Topic: Kalubalen Da Ke Gaban ’Yan Najeriya
Timeline: 2010-06-14 22:55:47
Kalubalen Da Ke Gaban ’Yan Najeriya
A Rubuce Da Abdulkarim Dayyabu
Yanzu dai siyasa da tattalin arziki da tsaro a Najeriya suna hannun barayin shugabanni ne da ’ya’yansu.
Canja wannan al’amari ya danganta ga hada kan talakawa su yi musu tawaye su kawar da su da kuri’arsu su tsaya sai abin da aka zaba aka ba su, ko da zai kai ga zanga-zangar kwana da kwanaki kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya. Idan ba mu yi haka ba, ba za mu iya fatattakar azzaluman da suke sace mana kuri’a daga baya su sace mana dukiyar kasa su je su zubar a kasashen waje ba. Kada mu yarda a maimaita abubuwan da aka yi mana a baya a zabe na gaba.
Idan muka yi haka za mu bayar da damar da za a kwato dukiyar kasa da aka sace, domin a samu a farfado da wutar lantarki; a samar da ruwan sha mai tsabta; a samar da tsaro; a farfafdo da masana’antu; a inganta kiwon lafiya da ilimi, mu koma cikin hayyacinmu.
Mu talakawa ya kamata mu fito mu tsaya cewa sai an kwato duk dukiyar da barayin shugabanni suka sace mana kafin a yi zaben shekara ta 2011. Dukkan barayin ba sa ko fitar da zakka balle a yi maganar haraji ga kasa. Tunda yake bas u ne suka hallice mu ba, tilas mu fito mu nuna musu karshensu ta hanyar tilasta a kwato abin da suka sata, idan kuma muka ki yin haka za mu ci gaba da zama bayinsu, ’ya’yanmu su zama bayin ’ya’yansu, jikokinmu jikokin bayinsu har abada! Kada mu yarda fajirai da matsafa su ci gaba da mulkarmu. Ko haka shi ne dimokuradiyyar? Bayan mun je Amurka mun gano ba haka suke yi ba, saboda haka a za mu yarda ba, tilas mu fito mu ja daga da su, kamar yadda magabatanmu suka yi har sai da suka kori Turawan mulkin mallaka daga mulki, suka kakkabe hannuwan sarakuna daga mulki. ’Ya’yan talakawa suke zama gwamnoni da shugabannin kasa.
Duk wanda ya tabbata maciyin amana, mai saba alkawari, mai karya, muna*****i shi suke so a siyasa, idan ba irinsu ba ne ba za su yarda da mutum ba. Har yaushe za mu yi ta zuba ido irin wadannan mutane suna ci gaba da mulkarmu ko suna zaba mana wadanda za su mulke mu don su ci gaba da sace mana dukiyar kasa suna mayar da sanya tsoronsu a zukatan jama’a. Tilas ne mu sanya Allah a gaba don a sami shugaban da zai magance irin wadannan miyagun shugabanni, idan muna son a sami zaman lafiya da ci gaba a kasar nan.
Malaman jami’a da na addini suna tara ilimi kamar Alhuda-huda, amma ba sa aiki da shi a wajen mu’amala a tsakaninsu da jama’a ko amanar da aka damka a hannunsu. Yayin da a gefe guda kuma ’yan boko suke cewa sai wanda yake da shaidar karatun sakandare ko fiye za a ba damar shiga zabe ba tare da la’akari da gogewa da amana da adalci ba, balle jam’iyya ko zabe ko wata dimokuradiyya.
Duk wadannan abubuwa suna faruwa ne a lokacin da gwamnati ta gaza sauke nauyin da ke kanta na tsare rayuka da dukiya da mutunci da addinin jama’a. Kuma duk gwamnatin da ba za ta iya tsare rayuka da dukiya da mutunci da addinin jama’arta ba, gara babu ita kowa ya kare kansa da kansa, ko wadanda suka amince wa juna su hadu su kare kansu.
Muna kalubalantar ’yan Majalisar Dokoki ta kasa kan yadda suka mallaki kazaman kudi da kadarori na miliyoyin Naira ba tare da sun kasance ’yan kasuwa ko masu wata sana’a ba. Muna zargin cewa wadannan kudade an same su ne ta hanyar kashe- mu-raba. Idan hukumomin da aka dora wa alhakin bin diddigin abin da kowane jami’in gwamnati ya mallaka da yadda ya yi ya same su don kwato wa talakawa kayansu ba su kwato ba, to mu a Rundunar Adalci ta Najeriya muna kira ga masu hakki su zo mu hadu mu nemo hanyoyin kwato hakkokinmu.
Muhimman abubuwan da muka sa a gaba sun hada da bin diddigin duk abin da kowane mai mulki da iyalansa da abokan harkokinsa suka mallaka gida da wajen Najeriya, tun daga lokacin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ciwo bashin IMF, ya kaddamar da shirin kowa ya ji a jikinsa-SAP, da kuma daga 1999 zuwa yanzu. Duk wanda yake da kowace irin gudunmawa da zai bayar muna maraba da shi.
Abdulkarim Dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
Lamba 11 Beirut Road,
Kano.
08023106666, 08060116666
Imel: jdaiyabu@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 864; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 4- /*}