Topic: Ya kai Musulmi! In ban da tasirin gaskiya a cikin zuciya, da wane abu ne, masu gaskiya zasu cancanci tafiya tare da Nabi
Timeline: 2012-06-19 02:35:32
Daga Sheikh Salihu Bin Muhammad Alu Talib
Ya kai Musulmi! In ban da tasirin gaskiya a cikin zuciya, da wane abu ne, masu gaskiya zasu cancanci tafiya tare da Nabi
Masallacin Harami na Makka Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, godiya ga Allah bisa datar da mu ga abin da yake alheri da ni’imarSa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, girmamawa ga sha’aninSa. Kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa mai kira zuwa ga yardarSa, Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da ’yan uwansa da aminci mai yawa.
Bayan haka, hakika bin Allah da takawa shi ne mafi alherin abin da ake wasiyya da shi, shi ne mafi alherin sutura, kuma shi ne mafi girman dabi’a, “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma ku fadi magana madaidaiciya. Sai (Allah) Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma duk wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa, lallai ya rabauta da babban rabo mai girma.” (k: 33:71-72).
Allah Ya jikan mutumin da ya tsarkake harshensa, kuma ya takaita maganganunsa, ya lizimci tafarkin gaskiya a maganganunsa, bai saba da maganganun da za su kai shi ga halaka ba.
Ya ku Musulmi! Yau za mu yi magana ne a kan wata dabi’a wadda ita ce shugabar kyawawan dabi’u, ta tara dukkan falala kuma jagorar kyawawan dabi’u, Allah Ya yabi kanSa da ita a cikin LittafinSa sai Ya ce, “Kuma wane ne mafi gaskiya daga Allah ga labari?” (k: 4:87). Da fadinSa “Wane ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?” (k: 4:122), kuma Ya ce, “Ka ce Allah Ya yi gaskiya.” (k: 3:95).
Sannan Ya siffanta Manzanni da AnnabawanSa da zababbunSa da waliyanSa da dabi’ar gaskiya, sai Ya ce, “Kuma ka ambaci Isma’ila a cikin Littafi, lallai shi ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi.” (k: 19: 54). Sannan Ya ce ga dukkan bayinSa: “Ya ku wadanda suka imani! Ku bi Allah da takawa, kuma ku kasance tare da masu gaskiya.” (k:9 :119).
Ya ku Musulmi! Siffantuwa da gaskiya ba nafila ce ko ganin dama ba, a’a farilla ce a kan kowane Musulmi, kuma ita dabi’a ce ta mumini da ya wajaba ya zamo zahiri da badininsa sun zamo daidai wajen gaskiya da tsarkakuwa.
Sai dai duk da yalwar wannan siffa da haduwar dukkan halitta a kan nagartarta, a yau mun fi bukatar yi wa juna wasiyya kan lizimtarta, a daidai wannan lokaci da ake fama da wasu miyagun dabi’u da suke jawo raunin imani da ruguza tarbiyya da sanya tsananin son abin duniya.
Ya ku Muminai! Gaskiya dabi’a ce abar yabo a duniya da Lahira, kuma alama ce ta takawa, kuma sababi na kankare kananan laifuf*****a da daukaka daraja, wadannan duk sun zo a cikin fadin Allah Madaukaki: “Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata game da ita, wadancan su ne masu takawa. Suna da abin da suke so wurin Ubangijinsu. Wancan shi ne sakamakon masu kyautatawa. Domin Allah Ya kankare musu mafi munin abin da suka aikata, kuma Ya saka musu ijararsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa.” (k:39:33-35). Amma a ranar sakamako, saurari fadin Allah Madaukaki: “Wannan ce ranar da masu gaskiya gaskiyarsu take amfanarsu. Suna da gidajen Aljanna, koramu suna gudana daga karkashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan ne babban rabo mai girma.” (k:5:119).
Gaskiya falala ce, kuma daukaka ce, kuma gwadabe ne mai haske, sannan rai ne ma daraja. Ma’abucinta mai dacewa ne da kowane alheri har abada. Ya ku Musulmi! Ku yi nazarin wannan Hadisi, an karbo daga Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya kara masa yarda) daga Annabi (Sallallahu Alaihi wa alihi Wasallam), ya ce, “Lallai gaskiya tana shiryarwa zuwa ga da’a, kuma lallai ne da’a tana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma lallai mutum zai rika yin gaskiya har sai ya kasance mai yawan gaskiya. Kuma lallai karya tana shiryarwa zuwa ga fajirci, kuma lallai fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta, kuma lallai mutum zai rika karya har sai an rubuta shi a wurin Allah (cewa shi) mai yawan karya ne.”
Buhari da Muslim suka ruwaito shi. A wata ruwaya ta Muslim ya ce, “Mutum ba zai gushe ba yana gaskiya, yana riko da gaskiya , har sai an rubuta shi a wurin Allah cewa, shi mai yawan gaskiya ne. Kuma mutum ba zai gushe yana karya ba, yana riko da karya, face an rubuta shi a wurin Allah shi mai yawan karya ne!”
Lallai gaskiya tana shiryarwa zuwa ga kowane aikin da’a, jagora ce ga kowane alheri, tana rikon hannun wanda yake aiki da ita zuwa ga shiriya har sai ya shiga gidan Aljanna. Yaya haka ba zai faru ba, alhali shi mai gaskiyar furuci ne, mai gaskiyar hali mai riko ga gaskiya a cikin dukkan maganganu da ayyuka?! Lallai shi yana fadi tare da aikata gaskiya da riko da gaskiya yana lizimtarta, yana dabi’antuwa da ita, yana adonta kalmominsa da ita, yana guje wa kura-kurai da kauce wa karya, ransa bai son karkata ga karya ko ha’inci, har sai an rubuta shi a wurin Allah cewa shi mai yawan gaskiya ne. Wane matsayi Musulmi yake nema bayan wannan? Lallai shi abokin tafiyar Annabawa da shahidai ne. “To wadannan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni’ima a kansu, daga Annabawa da masu yawan gaskatawa da masu shahada da salihai. Kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya.” (k: 4:69).
Ya kai Musulmi! In ban da tasirin gaskiya a cikin zuciya, da wane abu ne, masu gaskiya za su cancanci tafiya tare da Annabawa?
Ka sake nazartar wannan Hadisi mai inganci: “An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda), daga Annabi (Sallallahu alaihi wa alihi Wasallam) ya ce: “Idan zamani ya kusato, mafarkin Musulmi ba zai yi kusa da karya ba, don haka mafiyanku gaskiyar mafarki mafiyanku ga gaskiya. Kuma mafarkin Musulmi yanki arba’in da shida ne na annabta.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Ka yi nazarin wannan Hadisi, mafarki na gaskiya yanki ne na annabta, zai zamo a zuciyar mai yawan gaskiya, wanda ya daukaka kuma ya tsarkaka, don haka sai ya haskaka da hasken Allah, a bude masa murafan gaibu Allah Ya sanar da shi abin da Ya so.
Ya ku Musulmi! Wanda ya lizimci gaskiya a lokacin yarintarsa, zai kasance ya fi lizimtarta a lokacin girmansa. Duk wanda ya riki gaskiya a game da hakkin da ke kansa, zai fi rike ta a kan hakkin Allah, wanda ya nemi bin gaskiya za a shiryar da shi zuwa gare ta, ransa ya ji dadi, badininsa ya tsarkaka, sannan zuciyarsa ta haskaka.
Ya bayin Allah! Bai halatta ba a rika sako-sako da batun tsare gaskiya, domin gaskiya ita ce ginshikin addininmu, ita ce alama da bajin abin koyinmu Annabi Muhammad (SAW), wanda a lokacin rayuwarsa ya kasance mafi bayar da cikakken misali ga dan Adam wajen riko da gaskiya a cikin magana da aiki da amana, haka a cikin mu’amala, inda ya bar gurbi matabbaci da bai kauce masa ba, koda da misalin takun tururuwa. Gaskiya ta kasance siffarsa da dabi’arsa, an san shi da ita hatta gabanin aiko shi, har aka yi masa lakabi da mai gaskiya abin gaskatawa (Sadikul Amin), ya shahara da haka, an san shi da haka a tsakanin mutane. Lokacin da aka umurce shi da kira da isar da sakon Allah, ya tara mutane ya tambaye su kan yadda suka dauke shi wajen gaskata maganganunsa, idan ya ba su labari, sai suka amsa masa da abin da suka sani a kansa, suna masu cewa: “Ba mu sanka da wani abu ba face gaskiya!”
**{Legacy activities, comments etc counter: 788; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}