1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللهِ ۗ
وَاللهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ
لَكَاذِبُونَ
Itha jaaka almunafiqoonaqaloo nashhadu innaka larasoolu Allahi wallahuyaAAlamu
innaka larasooluhu wallahu yashhadu innaalmunafiqeena lakathiboon
Hausa
Idan munãfukai suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah
ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã
shaida lalle munafukan haƙĩƙa , maƙaryata ne.
|
Ayah 63:2 الأية
اتَّخَذُوا أَيْمَانَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا عَن سَبِيلِ اللهِ ۚ إِنَّهُمْ سَاءَ
مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Ittakhathoo aymanahum junnatanfasaddoo AAan sabeeli Allahi innahum saa makanoo
yaAAmaloon
Hausa
Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ
abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
|
Ayah 63:3 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ آمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ
لَا يَفْقَهُونَ
Thalika bi-annahum amanoothumma kafaroo fatubiAAa AAala quloobihim fahum
layafqahoon
Hausa
Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe
a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta.
|
Ayah 63:4 الأية
وَإِذَا رَأَيْتَهُمْ تُعْجِبُكَ أَجْسَامُهُمْ ۖ وَإِن يَقُولُوا تَسْمَعْ
لِقَوْلِهِمْ ۖ كَأَنَّهُمْ خُشُبٌ مُّسَنَّدَةٌ ۖ يَحْسَبُونَ كُلَّ صَيْحَةٍ
عَلَيْهِمْ ۚ هُمُ الْعَدُوُّ فَاحْذَرْهُمْ ۚ قَاتَلَهُمُ اللهُ ۖ أَنَّىٰ
يُؤْفَكُونَ
Wa-itha raaytahum tuAAjibuka ajsamuhumwa-in yaqooloo tasmaAA liqawlihim
kaannahum khushubunmusannadatun yahsaboona kulla sayhatinAAalayhim humu
alAAaduwwu fahtharhum qatalahumuAllahu anna yu/fakoon
Hausa
Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa, zã ka
saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace
tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya
ake karkatar da su?
|
Ayah 63:5 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا يَسْتَغْفِرْ لَكُمْ رَسُولُ اللهِ لَوَّوْا
رُءُوسَهُمْ وَرَأَيْتَهُمْ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ
Wa-itha qeela lahum taAAalawyastaghfir lakum rasoolu Allahi lawwaw
ruoosahumwaraaytahum yasuddoona wahum mustakbiroon
Hausa
Kuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa
kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.
|
Ayah 63:6 الأية
سَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَسْتَغْفَرْتَ لَهُمْ أَمْ لَمْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ لَن
يَغْفِرَ اللهُ لَهُمْ ۚ إِنَّ اللهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Sawaon AAalayhim astaghfarta lahum amlam tastaghfir lahum lan yaghfira Allahu
lahum inna Allahala yahdee alqawma alfasiqeen
Hausa
Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai
gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.
|
Ayah 63:7 الأية
هُمُ الَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُوا عَلَىٰ مَنْ عِندَ رَسُولِ اللهِ
حَتَّىٰ يَنفَضُّوا ۗ وَلِلَّهِ خَزَائِنُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَٰكِنَّ
الْمُنَافِقِينَ لَا يَفْقَهُونَ
Humu allatheena yaqooloona latunfiqoo AAala man AAinda rasooli Allahi
hattayanfaddoo walillahi khaza-inu assamawatiwal-ardi walakinna almunafiqeena
layafqahoon
Hausa
Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su
wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã
su fahimta.
|
Ayah 63:8 الأية
يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعْنَا إِلَى الْمَدِينَةِ لَيُخْرِجَنَّ الْأَعَزُّ مِنْهَا
الْأَذَلَّ ۚ وَلِلَّهِ الْعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَلَٰكِنَّ
الْمُنَافِقِينَ لَا يَعْلَمُونَ
Yaqooloona la-in rajaAAna ilaalmadeenati layukhrijanna al-aAAazzu minha
al-athallawalillahi alAAizzatu walirasoolihi walilmu/mineena
walakinnaalmunafiqeena la yaAAlamoon
Hausa
Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da
mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa,
kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."
|
Ayah 63:9 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُلْهِكُمْ أَمْوَالُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُمْ
عَن ذِكْرِ اللهِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tulhikum amwalukum wala awladukumAAan thikri
Allahi waman yafAAal thalikafaola-ika humu alkhasiroon
Hausa
Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga
ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
|
Ayah 63:10 الأية
وَأَنفِقُوا مِن مَّا رَزَقْنَاكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ
فَيَقُولَ رَبِّ لَوْلَا أَخَّرْتَنِي إِلَىٰ أَجَلٍ قَرِيبٍ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُن
مِّنَ الصَّالِحِينَ
Waanfiqoo min ma razaqnakummin qabli an ya/tiya ahadakumu almawtu fayaqoola
rabbilawla akhkhartanee ila ajalin qareebin faassaddaqawaakun mina assaliheen
Hausa
Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku
har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali
makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?"
|
Ayah 63:11 الأية
وَلَن يُؤَخِّرَ اللهُ نَفْسًا إِذَا جَاءَ أَجَلُهَا ۚ وَاللهُ خَبِيرٌ بِمَا
تَعْمَلُونَ
Walan yu-akhkhira Allahu nafsan ithajaa ajaluha wallahu khabeerun bimataAAmaloon
Hausa
Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani
ne ga abin da suke aikatãwa.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|