Topic: Tabarbarewar Karatun Addini A Makarantun Kwana
Timeline: 2010-06-14 23:04:41
Tabarbarewar Karatun Addini A Makarantun Kwana
A Rubuce Da Habibu Umar Yaro
An kafa makarantun kwana ne da manufa mai kyau a inda ake kai yara maza da mata domin su tattara hankalinsu a wuri guda su samu kyakkyawan karatu kuma ingantacce amma daga karshe sai ka ga garin neman gira an rasa ido. Abin nufi a nan shi ne za ka ga yara sun maida hankalinsu a kan karatun boko kawai amma karatun addini kuwa babu domin ba a cika kula da shi ba.
A yau idan muka duba za mu ga akwai dalibai dubbai a makarantun kwana wadanda suka hada da dalibai mata har da maza wadanda gaba dayansu sun riga sun bar gida a kalla tsawon shekaru shida amma abin bakin ciki sai ka ga yaro ko yarinya sun kammala sun dawo gida babu fahimtar addini saboda ba a damu da karatun addinin ba. Mafi yawancin lokuta idan ka ga ana karatun addini a irin wadannan makarantun, wasu daga cikin malamaine masu kishin addini a makaranta , suke ba da lokacinsu wajen koyar da yara ilmin addinin Musulunci, bayan an tashi daga karatu ko kuma ranakun da ba a karatun boko kamar Asabar da Lahadi. Shi ma ko da idan hakan ta samu baya wadatarwa saboda malaman su kansu suna da hidimomi irin nasu wadanda wasu lokutan ba sa samun damar koyar da yaran domin ba shi ne abin da aka dauke su su yi ba, suna dai yi ne kawai domin taimako .
Duk wani malami da yake koyarwa a makarantar kwana, ko kuma wani wanda ya yi nazarin rayuwar daliban makarantun kwana, hakika na san zai yarda da ni cewa sau da yawa wasu lokutan za ka ga irin wadannan makarantu suna ta kokarin karatu wajen saukar da yara karatun Alkur’ani tun daga Bakara har Nasi amma idan za ka bincika za ka samu mafi yawanci daliban ba su iya karatun ba. Abin kusan ana yin sa ne a wani mataki na gasa amma ba wai domin yara su koyi karatun ba, a’a abin ya zama waccan makaranta ta yi sauka mu ma sai mun yi.
To wadannan matsaloli da ake samu, ni a nawa tunanin, laifin na gwamnati ne, wanda bai kamata a gari ko kuma jiha ta musulmai a ce ana samun irin wannan matsalaba musamman ma a jihohi na musulmai da suke ikirarin gudanar da shari’ar Musulunci kamar misali Kano da Jigawa da sauransu.
Hakika koyar da yara maza da mata karatun Alkur’ani da sauran fannoni na addini wajibi ne domin sanin hukunce-hukunce wajen gudanar da ibada ga Allah (SWT).
Kuma ya kamata yaro ko yarinya tun suna kanana su koyi ilmin addini, domin su girma abin ya ratsa su. Don haka nake kira da babbar murya ga gwamnatoci musamman masu cewa suna gudanar da Sha’riar musulunci da su kula da karatun addini a makarantu kwana wajen daukar kwararrun malamai na musamman domin koyar da yara karatun Alkur’ani da sauran fannoni na addini. Kuma gwamanti ta yanka musu albashi mai tsoka domin su maida hankali wajen koyar da dalibai idan kuwa har gwamnati za ta ci gaba da nuna hakin shakulatin bangaro da karatun addini a makarantun kwana ya kamata iyaye masu kishin addini su daina kai ‘ya`yansu makarantun kwana, (boarding schools) gara su saka su a makarantun jeka ka dawo (day schools) idan sun dawo su tafi Islamiyya domin koyar karatun Alkur’ani da sauran fannoni na addini. Annabi {SAW} ya fada mana a hadisi cewa Dukkaninku masu kiwo ne, kuma sai an tambayeku abin da aka baku kiwo”. To idan mukayi nazarin wannan Hadisin za mu ga hakika akwai kalubale ga iyaye da Gwamnati wajen kula da karatu da tarbiyyar yara.
Allah Ya sa mu gane kuma mu gyara, amin.
Habibu Umar Yaro
Unguwar Kududdufawa Kano,GSM: 08030869999
e-mail:habib uyaro@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 2077; topic series: 3; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 3- /*}