Topic: Martani ga masu adawa da auren Sanata Yarima
Timeline: 2010-06-14 22:50:22
Martani ga masu adawa da auren Sanata Yarima
A Rubuce Da Yasir Ramadan Gwale
Ya dan uwa mai karatu ina mai yi maka fatan alkhairi da fatan kana lafiya.
Yau kam zan yi magana ne a kan wani batu da ya dauki hankalin kusan galibin kafafen yada labarai na gida da na kasashen waje a`yan kwanakin da suka gabata wato auren Sanata Yarima da wata yarinya ‘yar asalin kasar Masar. Gaskiya abin ya ba ni mamaki kwarai da gaske yadda na ji wasu wadanda Turawan yammacin duniya suka wanke musu kwakwale suke ta kwaroroto da Sanata Yarima.
Shi dai aure a shari’ar musulunci yana halatta ne a yayin da waliyyan yarinya da wakilan yaro suka amince su daura wa ‘ya`yansu aure a gaban shaidu. Ko da mutum uku ne wannan aure ya kullu. Dalilin da shariah ta halatta aure shi ne domin a kare maza da mata daga afkawa makarantar shaidan wato ka zakkewa matar da ba halalinka ba ce. aure shi ne yake hallata maka mace ko ya harantamaka ita. shi aure idan a ka yi shi ma’ana da yardar iyaye da kuma waliyai ya yi koda kuwa shekarun ma’auratan nawane.
Dangane da yamadidi da ake ta yi da Sanata Yarima, shi dai musulmi ne kuma ya yi imani musulunci shi ne addininsa kuma wannan addini da ya yi imani da shi bai haramta masa wannan aure ba to ban ga wani dalili da wasu mutane wadanda Turawan yammacin duniya suka wanke wa kwakwalensu za su yi kokarin kawo cikas ga wannan aure ba.
Duk maganar da suke yi shi ne wai akwai wata doka da ta baiwa yara ‘yanci wadda ake kira da suna Child Right Act, wadda ita wannan doka jihar da Sanata Yarima ya fito ba ta sanya mata hannu ba, wato da ita da zancen banza duk daya. Kuma wai shin Baturen da idan uwarsa ta tsufa zai kai ta gidan tsofaffi wai shi ta dame shi, shi ne zai kawo mana wata doka da ta shafi kananan yara mu yarda dashi? Tun farko su fara kulawa da iyayen yaran tukuna sannan su yi magana a kan yara.
Kuma ta inda za ka san wadannan mutane kururuwar iblis suke yi yara nawa wadanda ake kira under age suke yin karuwanci a Najeriya ba’a taba cewa yau ga doka da ta hana karuwanci ba, Sai aure da aka yi shi bisa shari`a da yardar iyaye da shaidu?
A yayin da yake zantawa da gidan rediyan BBC a makon da ya gabata Ustaz Zakariyya ya ce bisa sharia`r Islama babu haranci a wannan aure na Sanata Yarima matukar da amincewar yarinyar aka yi shi. Sannan kungiyoyi mata sun yi zanga-zanga a majalisa domin kalubalantar sanata Yarima wadanda suka hada da kungiyar likitoci mata ta Najeriya wato Medical Women Association of Nigeria, da kuma kungiyar kare mata a mataki na wayewa wato Women Right Adbancement and Protection Alternetibe (WRAPA) da kuma kungiyar lauyoyi mata ta Duniya wato (GAFA) wanda suka je majalisa karkashin jagorancin Mrs Chinelo Irele wadda ita ce shugabar kungiyar GAFA majalisa ta sace musu gwiwa inda ta nuna babu ruwanta da al’amarin da ya shafi auren Sanata Yarima don haka su tafi kotu su shigar da kara ruwan kotu ne ta kama Yarima da laifi ko ta ce ba shi da laifi. Wannan abin da majalisa ta yi wa wadannan mata ya yi daidai, sai dai kungiyoyin matan sun sami amincewar wasu sanatoci mata wadanda kiristoci ne, Sanatocin sun hada da Sanata Chris Anyanwu da Patricia Akwashiki da Emem Ekaette da Nkechi Nworgu. Tunda yake Yarima bai saba wa musulunci ba, babu wani mahaluki a kasar nan da zai ce wannan aure ba iyi ba, ballantana wasu da suka kasa zaman aure za su sanya baki acikin wannan batu .
Kodayake Duk wadannan kungiyoyi da ke da tushe daga kasar Amurka da Yammacin Turai, kuma wadannan kasashe da kuma kungiyoyi suna adawa da sake jaddada sharia`r Islama da sanata Yarima ya yi a lokacin da yake gwamna wannan babu abin da zai kara a taskar Yarima sai soyuwa a zukatan ‘yan Najeriya musulmi, Muna goya wa bayan sanata Yarima tun da dai wannan aure bai saba wa Addini musulunci ba.
Kuma duk wata kururuwa da wani musulmi ko wanda ba musulmi ba, za su yi a kan wannan aure, na sanata ba za su iya kawo cikas gare shi ba . Kuma wai a cewarsu idan aka kai Sanata Yarima kotu tana iya daure shi Shekara biyar ko tara ta Naira 500, 000. Ko kuma duka biyun amma kuma ban ji an ce auren ya warware ba to ashe kenan burin shi ne a kunyata shi , ba domin komai ba sai domin shi musulmi ne, wanda bai kunyata ba kuma babu wanda ya isa ya kunyata shi.
Kuma ai kwana- kwanannan mu ka ji ana zargin wasu limaman Addinin kirista da yin lalata da kananan yara a kasar Amurka me wadannan kungiyoyi suka yi akan wannan batu ko kuwa tsabar rainin hankaline ga musulmi. Ko kuwa wata dama ake son yin amfani da ita domin harzuka musulmin kasar nan a fake da wannan a ce an zo yakar ta’addanci ko kuma yakar masu tsaurin akida. Duk irin makirci da kulle- kullen da Amurka da kasashen Turai suke shirya wa musulmin kasar nan don a harzukamu to su sani a ankare muke kuma musulmai ba wawaye ba ne kuma ba jahilai ba ne.
An yi batun Boko Haram ba mu fusata ba, An yi na Jos, kusan kasha goma musulmi ba su fusata ba kuma aka kashe Malami a masallaci dab da lokacin zabe ba mu fusata ba, a ka yi ‘yan Panshekara wannan ma bai harzukamu ba, sannan ga batun Umar Faruk Mutallab wannan ma bai fusata musulmin Arewacin Najeriya ba don haka, ku ci gaba da makirci mu kuma Allah Shi Zai ba mu ilhamar gane makircinku. Allah Ya yi mana jagora Amin.
Yasir Ramadan Gwale
Shugaban kungiyar Muryar Talakawan Najeriya Reshen Jihar Kano
07028690570
**{Legacy activities, comments etc counter: 1267; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 4- /*}