Topic: Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (8)
Timeline: 2012-08-24 02:14:04
A Rubuce Da Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (8)
Sakamakon gazawa irin ta dan Adam a makon jiya mun hautsina tambaya ta 25 da ta 26 a wuri daya, kuma hakan ya sa fatawar da aka bayar ba ta fito sosai ba. Lura da haka ne ya sa muka sake komawa baya daga tambaya ta 25 don fito da ma’anar fatawar:
Tambaya ta 25: Daga ina ake fara dawafi, kuma a kusurwoyin Ka’aba ina ne ake sumbanta, kuma ina ne ake shafa?
Amsa: Ana fara dawafi daga kusurwar da Hajarul Aswad yake (wato wurin da ake sumbata). Idan aka kewayo, daidai wurin da aka fara, to, an yi daya ke nan. Haka za a yi har sau bakwai. Kuma Hajarul Aswad shi ake sumbata a kowane zagaye idan an samu iko. Idan kuma ba a samu iko ba, to, sai a sanya hannu a ciki a dawo da shi baki a sumbance shi. Idan kuma ba a samu dama ba, sai a daga hannu daidai in da Hajarul
Aswad yake a nuna shi a ce: “Allahu Akbar,” sai a wuce, kamar yadda ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi dawafin dakin Ka’aba a kan rakumi, kuma duk lokacin da ya zo wurin rukuni, sai ya nuna shi da wani abu da yake wurinsa, sannan kuma ya yi kabbara.” Sahihul Bukhari: Kitabul Hajji, Babut Takbiri Indar Rukuni, Hadisi na 1613, da Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Jawazid dawafi Ala Ba’irin, Hadisi na 1272.
Sumbatar hannu shi ne ra’ayin Jamhurum Malami, sabani Imamuna Malik wanda yake ganin kawai dora hannu a baki za a yi, ba tare da sumbata ba. Don neman karin bayani sai a duba littafin Khalisul Juman Tahzib
Manasikul Hajji Min Adwa’ul Bayan: na Shaikh Sa’ud Shuraim (Limamin Masallacin Harami), Shafi na 186, Bugun Darul Wadan.
A wannan wuri, bai kamata a yi kokawa ko a cutar da wasu ba. Domin Annabi (SAW) ya fada wa Sayyadina Umar (RA) cewa: “Ya Umar kai mutum ne mai karfi, kada ka cutar da mutanen da ba su da karfi wajen sumbatar Hajarul Aswad. In ka samu dama ka yi, in ba ka samu ba, ka daga hannu ka wuce.” Hadisi ne Sahihi: Imam Shafi’i da Imam Ahmad sun ruwaito shi. Duba Nasburrayah: Juzu’i na 3, Hadisi na 17; da kuma Fathur Rabbani: Juzu’i na12, shafi na 34, Hadisi na 244.
Wurin da ake shafa kawai, shi ne Rukunul Yamani: ba a sumbatarsa, kuma idan an yi nisa da shi, ba za a daga masa hannu ba. Idan ban da wadannan wurare, babu wani wuri da ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa shi ya shafa ko ya yi umarni a shafa don neman tabarruki ko makamancin haka. Amma Multazim (wurin da yake tsakanin kofar Ka’abah da Hajarul Aswad), za a iya rungumarsa, a yi addu’a. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW), cewa ya rungume shi ne, ya yi addu’a. Kuma haka mafi yawan sahabbai, kamar Abdullahi Ibnu Abbas da Urwatu Ibnu Zubair (RA), suka aikata. Duba Sahih Sunan Ibnu Majah: Kitabul Manasik, Babul Multazimi, Hadisi
na 2962; da Silsilah Sahihah Mujalladi na 5 shafi na 213
Saboda haka duk wanda ya shafi wuraren da ba a umarce shi ba, kamar Makama Ibrahim, domin neman tabarruki, kamar yadda wasu ke yi, to, ya saba wa shari’a. Mahajjaci ya sani cewa ya tafi aikin Hajji domin neman yardar Allah ne, saboda haka ya kamata ya guji abin da zai bata aikin hajjinsa.
Tambaya ta 26: Shin ko akwai addu’ar da aka kebance mai dawafi ya yi?
Amsa: A gaskiya babu wata addu’a da ta tabbata daga bakin Manzon Allah (SAW) wanda aka kebance ga mai dawafi. Sai dai akwai wata addu’a da aka ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) yana yi a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad kamar haka: “Rabbana atina fid duniya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa kina azaban nar.” Ma’ana: “Ya Ubangiji Ka ba mu mai kyau a nan duniya, kuma a Lahira Ka ba mu mai kyau, kuma Ka tsare mu daga azabar wuta.” (Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babud Du’a’i Fid dawafi, Hadisi na 1892. Kuma Sheikh Albani ya hassana shi, Koda yake wadansu almajiransa sun raunana shi, sai dai maganarsa ta cewa Hadisin hasan ne ta fi rinjaye).
Wannan ita ce addu’ar da Manzon Allah (SAW) yake yi a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad. Amma sai ga shi an buga littattafai da dama dangane da addu’o’in da ake cewa wai na dawafi ne, ana sayar wa mutane. Sai ka ga an ce ga addu’ar zagayen farko, ga kuma addu’ar zagaye na biyu har a gama dawafin. Irin wadannan littattafai su ne ke kara sa jama’a su kasa fahimtar yadda Manzon Allah (SAW) ya aikata wannan aiki. Wadannan addu’o’i, a matsayin wai addu’o’i ne na dawafi, ba su da wani asali daga cikin Littafin Allah ko kuma koyarwar Manzon Allah (SAW).
Ya ’yan uwa masoya Manzon Allah (SAW)! Wajibi ne a guji aukawa cikin kagaggun al’amura, domin kada a yi aikin baban giwa. Saboda haka, ya kamata a nisanci irin wadannan littattafan, sannan a daure a tambayi malamai irin yadda Manzon Allah (SAW) ya yi. Hakika yin hakan shi ne tsira, kuma shi ne cikakkiyar soyayya da mika wuya ga Sunnar Manzon Allah (SAW).
Don haka, ya kamata maniyyaci ya san abin da ya kai shi aikin Hajji, kuma me yake bukata a wurin Allah. Ya roke Shi da fatar ya samu biyan bukatarsa.
Muhimmin abu ga mahajjaci shi ne ya san cewa ya je aikin Hajji ne don neman yardar Allah, kuma don neman gafarar zunuban da ya aikata. Saboda haka, sai ya duba kyawawan addu’o’in da suka tabbata daga ingantattun Hadisan Manzon Allah (SAW).
Haka kuma, bukatun da ake da su na duniya da Lahira, a tabbata sun dace da koyarwar Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW). Amma idan ba a jin Larabci, wato ba za a iya yin addu’a da Larabci ba, to, sai a roki Ubangiji (SWT) bukatun alheri da suke cikin ran Alhaji ko Hajiya da harshen da za su iya fahimtar abin da suke roko. Don kada su je suna yin addu’a da Larabci, ba tare da sun san abin da suke fada ba.
Haka kuma a rika kokarin yin i’itirafi da zunubai, ana yawaita tuba ga Ubangiji (SWT), wato istigfari. Sannan kada a manta da iyaye da ’yan uwa da suka rasu, a rika tunawa da su, ana yi musu addu’a, tare da rokon kyakykyawan karshe ga mai aikin Hajji da iyaye da ’yan uwa da zuriyarsa da ke raye.
Tambaya ta 27: Idan mutum ya yi kokwanton adadin dawafinsa, yaya zai yi?
Amsa: Idan mutum yana kokwanton dawafinsa ya cika ko bai cika ba, sai ya gina shi a kan yakini. Misali kamar idan yana kokwanton hudu ne ko biyar ne, to, sai ya mayar da shi hudu, don shi ne yakini. Idan kuma yana ganin ya yi kari ne, sai ya bar shi haka, ya yi Sallah. Wannan ita ce fatawar Imam Malik. A duba Al-Istizkar, Mujalladi na 12 shafi na 170, mas’ala ta 17201
**{Legacy activities, comments etc counter: 2623; topic series: 2; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 2- /*}