Topic: Tuba da istigfari (3)
Timeline: 2012-03-27 18:40:39
Tuba da istigfari (3)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka makon jiya mun tabo istigfari da kalmomi masu alaka da shi, to yau za mu dora kamar haka:
Maganganun Malamai kan bambancin tuba da istigafari:
Idan aka hada ambaton tuba da istigfari, to a lokacin istigfarin ya zama neman gafara ta addu’a, tuba kuma ita ce yin nadama a bisa laifi tare da niyyar kin komawa da sabon. (Alfarkul Lagawiyya, shafi na 195).
Kuma an ce idan aka hada istigfari da tuba, to yana nufin nema tsari daga sharrin da ya gabata, tuba kuma juyawa zuwa ga aikin kwarai da neman tsari daga sharrin abin da mutum yake tsoro a gaba na daga miyagun ayyukansa. Kuma har wa yau istigfari yana daga cikin babin gusar da cuta, yayin da tuba yake nufin neman amfani, wato gafara ita ce a tsare mutum daga sharrin zunubi, tuba kuma ta samar masa da tsaro kana bin da yake so a bayanta. (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 1 shafi na 307-308)
Amma idan aka ambaci istigfari shi kadai ko tuba ita kadai, to dukka ma’anarsu daya ce. Ibn kayyim ya ce: “Ambaton istigfari shi kadai kamar tuba ce, shi kansa tuba a kashin kansa tare da kunsar neman gafara daga Allah, wato neman a shafe zunubi a kawar da gurbinsa a kuma tsare mutum daga sharrinsa, ba kamar yadda wadansu mutane suke zato ba, cewa gafara tana nufin suturcewa ce kawai, domin Allah Yana suturce ma wanda Ya yi masa gafara da wanda bai yi masa gafara ba, kuma suturcewar ta lizimci abin da ake ambata ko yankinsa.” (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 1 shafi na 308-309).
Na biyu alkara inaba da tuba:
Inaba kamar tuba ce, kasancewar tana nufin komawa ga Allah. Ibn Manzur yana cewa: “Inaba ita ce komawa ga Allah ta hanyar tuba.” (Lisanul Arab, Mujalladi na 14 shafi na 319)
Sai dai wadansu malamai kamar Ar-Ragib Al-Isfahani da Ibn kayyim da Almawurdi da Ibn Manzur da Aljauhari, suna ganin inaba wata ma’ana ce da aka kara a kan tuba.
Ibn kayyim (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, “Wanda ya tuba kuma ya tsayu a matsayinta, ya sauka a kan dukkan masaukan Musulunci, domin tuba cikakkiya ta kunshe su, ita mai shiga cikinsu ne. amma idan duddugensa ya tabbata a masaukin tuba, to sai ya sauka a masaukin inaba a bayan hakan.” (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 1 shafi na 133-134)
Na uku alakar awwabah da tuba:
Awwabah ma tana nufin komawa ga Allah kamar tuba. Ibn Manzur ya ce: “Al’awwabu, yana nufin komawa. Aba ila shai’in, ya koma, kuma ana cewa ya’ubu awwaban wa iyaban wa aubatun wa aibatun.” (Lisanul Arab, Mujalladi na 14 shafi na 319)
Shi kuma Azzubaidi cewa ya yi: “Al’awbatu-komawa, Aba shai’in-ya koma, kuma ana cewa awwabu da ta’awwaba da ayyaba, dukkansu dai ma’anarsu ya koma.” (Tajul Arus Min Jawahiril kamus, Mujalladi na 1 shafi na 152).
Hukuncin tuba da sharuddanta
Alkur’ani Mai girma da Sunnah sun yi umarni da tuba, daga cikin abin da ya zo cikin Alkur’ani akwai fadin Allah Madaukaki: “Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, ya ku muminai! Tsammaninku ku samu babban rabo.” (k: 24: 31).
As- Sa’adiy ya ce: “Allah Ya yi umarni da tuba, sai Ya ce: “Ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, ya ku muminai! Tsamanninku ku samu babban rabo.” Sannan Ya jnigina samun babban rabo ko nasara da tuba, don haka ba hanyar samun babban rabo da nasara sai da tuba. Tuba kuma ita ce barin abin da Allah Yake ki a fili da boye zuwa ga abin da Yake so a fili da boye. Wannan yana nuni da cewa kowane mumini yana bukatar tuba, saboda Allah Yana magana ne da muminai gaba daya, kuma a cikin hakan akwai kwadaitarwa ga ikhlasi a cikin tubar.” (Taisirul Karimir Rahman, shafi na 516)
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku nemi Ubangijinku gafara, sannan kuma ku tuba zuwa gare Shi. Lallai Ubangijina Mai jin kai, Mai nuna soyayya.” (k: 11: 90). Kuma Ya sake cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku koma (tuba) zuwa ga Allah komawar gaskiya…” (k: 66: 8). Da ayyoyi da dama da suka yi magana kan tuba.
Amma Hadisan da suke shiryarwa zuwa ga tuba daga cikinsu akwai:
An karbo daga Burdah, ya ce “Na ji Al-Agar Almazini (RA) yana ba Ibn Umar labara, ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah, domin ni ina tuba a kowane wuni sau dari.” Muslim ya ruwaito a Hadisi na 2702
Ayoyi da Hadisin da suka gabata, suna umarni da tuba, kuma asalin kowane umarni wajibci ne, ba a juya shi zuwa mustahabbanci said a wata karina, kuma babu karinar a nan. (Nihayatus Saul fi Sharhi Minhajil Usul, Mujalladi na 2 shafi na 251 da Irshadil Fuhul Ila Tahkikil Hakki Min Ilimil Usul, Mujalladi na 86 shafi na 102).
Khurdabi ya ce: “Al’umma ta hada a kan cewa tuba farilla ce a kan muminai.” (Aljami’u Li’ahakamil kur’an, Mujalladi na 5 shafi na 90).
Kuma ya ce: “Ita faralin aini ce a kan daidaikun mutane a kowane hali da zamani.” (Aljami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 18 shafi na 197 da Mujalladi na 12 shafi na 238)
Shaihul Islam Ibn Taimiyya ya ce: “Babu makawa ga kowane bawa ya rika tuba, ita wajiba ce a kan mutane farko da na karshe.” (Majmu’u Fatawi na Ibn Taimiyya, Mujalladi na 10 shafi na 310).
Nazari yana karfafa cewa mutum bai kubuta daga aikata sabo, ba mutumin da yake kubuta daga wannan nakasa, sai dai a samu wani ya fi wani gwargwado-gwargwado. Amma yin kuskure ko sabo abu ne da babu makawa, don haka ne aka tilsta tuba ta gaskiya, kuma kan haka ne Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Dukkan ’yan Adam masu kuskure ne, mafiya alherin masu kuskure, su ne masu tuba.” Tirmizi da Ibn Majah da Ahmad suka ruwaito shi.
Domin haka ne mantuwa da gazawa suka zamo dabi’ar mutum.
Kuma saboda zunubi tana samuwa ne sakamakon kaucewar mutum daga madaidaiciyar hanya kuma tana illa ga jin dadin dan Adam, sai ya zamo tana barazana ga rayuwar mutane, tana nakasa jin dadinta tana kai tag a mahalaka, don haka ba wani daga cikin masu hankali da zai yarda da wannan tafiya a ce ya tsaya ba ya wani yunkuri na gyara shi. Domin haka tuba ta zama wajibi bisa hujja ta hankali da ingantaccen nazari. (Hadir Ruh Ila Ahkamil Taubatun Nusuh, shafi na 5, kuma a duba littafin Attaubah na Dokta Amal Nusair, shafi na 24)
Tuba wajiba ce daga kowane zunubi babba da karami, wanda aka sani da wanda ba a sani ba, wanda aka yi bisa ganganci ne ko wanda aka yi bisa mantuwa, da gaske ne ko da wasa. Wannan urmanin Allah Madukaki ne ga bayinSa. Kuma wannan umarni na gam-hade ne, ya kunshi dukkan zunubi bai kebe tuba daga wani zunubi ban da wani ba.
Imam Razi yana fadi wajen tafsirin fadin Allah Madaukaki: “Sai wadanda suka tuba kuma suka gyara, kuma suka bayyana, to, wadannan Ina karbar tubarsu.” (k: 2: 160). “Tuba ba ta zama tuba, sai da barin abin da ya kamata a bari, da aikata abin da ya kamata a aikata.” (Tafsirul Alfakharu Ar-Razi, Mujalladi na 4 shafi na 150).
A cikin Sunnar Manzon Allah (SAW) akwai Hadisai da yawa da suke nuni a kan yadda (Sallalahu Alaihi wa alihi Wasallam) yake yawaita tuba, kuma a cikin aikinsa akwai karantarwa ga al’ummarsa (SAW).
An karbo daga Abu Musa daga Annabi (SAW) cewa ya kasance yana addu’a da wannan addu’a: “Ya Ubangiji! Ka gafarta min kuskurena da jahilicina da wuce ka’idata a cikin dukkan al’amarina, da abin da Ka fi ni saninsa. Ya Ubangiji! Ka gafarta min kurakuraina da gangancina da jahilicina da kakacina da dukkan abin da ke wurina. Ya Ubangiji! Ka gafarta min abin da na gabatar da wanda na jinkirtar da wanda na boye da wanda na bayyana. Kai ne Magabaci kuma Kai ne Majinkirci, kuma Kai a kan dukkan komai Mai iko ne.” Buhari ya ruwaito shi a Hadisi na 6390.
Abin da wannan Hadisi yake nuni shi ne lallai bawa yana rokon Allah tuba da gafara ne a dukkan halayensa na ganganci da jahilci da kakaci da abin ya aikata a boye ko a fili.
Sai mako na gaba insha-Allah za mu dora.
Wassalamu alaikum
**{Legacy activities, comments etc counter: 1064; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}