Topic: Shugaban kasa a karkashin kasa
Timeline: 2010-06-14 23:01:45
Shugaban kasa a karkashin kasa
A Rubuce Da Muhammad Sulaiman Abdullahi
Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma. Allah Mai girma, lallai Allah Ya cika Sarkin Sarauta, Mai mulkin da ba wanda ya isa ya koya maSa yadda Zai yi, kuma ba wanda ya isa ya hana Shi yin abin da Ya ga dama a lokacin da Ya ga dama ga wanda Ya ga dama, ko da kuwa ba a so.
Allahu Akbar, a ranar Laraba ne wato 5 ga Mayu, wannan watan da muke ciki, na shekarar 2010, Allah Ya yi wa mutum na farko a tsarin mulkin Najeriya rasuwa, wato Alhaji Umaru Musa ‘Yar’aduwa. Addu’ar da za mu yi masa a nan ita ce, Ya Allah Ka jikansa Ka yi masa rahama, kurakuransa muna fata Allah Ka yafe masa. Wata mata ta ce “ni dai ko me ya yi min na yafe masa” Wannan magana da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun fadi haka. Allah Ka bai wa iyalansa hakurin rashinsa, Allah Ka sa can ya fi nan. Allah Ka samar mana da wanda ya fi shi, amin.
Al’ummar wannan kasa ta Najeriya, daga wadanda suke son sa har wadanda suke adawa da salon mulkinsa, sun shiga jimami da alhini na rasuwar wannan bawan Allah. Da yawa daga cikin mutane kuma, tausayi ne ya kama su, saboda ganin irin wahalar da wannan bawan Allah ya sha kafin ya rabu da duniya. Wasu kuma, wadanda su ne kadan a cikin jama’a suna daukar cewa mutuwar kamar ma ba ta shafe su ba, domin suna ganin kamar mutuwar ta wasu rukuni na al’umma ce. Ko ma dai ya kowa yake kallon wannan rasuwa, abin da ya kamata al’umma su gane shi ne, Allah shi ke da iko a kan kowa da komai, komai karfin ka ko mulkinka ko kudinka, idan ta Allah ta zo babu tsimi ba dabara, haka za ka bar wannan duniyar ka tafi ka tarar da abin da ka shuka.
Rayuwa da rasuwar shugaban kasar Nijeriya, Alhaji Umaru Musa ‘Yar aduwa, wata aya ce ga duk wani mai hankali mai jini da kwakwalwa a jikinsa. Babban dalilin fadan hakan kuwa shi ne, a lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yar aduwa yana da rai, dukkan wani mahaluki mai hankali ya san cewa Umaru ya kai koluluwa a duk wani matsayin da dan adam zai yi buri a duniya. In ta bangaren kudi ne, Allah ya yi masa yadda mutum zai iya tabbatarwa da kansa cewa lallai Ummaru ya kai kololuwa. Ta fuskar mulki kuwa, nan ma sai da ya kure maleji, domin ya kai har karshe. irin mulkin da Allah ya ba shi, a cikin mutum Miliyan dari da hamsin, mutum sha uku ne kawai suka taba kai wannan matsayin. Haka kuma a bangaren duk wani dadi da mutum zai iya tunowa, Ummaru ya kai wajen har ya wuce.
Duk da wannan matsayi da daukaka da Allah Ya wadata Umaru da shi, sai ga shi Allah ya rage shi da ni’imar lafiya, wadda da Umaru yana da rai, shi zai fi tabbatar mana da haka. Wani abin mamaki da al’ajabi da aya, da Allah madaukakin Sarki Ya nuna mana a lokacin rayuwar ‘Yar aduwa shi ne, duk da wadancan abubuwa da Allah Ya huwace masa, sai ga shi da ransa a duniya, amma ana yin mulkin kuma yana ji yana gani, a gaban idonsa ake komai, amma shi ba shi da ikon ya sa bakinsa. Har ta zamanto komai za a yi, sai dai a yi da sunansa, amma shi din ba shi da ikon yin komai, kuma duk wata dama ta duniya da ake nema Allah Ya riga Ya ba shi, sai dai lafiya kadai ita ce Allah Ya rage shi da ita domin ya nuna aya ga ‘yan baya.
Wani abu da al’umma suke yi na rashin adalci shi ne, kin yabon mutum a lokacin da yake da rai ko don wannan din ya kara masa karfin gwiwa. A’a halinmu shi ne mu yi ta suka ko bambadanci, maimakon yabo da fadin gaskiya. Irin nau’in sukar da muke yi wa shugabanni wani lokacin bisa kage da karya, yakan dagula lissafin shugaba ya kasa komai kuma ya kin yin komai.
Babban dalilin fadin haka shi ne, sai bayan rasuwar shugaba ‘Yar aduwa ne, mutane suka fara sanin ayyukansa. Suka fara kwakwazo a kafafen yada labarai, wai shi ne ya yi kaza kuma shi ne ya yi kaza. Amma a lokacin yana raye ba a fadar wadannan abubuwa a matsayin wasu abubuwan ci gaba.
Daga cikin abubuwan da aka fi lissafawa sun hadar da daidaita da yafiya ga tsageru kuma ‘yan ta’addan Naija Delta, sai kuma gyara da ya yi a harkar tafiyar da tsarin bankuna. Daga nan kuma sai daidaita harkar NNPC, ko kuma a ce harkar hada-hadar man fetur, wanda wannan shi ne ya fi shafar talaka kai tsaye. Bayan wadanan akwai abubuwa da dama da shugaba ‘Yar aduwa ya gabatar a lokacin rayuwarsa musamman ga ‘yan Najeriya. Ko ba komai, yadda ya gaji wannan kasa daga hannun Obasanjo, da kuma yunkurin Obasanjon na wargatsa kasar a sakamakon ya rasa tazarce karo na uku, to ko namijin kokarin da shugaba ‘Yar aduwar ya yi wajen tsayar da kasar ba tare da ta tarwatsewa ba, shi ma abin a yaba masa ne. Hatta zabar ‘Yar aduwa da shugaba Obasanjo ya yi don ci gaba da tafiyar da wannan kasa, hakan ma wani yunkuri ne na rusa kasar da kuma jefa ta cikin halin ni-‘yasu.
Lallai kuwa ya rasu ya bar kasar nan a cikin halin kunci da talauci, kamar yadda yawancin shugabannin Najeriya suke rasuwa suna barinta. Wasu abubuwan da suka tafi ba daidai ba a zamanin shugaba ‘Yar aduwa suna da yawa, duk da dai a lokacin rayuwarsa, a iya ba shi uzurin rashin cikakkiyar lafiya, amma dai hakan ba zai hana a tabbatar cewa abubuwan ba su tafi yadda ake bukata ba. Za a iya tuno kudurori bakwai (7) da shugaba ‘Yar `aduwa ya kirkira kuma ya yi nufin cim musu. Daga cikin wadannan kudurori guda 7, ba wanda Allah Ya ba shi ikon ganin bayansa. Hatta a lokacin aka sanar da rasuwarsa, galibin sassan kasar nan ba wutar lantarki, balle maganar tsaro da asibiti da kayan abinci, da sauransu, wanda duk wadannan suna daga cikin kudurori bakwai da ya yi alkawarin cim ma a lokacin mulkinsa. To amma dai ta Allah ta tabbata gare shi, ba tare da ya kammala wa’adinsa a kan mulki ba balle a ga zai iya karasawa ko kuma a’a.
Fatanmu ga sabon shugaba wato Dr Goodluck Ebele Jonathan, shi ne mu ga ya dora a wurin da maigidansa ya tsaya. Duk da cewa a lokacin rantsar da shi, wato ranar Laraba 05 ga Mayun da muke ciki, ya tabbatar wa da ‘yan kasa cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne kan abubuwa muhimmai guda uku, wadanda daga ciki akwai Naija Delta wato yankin da ya fito. To a nan muke yi masa fatan alheri, gami da tabbatar masa da cewa lallai ya kamata ya tabbatar ya dora a kan inda mai gidansa ya tsaya.
Da fatan Allah Ya taimake mu, Ya kuma zaunar da wannan kasa tamu lafiya, shi kuma marigayi shugaba ‘Yar aduwa, Allah Ya jikansa da gafara, mu kuma Allah Ya kyauta namu zuwan idan tamu mutuwar ta riske mu, amin. Allah Ya ba wa iyalansa, musamman mahaifiyarsa, Hajiya Dada, da uwargidansa, Hajiya Turai da ‘ya’yansa da ‘yan uwansa, da abokan arziki da sauran ‘yan Najeriya hakurin jure wannan babban rashi.
Muhammad Sulaiman Abdullahi
muhammadunfagge@gmail.com This e-mail address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it
No. 335 dantumbushi Street Fagge D, Kano
**{Legacy activities, comments etc counter: 1155; topic series: 6; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 6- /*}