Topic: Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (1)
Timeline: 2012-08-24 01:57:41
A Rubuce Da Malam Abdurrahman Ibrahim Idris
Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (1)
Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da aminici su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, yau za mu katse darasin da muke yi kan aikin Hajji, domin tavo wani abu kan azumin watan Ramadan. Kuma za mu kawo wata lacca ce mai taken: “Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma,” da Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi da Qungiyar Xalibai Musulmi ta jihar suka shirya a xakin taro na Babban Masallacin Bauchi a ranar Asabar da ta shige. Za mu fara da laccar Malam Abdurrahman Ibrahim Idris, sannan ta Malam Ahmad Tijjani Sa’id kamar yadda suka gabatar. Bismillah: Kalmar azumi a Larabci, Assaumu, na nufin Al-Imsak (kamewa). Al- Imsak a fannin tabiyya abu ne mai muhimmanci.Duk abubuwan da suke miyagu Allah Maxaukaki Ya yi hani a kai ne ta cewa, ku kame ga barin mummunan aiki, ku kame daga alfasha, ku kame ga barin mummunar magana. Don haka ita kanta kalmar Assaumu tana wakiltar wani abu a vangaren tarbiyya.
Sannan azumi a vangaren umarni, cewa a yi kaza, a yi kaza, nan ma yana da tasiri wajen tarbiyya. Allah (SWT) Ya ce: “Ya ku wanxada suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta a kan waxanda suke gabaninku, la’alla ku yi taqawa.” (Baqara).
Malaman tafsiri sun ce la’alla a nan ta tabbaci ce, wato tana nuna cewa in har za ku yi azumin nan kamar yadda aka wajabta muku, akwai tabbacin cewa za ku samu taqawa. Ita kuma taqawa tana nufin shamaki ko katanga wadda za ta hana aikata aikata miyagun ayyuka ko shiga wuta. Azumi yana da wannan tasiri, kamar yadda Allah Ya faxa, domin ana samun shamaki ko katangewa daga aikata miyagun abubuwa a cikin watan azumin Ramadan. Mutane kan nisanci ayyuka marasa kyau da yawa, hatta masu shan miyagun qwayoyi suna ta’addanci za a ga suna zaman lafiya.
Littattfan tafsiri sun nuna cewa azumin watan Ramadan yana koya haquri, domin yin azumi a zauna daga ketowar Alfijir zuwa faxuwar rana ba a ci ba a sha komai ba, tarbiyya ce ake koyar da mutum kan haquri. Saboda akwai yanayin da zai iya samun kansa a halin rashin abinci. Don haka ana nuna masa bai kamata ya je ya saci na wasu ko ya yi musu qwace ba, domin azumi ya koya masa haquri da babu.
Bai kamata mutum ya yi almundahana ya saci dukiyar al’umma ko ya yi fashi don ya ciyar da kansa qarfi da yaji ba.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan xayanku yana azumi kada ya tara da iyalinsa kada ya yi fasiqanci kada ya nuna jahilci, idan wani ya neme shi da faxa ya ce: “Ni ina azumi! Ni ina azumi!” Nan ma azumi na koyar da haquri, ana neman mutum da faxa yana cewa, yana azumi. Abubuwa uku da azumi ya hana ci da sha da jima’i, su ne tushen mafi yawan varnar da ake yi.
Idan ka ga mutum ya saci kuxi da biro ko ya valle gidan wani ya yi sata, ko ya tsare hanya da bind- iga ya yi fashi, yana son ya ci abinci ne. Ko yana son ya biya buqatarsa ta sha’awa ta kowace hanya, domin ko mace ba zai same ta ba ko sisi ba, sai da kuxi. Don haka kamewa abu ne mai kyau da qima a Musulunci, mutum ya zama mai tsantseni mai taka-tsantsan, kamar yadda azumi ke koyarwa. Zai yi kyau mu dage ko bayan azumi duk abin da ya biyo ta ofishinmu mu rubuta gaskiya, kada mu qara ko sisi don mu ci kuxin da ba namu ba. Haka kamar yadda muka koya a lokacin azumi, muna buqatar matanmu da rana amma muka kame, in muka samu kanmu a wurin da ba matan namu, ko a wurin da mutane ba su xauki zina abar qyama ba, to nan ma mu kame.
Sannan azumi na koyar da jarunta ta hanyar haquri da yunwa na tsawon yini, wannan zai sa idan Musulmi mace ko namiji suka samu kansu a fagen yaqi su iya jure wa yunwa. A zamanin Manzon Allah (SAW) an riqa samun mata jarumai a fagen yaqi da suke cewa, suna son su zama maqwabtansa a Aljanna. Kamar yadda Ummu Imarah ta yi qoqari a Yaqin Uhudu, har Annabi (SAW) ya ce da ita: “Tambaye ni abin da kike so ya Ummu Imarah!” Saboda yadda ya ga ta jajirce tana yaqi a kusa da shi a lokacin da wasu maza suka gudu. Sai ta ce: “Ni Aljanna nake so in kasance tare da kai Ya Rasulullah!” Sai ya ce: “Aljanna ta tabbata gare ki ya Ummu Imarah!” Don haka bai kamata qaramin ciwon gyambon ciki (olsa) ya hana Musulmi yin azumi ba, musamman irin ciwon da in mutum ya je banki zai iya yini bai ci abinci ba sai ya karvi kuxinsa.
Saboda qarfafa gwiwar Musulmi su zamo masu dauriya da jajircewa malamai da dama suna ganin bai kamata saboda haihuwa ko shayarwa mace ta qi yin azumi ba, in ba za ta iya ba ne kawai aka ce ta jinkirta zuwa wani lokaci. Amma abinci a ofis, abinci a gida abinci a mota ko’ina yawo da abinci, mutum ya zama bawan abinci ke nan. Alhali wata rana mutum yana iya samun kansa a yanayin da in ba ya da jarumta ba zai iya xauka ba.
Sannan azumi na koyar da adalci ko biyayya. Adalci ne kowa ya tsaya inda Allah Ya ce a tsaya, kuma adalci ne mutum ya tsaya inda shugaba ya ce. A tsaya bisa umarnin Allah da haninSa, in aka qetare an yi zalunci. Azumi kan sa mutum ya tsaya kan rayuwar da Allah Ya ce a tsaya a kai, zalunci ne wani ya qetare. Rashin bin wannan qa’ida ya sa kusan kowa ke rububin neman tara dukiya qarfi da yaji. Qalilan ne daga mutane suka yarda cewa ba kowa ne zai zama mai kuxi ba, kamar yadda Allah Ya tsara don rayuwa ta tafi daidai. Ko a wajen ciyar da iyali Allah Ya bambanta mai akwai da marar shi, inda Ya ce: “Domin mai yalwa, ya ciyar daga yalwarsa, wanda aka quntata masa arzikinsa ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya xora wa wata rai sai abin da Ya ba ta.” Ashe da sanin Allah, Ya ajiye mutane wasu da dukiya mai yawa wasu matsakaiciya wasu marasa ita.
Azumi yana koyar da tarbiyyar hana kallon abin da bai halatta ba.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya ku taron samari! Wanda yake da ikon aure daga cikinku ya yi aure. Domin ya fi runtse ido da tsare farji. Wanda ba ya da iko, ya yi azumi domin shi garkuwa ne gare shi.” Allah Ya umarci muminai maza da muminai mata su runtse idanuwansu kuma su katange al’aurarsu, sai ga shi Annabi (SAW) ya nuna aure na katange al’aura da runtse ido, sannan ya nuna azumi na katange duka biyun. Idan mutum ba ya azumi kowace mace tana iya burge shi, amma in yana azumi komai kyan mace sai ya ji ba ta burge shi, saboda yana cikin wani hali, wani lokaci in ana azumi magana ma ba a iya yi.
Sannan azumi na koya kyautatawa wajen ciyar da jama’a.
Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da ladar wanda ya yi azumin ba tare da an rage wa mai azumin lada ba.” Mutum na son a riqa tallafa masa, kuma al’umma zauna lafiya idan akwai wanda ya damu da ita, yake taimaka mata da kula da ita. Hakan yana maganin qyashi da jin haushin juna a tsakanin jama’a. Kowa ya yi qoqarin kyautata wa xan uwansa, ya tallafa masa da kowane abu na inganta rayuwa.
Azumi yana tarbiyyar Musulmi kan lizimtar gaskiya, saboda mutum yana iya shiga bayan gida ya sha ruwa ko ya ci abinci, ya fito ya ce yana azumi, amma bai yi haka ba, saboda tsoron Allah. Shi ya sa malamai ke cewa azumi sirri ne a tsakanin bawa da Ubangijinsa. To haka ake son Musulmi ya kasance a tsakaninsa da mutane wajen tsare haqqoqi da amanoninsu da suke hannunsa.
Wata tarbiyya da muke samu a lokacin azumin Ramadan shi ne yawaita karatun Alqur’ani da zikiri da sauransu. Watan Ramadan wata ne na Alqur’ani, a cikinsa aka saukar da shi daga Lauhul Mahfuz zuwa saman duniya, sannan aka riqa sassaukar da shi daki-daki. Ba watan da mutane suke jin Alqur’ani suke karanta shi kamar a cikinsa, kana barci a gida wani masallaci zai iso maka da shi, kana zaune rediyo na yi za ka ji, talabijin na yi ka ji, ka fita kasuwa ka ji, duk inda ka zaga za ka ji alaramma yana jan banqi mai fassara na yi.
**{Legacy activities, comments etc counter: 754; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}