1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ لَهُ الْمُلْكُ
وَلَهُ الْحَمْدُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Yusabbihu lillahi ma feeassamawati wama fee al-ardilahu almulku walahu alhamdu
wahuwa AAala kullishay-in qadeer
Hausa
Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah.
Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon
yi ne.
|
Ayah 64:2 الأية
هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ فَمِنكُمْ كَافِرٌ وَمِنكُم مُّؤْمِنٌ ۚ وَاللهُ بِمَا
تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Huwa allathee khalaqakum faminkum kafirunwaminkum mu/minun wallahu bima
taAAmaloonabaseer
Hausa
Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare
ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
|
Ayah 64:3 الأية
خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُمْ
ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ
Khalaqa assamawati wal-ardabilhaqqi wasawwarakum faahsana suwarakumwa-ilayhi
almaseer
Hausa
Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an
nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take.
|
Ayah 64:4 الأية
يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا
تُعْلِنُونَ ۚ وَاللهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
YaAAlamu ma fee assamawatiwal-ardi wayaAAlamu ma tusirroona wamatuAAlinoona
wallahu AAaleemun bithati assudoor
Hausa
Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke
bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin
ƙirãza.
|
Ayah 64:5 الأية
أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَبَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَبْلُ فَذَاقُوا وَبَالَ
أَمْرِهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Alam ya/tikum nabao allatheena kafaroomin qablu fathaqoo wabala amrihim walahum
AAathabunaleem
Hausa
Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka
ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?
|
Ayah 64:6 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُ كَانَت تَّأْتِيهِمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالُوا
أَبَشَرٌ يَهْدُونَنَا فَكَفَرُوا وَتَوَلَّوا ۚ وَّاسْتَغْنَى اللهُ ۚ وَاللهُ
غَنِيٌّ حَمِيدٌ
Thalika bi-annahu kanatta/teehim rusuluhum bilbayyinati faqalooabasharun
yahdoonana fakafaroo watawallaw wastaghnaAllahu wallahu ghaniyyun hameed
Hausa
Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji
bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka
kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah
wadãtacce ne, Gõdadde.
|
Ayah 64:7 الأية
زَعَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَن لَّن يُبْعَثُوا ۚ قُلْ بَلَىٰ وَرَبِّي
لَتُبْعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلْتُمْ ۚ وَذَٰلِكَ عَلَى اللهِ
يَسِيرٌ
ZaAAama allatheena kafaroo an lanyubAAathoo qul bala warabbee latubAAathunna
thummalatunabbaonna bima AAamiltum wathalika AAalaAllahi yaseer
Hausa
Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã
rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle
anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi
ne."
|
Ayah 64:8 الأية
فَآمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَالنُّورِ الَّذِي أَنزَلْنَا ۚ وَاللهُ بِمَا
تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Faaminoo billahiwarasoolihi wannoori allathee anzalna wallahubima taAAmaloona
khabeer
Hausa
Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma
Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne.
|
Ayah 64:9 الأية
يَوْمَ يَجْمَعُكُمْ لِيَوْمِ الْجَمْعِ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ التَّغَابُنِ ۗ وَمَن
يُؤْمِن بِاللهِ وَيَعْمَلْ صَالِحًا يُكَفِّرْ عَنْهُ سَيِّئَاتِهِ وَيُدْخِلْهُ
جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ ذَٰلِكَ
الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Yawma yajmaAAukum liyawmi aljamAAi thalikayawmu attaghabuni waman yu/min
billahiwayaAAmal salihan yukaffir AAanhu sayyi-atihiwayudkhilhu jannatin tajree
min tahtihaal-anharu khalideena feeha abadan thalikaalfawzu alAAatheem
Hausa
A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma
wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa
mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga
ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai
girma.
|
Ayah 64:10 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ
خَالِدِينَ فِيهَا ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Wallatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina ola-ika as-habuannari khalideena
feeha wabi/sa almaseer
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan
wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita.
|
Ayah 64:11 الأية
مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللهِ ۗ وَمَن يُؤْمِن بِاللهِ
يَهْدِ قَلْبَهُ ۚ وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Ma asaba min museebatinilla bi-ithni Allahi waman yu/min billahiyahdi qalbahu
wallahu bikulli shay-in AAaleem
Hausa
Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da
Allah,Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.
|
Ayah 64:12 الأية
وَأَطِيعُوا اللهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَإِنَّمَا
عَلَىٰ رَسُولِنَا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
WaateeAAoo Allaha waateeAAooarrasoola fa-in tawallaytum fa-innama AAalarasoolina
albalaghu almubeen
Hausa
Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya
bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu.
|
Ayah 64:13 الأية
اللهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ وَعَلَى اللهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Allahu la ilaha illahuwa waAAala Allahi falyatawakkali almu/minoon
Hausa
Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.
|
Ayah 64:14 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ مِنْ أَزْوَاجِكُمْ وَأَوْلَادِكُمْ عَدُوًّا
لَّكُمْ فَاحْذَرُوهُمْ ۚ وَإِن تَعْفُوا وَتَصْفَحُوا وَتَغْفِرُوا فَإِنَّ
اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooinna min azwajikum waawladikum AAaduwwan lakum
fahtharoohumwa-in taAAfoo watasfahoo wataghfiroo fa-inna Allahaghafoorun raheem
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi
a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma
kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 64:15 الأية
إِنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلَادُكُمْ فِتْنَةٌ ۚ وَاللهُ عِندَهُ أَجْرٌ
عَظِيمٌ
Innama amwalukum waawladukumfitnatun wallahu AAindahu ajrun AAatheem
Hausa
Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako
mai girma.
|
Ayah 64:16 الأية
فَاتَّقُوا اللهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ وَاسْمَعُوا وَأَطِيعُوا وَأَنفِقُوا خَيْرًا
لِّأَنفُسِكُمْ ۗ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Fattaqoo Allaha maistataAAtum wasmaAAoo waateeAAoo waanfiqookhayran li-anfusikum
waman yooqa shuhha nafsihi faola-ikahumu almuflihoon
Hausa
Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma
ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar
ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
|
Ayah 64:17 الأية
إِن تُقْرِضُوا اللهَ قَرْضًا حَسَنًا يُضَاعِفْهُ لَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۚ
وَاللهُ شَكُورٌ حَلِيمٌ
In tuqridoo Allaha qardanhasanan yudaAAifhu lakum wayaghfir lakum
wallahushakoorun haleem
Hausa
Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku
kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri.
|
Ayah 64:18 الأية
عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
AAalimu alghaybi washshahadatialAAazeezu alhakeem
Hausa
Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|