Muhawara Hausa
 



NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 03
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin Daga Dr. Mansur Sakkwato 

NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 03

Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi – 

Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi'a.

Cigaba ME YA RABA NI DA ADDININ SHI'A?

AUREN WUCIN GADI (Mut'ah)

Shi dai wannan aure duk da yake mun tashi mun tarar ana yin sa, ana kuma halasta shi, kai har ma ana sanya shi cikin aikin lada, da dai zuciyata ba ta natsu da shi ba. Tun kafin na san dalilan haramcinsa sau da yawa nakan ce da mutum a cikin tattaunawa ''kana son a yi da qanwarka''? Kafin ya ba ka amsa sai ka ga nan take ya fusata. Wato dai a aqidance mun yarda da shi amma a birnin zuciyarmu muna jin ba dadi!

Gaskiyar magana ita ce, an taba halasta wannan auren a wani dan quntataccen lokaci a zamanin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam bisa kamawar uzuri da lalura, daga bisani kuma aka shelanta haramcinsa har zuwa ranar alqiyama.

Wannan ya zo qarara a cikin ingantattun riwayoyi daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam. Abin ban mamaki ma shi ne yadda ruwayoyin Ahlulbaiti amincin Allah ya tabbata a gare su suka bayyana muni da haramcin wannan aure da zargin ma su yin sa. Amma idan ka bijiro da su ka ce, me ya sa ba mu aiki da wadannan riwayoyin sai ka ga malami ya turo ma ka hajar mujiya. Ba zai ce ma ka uffan ba. Ga kadan daga cikin irin wadannan riwayoyin:

v An karbo daga Abdullahi dan Sinan ya ce, na tambayi baban Abdullahi Alaihis Salam game da hukuncin auren Mut'ah, sai ya ce, ''kada ka qazanta kanka da shi''.

Ali dan Yaqdin ya tambayi Abul Hasan Alaihis Salam game da auren Mut'ah sai ya ce ma sa: ''me ya hada ka da shi? Allah ya raba ka da shi''.

v An karbo daga baban Abdullahi Alaihis Salam cewa, babu masu yin auren Mut'ah a wurinmu sai fajirai.

Ad-Dusi a cikin Al-Istibsar ya ruwaito daga Amru dan Khalid daga Zaid dan Ali daga iyayensa daga Ali dan Abu Dalib Radhiyallahu Anhu cewa, annabi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam ya haramta cin naman jakan gida da kuma auren Mut'ah.

Duk da ingancin wannan riwaya sharhin da Dusi ya yi ma ta kawai shi ne cewa, ''Dole ne mu dauki wannan riwaya a matsayin cewa, an fade ta ne bisa taqiyya (waskiya) domin ta dace da riwayar amawa (Ahlus-Sunna). To, ka ji fa! Ali dan Abu Dalib Radhiyallahu Anhu wai, ya yi ma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam qarya da sunan taqiyya!!

TUFKA DA WARWARA A CIKIN ADDININ SHI'A:

A lokacin quruciya mun saba da raya dararen Ashura da kuka da marin fuska da yanka jiki muna tuna kisan sayyidi Husaini Alaihis Salam amma da dai rana ba mu taba tsayawa mu yi tunanin hujjar yin haka a addini ba.

Shin wai Allah ne ya yi umurni da haka ko manzonSa? Ko kuwa dai lamarin son zuciya ne kawai?

Malamanmu ba za su taba bari hankalinmu ya je can ba. Ina! Dubi irin fatawar da Tibrizi ya bayar da aka tambaye shi mene ne hujjar makokin Husaini Alaihis Salam da ake yi?

Kuma ko imamai sun koyar da yin sa?

Ga amsar da ya bayar:

''A da can Imaman Shi'a sun rayu a zamanin da ake yin taqiyya, babu 'yancin bayyana ra'ayi saboda tsoro.

Saboda haka ba a hujja da lokacinsu don ba su samu dama ba, da sun rayu a irin zamaninmu da babu shakka za su yi wadannan makokai saboda alamomin addini ne kamar yadda muke yi, kamar kafa baqar tuta a qofofin gidaje da cibiyoyin addini don bayyana baqin ciki. Yin haka yana da kyau''.

To, ka ga a nan ba wata hujja sai son zuciya. Ba umurnin Allah ba ne ba na manzo ba, ba kuma wani Imami da ya ce ayi haka. Amma kuma ana kiran haka wai, raya addinin Allah ko alamomin addininsa.

Idan ka yi duba da kyau za ka samu riwayoyin imamai da tsofaffin malaman Shi'a sun ci karo da wannan sabon addini da 'yan Shi'a a duniya suke yi. Ga wasu 'yan misalai kadan:

v Ibnu Babawaihi Al-Qummi ya riwaito cewa, yana daga cikin kalaman annabi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam da ba wanda ya riga shi fadar su cewa, ''Kukan mutuwa na cikin al'amurran jahiliyya''.

Ad-Dabarsi ya riwaito daga Ali Alaihis Salam cewa, ''abubuwa guda uku na cikin lamurran jahiliyya wadanda mutane ba za su daina su ba har ranar tashin qiyama: neman ruwan sama ta hanyar duba taurari da sukar asali da dangantakar mutane da kuma kukan mutuwa''.

Ba wannan ce kadai ba, akwai wasu riwayoyin wadanda za mu kawo su a darasi na gaba da yardar Allah. A kasance tare da mu.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 02 @ 07:55:39 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin



"NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 03" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com