Topic: An sami tuntube wajen tabbatar da ginshikin dimokuradiyya - Dokta Salihi
Timeline: 2010-06-14 22:58:48
An sami tuntube wajen tabbatar da ginshikin dimokuradiyya - Dokta Salihi
A Rubuce Da Ubale Garba dambatta, a Kano
Shi kuwa Shugaban Sashin Kimiyyar Siyasa na Jam’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Haruna Salihi wanda masani ne a harkokin siyasar duniya na kasa da kasa cewa ya yi,
babban abin da za a iya cewa an samu na wata riba a wannan mulki na dimokuradiyya shi ne na yadda ya iya juya duk wata rikita-rikita da ta taso ta kuma ya dore. Ya ce akwai abubuwa da dama na tuntube da za a iya cewa an samu, musamman rashin gudanar ingantaccen zabe. Ya ce tun lokacin da aka gudanar da zaben 1999 ba sake gudanar da wani zabe da za a iya cewa mai inganci ne ba, kuma lokacin da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya kusa kammala wa’adin mulkinsa ya yi kokarin yin tazarce, duk wadannan abubuwa ne na tuntube.
Farfesa Salihi ya ce “Babban abin sha’awa shi ne na kwanan nan da marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya rasu, sai ga shi an canja tafiyar mulki ba tare da wata matsala ba, duk wadannan abubuwa ne na ban sha’awa a tafiyar, wannan ni ina gani wata alama ce da za a iya cewa mulkin nan ya dauki hanyar zama da gindinsa.”
Ya ce, amma har yanzu akwai matsala kan babban ginshikin mulkin dimokauradiyya na ba ’yan kasa ’yancin walwala da zaba ko sauya gwamnati sduk lokacin da suke so. “Abin takaici shi ne tun lokcin da mulkin dimokuradiyya ya dawo cin hanci da rashawa ya karu maimakon kyautata rayuwar ’yan kasa. Amma ga harkokin jami’yyun siyasa da kungiyoyi da majalisu da kuma ba kafafen watsa labarai ’yanci duk wadannan akwai riba, amma ba batun kyautata rayuwar al’umma ba, hasali ma sai kara jefa su cikin talauci da tsarin ya yi duk da irin dimbin arzik da Allah Ya hore wa kasar nan a wannan lokaci.”
Farfesa Salihi ya ce, babban abin da ke kawp barazana ga mulkin dimokuradiyya shi ne rasa ginshikin ita dimokuradiyyar na ba ’yan kasa ’yancin zabar abin da suke so kuma su canja gwamnati duk lokacin da suke so.
Ya ce yadda ake gudanar da zabe da yadda ’yan siyasa suka dauki kansu, wani lokaci har da mu talakawa kan dole sai na yi wani abu da kuma nadi maimakon zabe, duk abubuwa ne da suke iya kawo barazana ga tsarin.
Sauran matsalolin sun hada da yadda jam’iyyun siyasa da gwamnati suke gudun duk abubuwan da ya kamata su yi na gyara idan ana bukatar tsarin ya dore. Ya ce duk da yake babu tabbataccen nazari amma abin da aka gano dangane da basirar ’yan Najeriya game da harkokin siyasa cikin kowane mutum goma kimanin mutum shida suna da wayewa ta siyasa, amma talauci ya sa kusan ya samu tarnakin gudanar da ’yancinsa na zaba ko sauya gwamnati kamar yadda tsarin ya shimfida masa.
Farfesa Haruna Salihi ya ce yawan jam’iyyu a tsarin dimokuradiyya baa bin tsoro ko damuwa ba ne, domin abin da tsarin dimokuradiyya ya shimfida shi ne jam’iyya tuta ce da ke wakiltar ra’ayi ko akidar al’umma, kuma da zarar aka ce za a kayyade su kamar an dauki hanyar sare ’yancin mutane ne.
“Idan aka duba ko kasashen da suka ci gaba a siyasa irin su Amurka da Birtaniya za a ga ba sa rage yawan jam’iyyunsu sai dai su jam’iyyun idan sun girma su nemi hadewa wuri guda da wadanda suke ganin suna da ra’ayi ko akida iri daya. Sannan yanzu ana ta samun wasu jam’iyyun na ta kunno kai a Nahiyar Turai kamar Green Party da sauransu.”
Ya ce a nahiyaramu ta Afrika idan aka ce za a rage jam’iyyu shugabanni za su hade su da karfen tsiya, kamar yadda ya faru a kasar Zimbabwe. “Abin da za a yi shi ne hukumar zabe ta bullo da wasu hanyoyi na sa ido kan yadda jam’iyyun siyasa suke gudanar da ayyuka, musamman wajen ba su kason kudaden da gwannati takan ware musu ya kasance kodai a yi amfani da irin yawan kujerun da suke da su a majalisu ko kuma yawan offisoshi a kasa.
Dokta Baffa Aliyu Umar ya bayyana cewa akwai sauran tafiya game da ci gaban rayuwar al’umma idan aka kwatanta nasarar da aka samu a cikin shekara 11, da dawowar mulkin dimokuradiyya.
Doktan wanda masanin halayyar dan Adam ne ya ce “dawowar siyasa ya haifar da samun karin kudin shiga, amma kayan kyautata jin dadin rayuwa sun yi wa al’umma karanci. Kuma kasar ta daina tafiya kan turbar da shugabannin al’umma da suka ja ragamarta a bayan samun ’yancin kai.”
Dokta Baffa ya ce wadannan shugabanni da suka hada da Malam Aminu Kano da Dokta Nnamdi Azikiwe da Ahamdu Bello Sardauna da Abubakar Tafawa balewa da Cif Obafemi Awolowo, sun dora kasar nan a kan turbar ci gaba, kafin shugabannin da suka biyo baya su dakile ta.
Malamin wanda ke koyarwa a fannin nazarin kimiyyar halayyar dan Adam a Jami’ar Bayero, Kano ya nuna rashin jin dadi kan yadda cin hanci da rasahawa suka yi wa kasar nan katutu, suka kuma dakile ci gabanta a tsawon shekara 11 da dawowar mulkin dimokuradiyyar. Haka kuma a siyasance, ya ce har yanzu ana rigima kan wa ya kamata ya mulki kasa, kuma daga wane bangare zai fito, a maimakon a dubi cancanta da kyawawan halayensa.
Ya ce Jamhuriyya ta Uku daga 1998 zuwa yanzu ta haifar da nasarorin dawowar mulkin siyasa da kuma karin samun kudin shiga na fetur da kuma karin talauci da satar kudin gwamnati daga masu mulki.
Doktan ya ce yawan tashe-tashen hankula da rigingimu tsakanin kabilu da mabiya addinai yana da nasaba da wasu matsaloli na rashin adalci da rashin gaskiya da talauci da siyasa da sauransu da gwamnati ta kasa warwarewa.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1096; topic series: 1; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 1- /*}