAAoowallahu la yahdee alqawma alfasiqeen

Hausa
 
Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kő kuwa su yi tsőron a tũre rantsuwőyi a băyan rantsuwőyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bă Ya shiryar da mutăne făsiƙai.

Ayah  5:109  الأية
يَوْمَ يَجْمَعُ اللهُ الرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَا أُجِبْتُمْ ۖ قَالُوا لَا عِلْمَ لَنَا ۖ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Yawma yajmaAAu Allahu arrusulafayaqoolu matha ojibtum qaloo la AAilma lanainnaka anta AAallamu alghuyoob

Hausa
 
A ranar da Allah Yake tăra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (ză) su ce: "Băbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."

Ayah  5:110  الأية
إِذْ قَالَ اللهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ اذْكُرْ نِعْمَتِي عَلَيْكَ وَعَلَىٰ وَالِدَتِكَ إِذْ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ الْقُدُسِ تُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ وَكَهْلًا ۖ وَإِذْ عَلَّمْتُكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ وَالْإِنجِيلَ ۖ وَإِذْ تَخْلُقُ مِنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ بِإِذْنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيْرًا بِإِذْنِي ۖ وَتُبْرِئُ الْأَكْمَهَ وَالْأَبْرَصَ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ تُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ كَفَفْتُ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَنكَ إِذْ جِئْتَهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Ith qala Allahu yaAAeesa ibna maryama othkur niAAmatee AAalaykawaAAala walidatika ith ayyadtuka biroohialqudusi tukallimu annasa fee almahdi wakahlanwa-ith AAallamtuka alkitaba walhikmatawattawrata wal-injeela wa-ithtakhluqu mina atteeni kahay-ati attayribi-ithnee fatanfukhu feeha fatakoonu tayranbi-ithnee watubri-o al-akmaha wal-abrasabi-ithnee wa-ith tukhriju almawta bi-ithneewa-ith kafaftu banee isra-eela AAanka ithji/tahum bilbayyinati faqala allatheenakafaroo minhum in hatha illa sihrun mubeen

Hausa
 
A lőkacin da Allah Ya ce: "Yă Ĩsă ɗan Maryama!Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lőkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ˇudusi,kană yiwa mutăne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kană dattijo. Kuma a lőkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lőkacin da kake yin halitta daga lăkă kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kană warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lőkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lőkacin da Na kange Banĩ Isră'ĩla daga gare ka, a lőkacin da ka je musu da hujjőji bayyanannu, sai waɗanda suka kăfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bă kőme ba ne, făce sihiri bayyananne.'

Ayah  5:111  الأية
وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى الْحَوَارِيِّينَ أَنْ آمِنُوا بِي وَبِرَسُولِي قَالُوا آمَنَّا وَاشْهَدْ بِأَنَّنَا مُسْلِمُونَ
Wa-ith awhaytu ila alhawariyyeenaan aminoo bee wabirasoolee qaloo amannawashhad bi-annana muslimoon

Hausa
 
"Kuma a lőkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawăriyăwa cewa ku yi ĩmăni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmăni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, măsu sallamăwa ne."

Ayah  5:112  الأية
إِذْ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ هَلْ يَسْتَطِيعُ رَبُّكَ أَن يُنَزِّلَ عَلَيْنَا مَائِدَةً مِّنَ السَّمَاءِ ۖ قَالَ اتَّقُوا اللهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Ith qala alhawariyyoonaya AAeesa ibna maryama hal yastateeAAurabbuka an yunazzila AAalayna ma-idatan mina assama-iqala ittaqoo Allaha in kuntum mu/mineen

Hausa
 
A lőkacin da Hawarăyăwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yană iyăwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samă?" (Ĩsă) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."

Ayah  5:113  الأية
قَالُوا نُرِيدُ أَن نَّأْكُلَ مِنْهَا وَتَطْمَئِنَّ قُلُوبُنَا وَنَعْلَمَ أَن قَدْ صَدَقْتَنَا وَنَكُونَ عَلَيْهَا مِنَ الشَّاهِدِينَ
Qaloo nureedu an na/kula minhawatatma-inna quloobuna wanaAAlama an qad sadaqtanawanakoona AAalayha mina ashshahideen

Hausa
 
Suka ce: "Mună nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukătanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kă yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga măsu shaida a kansa."

Ayah  5:114  الأية
قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ اللهُمَّ رَبَّنَا أَنزِلْ عَلَيْنَا مَائِدَةً مِّنَ السَّمَاءِ تَكُونُ لَنَا عِيدًا لِّأَوَّلِنَا وَآخِرِنَا وَآيَةً مِّنكَ ۖ وَارْزُقْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Qala AAeesa ibnu maryama allahummarabbana anzil AAalayna ma-idatan mina assama-itakoonu lana AAeedan li-awwalina waakhirinawaayatan minka warzuqna waanta khayru arraziqeen

Hausa
 
Ĩsă ɗan Maryam ya ce: "Yă Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dőmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ăyă daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin măsu azurtawa."

Ayah  5:115  الأية
قَالَ اللهُ إِنِّي مُنَزِّلُهَا عَلَيْكُمْ ۖ فَمَن يَكْفُرْ بَعْدُ مِنكُمْ فَإِنِّي أُعَذِّبُهُ عَذَابًا لَّا أُعَذِّبُهُ أَحَدًا مِّنَ الْعَالَمِينَ
Qala Allahu innee munazziluhaAAalaykum faman yakfur baAAdu minkum fa-innee oAAaththibuhuAAathaban la oAAaththibuhu ahadanmina alAAalameen

Hausa
 
Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kăfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Ină azabta shi, da wata azăba wadda bă Ni azabta ta ga kőwa daga tălikai."

Ayah  5:116  الأية
وَإِذْ قَالَ اللهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيْنِ مِن دُونِ اللهِ ۖ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ ۚ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ ۚ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلَا أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ ۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Wa-ith qala Allahu yaAAeesa ibna maryama aanta qulta linnasiittakhithoonee waommiya ilahayni min dooni Allahiqala subhanaka ma yakoonu lee an aqoola malaysa lee bihaqqin in kuntu qultuhu faqad AAalimtahutaAAlamu ma fee nafsee wala aAAlamu ma feenafsika innaka anta AAallamu alghuyoob

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Allah Ya ce: "Yă Ĩsă ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutăne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautăwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsă) Ya ce: "Tsarkinka yă tabbata! Bă ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da băbu wani hakki a gare ni. Idan nă kasance nă faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kană sanin abin da ke a cikin raina, kuma bă ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."

Ayah  5:117  الأية
مَا قُلْتُ لَهُمْ إِلَّا مَا أَمَرْتَنِي بِهِ أَنِ اعْبُدُوا اللهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ ۚ وَكُنتُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا مَّا دُمْتُ فِيهِمْ ۖ فَلَمَّا تَوَفَّيْتَنِي كُنتَ أَنتَ الرَّقِيبَ عَلَيْهِمْ ۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ
Ma qultu lahum illa maamartanee bihi ani oAAbudoo Allaha rabbee warabbakumwakuntu AAalayhim shaheedan ma dumtu feehim falammatawaffaytanee kunta anta arraqeeba AAalayhim waanta AAalakulli shay-in shaheed

Hausa
 
"Ban faɗa musu ba făce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nă kasance mai shaida a kansu matuƙar nă dawwama a cikinsu, sa'an nan a lőkacin da Ka karɓi raina Kă kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kőme, Halartacce ne.

Ayah  5:118  الأية
إِن تُعَذِّبْهُمْ فَإِنَّهُمْ عِبَادُكَ ۖ وَإِن تَغْفِرْ لَهُمْ فَإِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
In tuAAaththibhum fa-innahum AAibadukawa-in taghfir lahum fa-innaka anta alAAazeezu alhakeem

Hausa
 
"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, băyinKa ne, kuma idan Ka găfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima."

Ayah  5:119  الأية
قَالَ اللهُ هَٰذَا يَوْمُ يَنفَعُ الصَّادِقِينَ صِدْقُهُمْ ۚ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ رَّضِيَ اللهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Qala Allahu hathayawmu yanfaAAu assadiqeena sidquhum lahumjannatun tajree min tahtiha al-anharukhalideena feeha abadan radiya AllahuAAanhum waradoo AAanhu thalika alfawzu alAAatheem

Hausa
 
Allah Ya ce: "Wannan ce rănar da măsu gaskiya, gaskiyarsu take amfăninsu. Sună da gidăjen Aljanna, ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, sună madawwama a cikinsu har abada. Allah Yă yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."

Ayah  5:120  الأية
لِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا فِيهِنَّ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Lillahi mulku assamawatiwal-ardi wama feehinna wahuwa AAalakulli shay-in qadeer

Hausa
 
Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kőme Mai ĩkon yi ne.
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us