*Legacy Post Number 9 from MediaHausa
Topic: Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa
Timeline: 2010-06-14 23:07:08
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa
A Rubuce Da Usman Musa Gabari
‘Yan uwana ‘yan Najeriya, godiyata a gare ku ba ta misaltuwa, saboda yadda kuka nuna damuwarku game da halin da rayuwata take ciki, musamman tun daga ranar 23 ga watan Nuwamba, 2009,
watau ranar da na tafi asibitin Sarki Abdul-Aziz da ke Jidda, Saudi Arabiya, don yin jinyar rashin lafiyar da na dade ina fama da ita.
Na sami labarin irin duk addu’o’in da kuka rika yi mini a kan Allah Ya ba ni lafiya, kuma na san da yawanku sun yi matukar farin ciki a yayin da suka ji muryata, a ranar 12 ga watan Janairu, 2010, a wata ‘yar takaitacciyar hira da na yi da sashen Hausa na rediyon BBC. A lokacin ina cikin radadin tsananin rashin lafiya, amma na daure na yi wannan hira don kwantar da hankulan jama’a. Ga yadda na sami labari, hirar ta yi amfani wurin rage damuwar da aka shiga saboda rashin sanin halin da lafiyata take ciki, kuma na sami labari ma har majalisun kasa sun yi amfani da ita a matsayin sakon da suka ce za su iya yin amfani da shi wurin nada mataimakina a matsayin mukaddashi. Kodayake an sami wasu da suke ganin cewa ba ni ne na yi wannan hira ba, amma dai tabbas ni ne.
Kun sake samun kanku cikin farin ciki, a wasu garuruwan ma (ciki har da jihata ta haihuwa,wato Katsina) har shagulgulan murna aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu. 2010, lokacin da labarin dawowata daga kasar Saudiyya ya bayyana. Duka dai kuna farin ciki ne saboda kyakkyawan fatan da kuke yi mani na samun lafiya, don in sami damar ci gaba da ayyukan da na faro, da kuma jagorancin kasarmu bisa turba ta gaskiya, ni ma na so hakan, sai dai babu abin da yake tabbata sai abin da Allah Ya so.
Na sami labarin duk irin abubuwan da suka dinga faruwa tun daga lokacin da na kwanta rashin lafiya, an yi ta shaci fadi iri daban-daban a kan kasa, da kuwa ni kaina da iyalaina. Wannan duk na dauke shi a matsayin wani tsari na Mahalicci, kuma hikimomin da Ya boye a cikin faruwar wannan, za su bayyana a yanzu ko kuma can gaba. A nan nake jinjina juriyar mai dakina abar kaunata, Hajiya Turai, wadda tafi daukar kaso mafi girma na irin wancan shaci-fadi da surutai, ba don komai ba, sai don irin yadda ta nuna jajircewa gurin kula da ni a wannan yanayi na tsananin rashin lafiya. Ni na amince kin yi biyayyar aure, kuma ladanki na wajen Allah, da fatan samun tsayin rai gurin ci gaba da kula da zuri’armu, cikawa da imani, har mu sake haduwa cikin rayuwar ni’ima maras karshe a gidan Aljannah.
A daren Labara 5 ga watan Mayu, 2010 na amsa kiran Allah Mahaliccina, kamar yadda lallai ne kowane rayayye sai ya amsa wannan kira. Na bar duniya ina cike da burin kyautata al’amuran kasar mu, da dora ta a kan ginshiki mai karfi don ta zama abar misali a duniya, gurin shiga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Tun ina duniya, kuma ina bisa karagar mulki, an yi ta korafi a kan kudurori bakwai na gwamnatina, da burin da na dauka na sanya Najeriya a cikin kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya. To, ni na san da gaske nake har ga Allah, kuma da na sami dama da an sha mamakin tabbatar wancan kuduri, da yadda Najeriya za ta bunkasa kafin shekara ta 2020, kamar yadda aka yi mamakin hanyar da na bi wurin warware matsalar Niger-Delta.
Na so gyara tsarin zabe don tabbatar da zabe na gaskiya, saboda haka ne ma na kafa kwamitin Uwais.
Da ni ne zan gudanar da zaben kasa a 2011, kuma a ce na tsaya takara, sai ya zamo ban ci ba to, da na kafa tarihi gurin karbar faduwa da mika mulki ga wanda ya ci zabe, in tattara komatsaina in koma Katsina, in ci gaba da kula da iyalina da yin noma da koyarwa, kamar yadda na kafa tarihi wajen bayyana kadarorin da na mallaka da kuma tabbatar da cewa zaben da ya kai ni ga mulki yana da tangarda.
Na so samar da wutar lantarki megawatt 6000 a karshen 2009, kamar yadda na ayyana! kuma da a ce ina duniya, lallai da na binciki dalilin rashin samuwar mega watt din da na ayyana. Na so in ga kammalar aikin yashe kogin Neja. Na so dawo da martabar Najeriya da ‘yan Najeriya, ta yadda za su bugi kirji su yi alfahari da kasancewarsu ‘yan Nijeriya a ko’ina suke a duniya.
Na gode bisa yabo da shaidu na alherin da ake ta bayarwa a kaina, musamman yadda aka yi zama na musamman a majalisar zartarwa ta kasa a ranar 12 ga Mayu 2010, don alhinin rashina. Ina fatan za a dora bisa ayyukan alherin da na fara don ladana ya tabbata.
Kamar yadda da nake jan ragamar to, su ma wadanda ke kai da wadanda za su biyo bayansu lallai ne za a wayi gari sun kauce, su ma taho inda nake! Saboda haka ina fatan gudanar da shugabanci na gari, tsoron Allah da tsantseni cikin sadaukar da kai da aiki tukuru don kasar mu ta kai ga ci. Cikin biyayya, ladabi da girmamawa nake addu’ar Allah Ya girmama ladan mahaifiyata bisa juriyar rashin ‘ya’yanta, haka su ma ‘yan uwa da makusanta na bisa juriyar da kuka nuna.
Ina fatan ci gaba da addu’o’inku na neman gafara a gare ni, kamar yadda nake neman afuwarku da yafewarku, bisa kura-kuran da na yi lokacin nake jan ragamar jagoranci ku.
Yanzu haka na kasance a kushewata, makabartar Wali dan Marina da ke birnin Katsina, da rahamar Allah, da kuma addu’o’inku za ta kasance wani ni’imtaccen dausayi daga cikin kasaitattun dausayoyin Aljannah.
Usman Musa Gabari 064916266, 08033510179
**{Legacy activities, comments etc counter: 14585; topic series: 5; forum: MediaHausa; legacy score: 5; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 5- /*}
Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi
Koma zuwa "Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi"
Tsalle zuwa
- Labarai da Ra'ayi
- ↳ Labaran Gida da na Ƙasa
- ↳ Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya
- ↳ Labaran Duniya da Tsakanin ƙasashe
- ↳ Sharrin Kiyayya ga Musulunci, Yaƙin Ta'addanci da Mugayen Sihiyonanci
- ↳ Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi
- Fatawa da Hukunce-hukunce
- ↳ Fatwa da Hukunce-hukuncen Shari'a
- ↳ Ramadan, Azumi, Idi da Sauransu
- ↳ Hajji, Umrah da Ziyarar Ƙasa Mai Tsarki
- ↳ Fiqhu Ibada Da Rukunan Ka'idojin
- ↳ Mu'amalar Fiqhu, Mu'amala da Kuɗi
- Tambayoyi da Amsoshi
- ↳ Tambayoyi da Amsoshi Alƙur'ani, Hadisi da Fiqhu
- ↳ Tambayoyi da Amsoshi Aqeedah, Manhaj da Adab (Da'a)
- ↳ Tambayoyi da Amsoshi Tarihin Rayuwa da Adabi
- ↳ Tambayoyi da Amsoshi na Kai, Iyalai da Al'ummomi
- ↳ Tambayoyi da Amsoshi na Gabaɗaya da Fasaha
- Qur'ani da Hadisi
- ↳ Alƙur'ani Mai Tsarki, Tafsirai da Fassarori
- ↳ Hadith Mai Girma, Sunnah da Hadisai
- ↳ Kimiyyar Alƙur'ani, Littattafai da Littattafai
- ↳ Kimiyyar Hadisi, Nassoshi da Rubuce-rubuce
- ↳ Karatun Alƙur'ani Mai Tsarki da Haddacewa
- Aqeedah da Manhaj
- ↳ Aqeedah (Koyarwa), At-Tawheed (Addinin Tauhidi) da Iman (Imani)
- ↳ Ash-Shirk (Mai Haɗa Allah), Bidi'a (Mai ƙirƙira daga Addini) da Gulu' (Mai Tsattsauran Ra'ayi)
- ↳ Sunnah ta Annabi (Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi)
- ↳ Annabi Muhammad, Manzon Karshe (Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi)
- ↳ Sahabban Annabi (Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi)
- Mata Da Iyalai
- ↳ Nikah (Aure) da Khitbah (Hulɗa)
- ↳ Talaq (Saki) da Khula' (Sakin Mata da Mata suka Fara)
- ↳ Ar-Rahim (Dangantakar Jini) da Walat (Tsarewa)
- ↳ Lamunin Mata, Mata Musulmai Masu Kyau da Lafiya
- ↳ Iyali, Mata da Yara (Na Halitta da Kuma Waɗanda aka Rene Su)
- Al'ummomi da Yan Unguwa
- ↳ Sabbin Musulmai da Kokarin Wayar da Kan Jama'a
- ↳ Masallatai da Cibiyoyin Musulunci a Gare Shi
- ↳ Al'ummomin Musulmi a Duniya a Gare Shi
- ↳ Sanarwa da Faɗakarwa ga Jama'a
- ↳ Kare Annabinka (Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi) a Gare Shi Duniya
- Roko da Buƙatun
- ↳ Buƙatun Koke-koke, Kira, da AAyyukan Agaji
- ↳ Buƙatun Sadaka na Masallatai, Ayyuka da Tallafi
- ↳ Buƙatun Sadaka na Makarantu, Ayyuka da Tallafi
- ↳ Kudaden Tallafi na Al'umma da Tallafi
- ↳ Buƙatun Addu'o'i na Kai, Ruqia da Ruhaniya
- Gabaɗaya da Fasaha
- ↳ Bayani na Gabaɗaya da Ilimi
- ↳ Ilimin Fasaha da Bayanai
- ↳ Harshen Larabci, Nahawu da Adabi
- ↳ Tarihin Musulunci, Tarihin Rayuwa da Labarun Musulunci
- ↳ Daban-daban, Aikin Gida na Makaranta, Lafiya da Sauransu