Topic: Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (3)
Timeline: 2012-03-27 18:53:46
Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (3)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Na so a ce rubutuna kan Ashura ya fito tun a makon jiya, kafin Ranar Ashura, to amma sai ya zamo maganar da na faro kan hijira ba ta kammalu yadda za a jingine ta ba. Alhamdu lillahi ala kulli halin, yau za mu kammala batu kan hijirar har mu duba Ashura wadda daya ce daga cikin ranakun Muharram da wadansu abubuwa masu dadi da marasa dadi suka faru a cikinta da za a ci gaba da tattaunawa kanta, bismillah:
An ce adadin wadanda suka marabci Annabi (SAW) sun kai Ansar (mutanen Madina) 500, maza da mata suka hahhau saman gidaje samari da ’yan mata suka mamaye kan hanyoyi suna cewa: “Ya Muhammad! Ya Rasulullah! Albarra’u ya ce:”Ban taba ganin mutanen Madina sun yi farin cikin da ya kai farin cikinsu ga (isowar) Annabi (SAW) ba.”
Anas yana cewa: “Na gan shi ranar da ya shiga Madina, ban taba ganin wata rana ba a rayuwata da ta fi wannan kyau da haske kamar ranar da ya shigo mana.” Ahmad ya ruwaito, Hadisi na 3925.
Wannan hijira ba fa ta jin dadin duniya ce ba, a’a hijira ce ta tilas don tsira da addini daga darkakewar makiya. Wannan ne ya sanya bayan wafatin Manzon Allah (SAW), manyan masoyansa da suka tashi yanke shawara kan ajiye wa mabiyansa kalandar kidayar shekara bayan an kai an kawo game da a dauki lokacin haihuwarsa ko lokacin fara saukar wahayi da sauransu, wadannan masoya nasa suka yanke shawarar cewa a dauki hijirasa (SAW).
To amma abin bakin ciki ba ma a turke mutum ya yi bayani kan hijirar da abubuwan da ta kunsa ba, a’a a ce masa yau nawa ne ga watan Hijira sai ya tsaya yana kame-kame, wannan ya fi komai takaici.
Galibin Musulmi a yau sun jahilci kidayar kwanakin Hijira sun jahilci hatta sunayen watannin Musulunci. Ba su kidaya sai dai na Turawa ko makamantansu.
Sheikh Abu Ya’ala Az-Zawwawi (Allah Ya yi masa rahama) bayan ya yi bayani kan yadda aka samo kidayar Hijira sai ya ce: “Yana daga cikin jahilci da gafala ko a ce abin kunya da takaici a samu Musulmi yana lissafin kwanakin shekara da watan Yuni ko Afrilu da Agusta da sauransu, duk da cewa shekarar Hijira ta soke ta. Sai ya bar wanda ya shafe ya sanya Hijira abar kauracewa, Allah Ya yi mana tsari…. Wane irin gafala ne wannan! Abin da ake bukata a fahimci Hijirar da ma’abucin Hijirar (SAW) da wadanda suka biyo bayansa da wadanda suka biyo su daga cikin al’ummarsa har zuwa Ranar Sakamako.” ( a duba: Samaratul Ula li Jam’iyyatut Talbatil Jaza’irin Az-Zaituniyin, shafi na 41-42.)
Yanzu bari mu leka Ashura azuminta da bidi’o’in da aka shigar cikinta.
Mece ce Ashura?
Ashura da maddi (ja) tana nufin ranar 10 ga Muharram ne, wadansu sun ce tara. (Lisanul Arab, Mujalladi na 5 shafi na 2952-2953).
Imam Khurdabi ya ce, “An kira ta da Ashura ce don mubalaga da girmamawa (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 245).
Amma abin da aka ambata na cewa an kira ta da wannan suna ne, saboda Allah Madaukaki Ya karrama Annabwa10 da karamomi 10 a cikinta, ko kuma ita ce karramawa ta 10 da aka yi wa wannan al’umma ba ya da dalili ingatacce. (Almannawi ya ambaci haka a cikin Alfaidu, Mujalladi na 4 shafi na 299).
Wace rana ce wannan?
Ma’abuta shari’a sun samu sabani kan ayyana ta zuwa gida biyu:
1. Magana ta farko: Cewa ita ce ranar 10 ga watan Allah mai alfarma na Muharram. Wannan shi ne maganar Jamhurun Malamai daga Salaf da Khalaf. Daga cikin wadanda suka fadi haka akwai Sa’idu bin Musayyib da Hasanul Basri da Malik da Ahmad da Is’hak da sauransu da dama, kuma wannan shi ne zahirin Hadisai da manufar lafazin kalmar.
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da azumin Ashura, ranar 10 ga wata.” Tirmizi ya ruwaito a babin azumi, Hadisi na 755.
Zubairu bin Munir ya ce: “Mafi yawa sun tafi a kan ranar Ashura ita ce ranar 10 ga watan Allah Muharram.” (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 245).
2. Magana ta biyu: Cewa ita ce ranar tara ga Muharram. Wannan shi ne zahirin maganar Ibnu Abbas. Kuma a kan haka yini ya kasance ana idafarsa ga dare mai zuwa ne.
An karbo daga Alhakam bin A’araj ya ce: “Na je wurin Ibnu Abbas (RA) a kusa da Zam-Zam sai ne ce masa: “Ka ba ni labari kan ranar Ashura?” Sai ya ce: “Idan ka ga jinjirin watan Muharram ka kidaya ka wayi asubahin ranar tara kana mai azumi.” Sai na ce: “Shin haka Annabi (SAW) ya kasance yana azumtarsa?” Ya ce, “Eh haka ne!” Muslim Ya ruwaito a babin azumi.
Sai dai Zubairu Ibnu Munir ya yi sharhi kan maganar Ibnu Abbas inda ya ce: “Maganarsa: “Idan ka wayi garin tara” yana nuni ne da ranar 10. Domin ba ya wayar garin ranar tara yana mai azumi, bayan ya wayi asubar tara face ya yi niyyar azumin don daren da ke zuwa wato daren 10 ga watan.”
Hafiz Ibnu Hajrin ya ce: “Wannan fahimta tana karfafa abin da Muslim ya ruwaito har wa yau ta wata fuskar daga Ibnu Abbas cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Idan na kai badi zan azumci tara.” Muslim ya ruwaitoa babin azumi. Sai ya rasu kafin hakan. Wannan a zahiri ya nuna Annabi (SAW) yana azumtar 10 ga watan ne, kuma ya yi himmar ya azumci tara sai ya rasu kafin haka.” (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 245).
Ibnu kayyim ya ba maganar Ibnu Abbas wata fassara ta daban inda ya ce: “Bisa fahimtar maganarsa (RA): “Ku yi azumin tara da goma, ku saba wa Yahudawa”: Yana nuna maganar Ibnu Abbas: “Idan ka ga jinjirin watan Muharram ka kidaya, idan ya kai ranar tara ka wayi gari kana mai azumi” ba yana nufin Ashura ranar tara ce ba. A’a ya umarce shi ne da ya yi azumin ranar tara gabanin Ashura………..” (Tahzibus Sunnan, Mujalladi na 3 shafi na 323-324).
Azumin Ranar Ashura:
Akwai Hadisai da dama da suka kwadaitar kan azumin ranar Ashura, daga ciki akwai:
“Lallai azumin Ashura yana kankare zunubin shekara daya, kuma lallai azumin ranar Arfa yana kankanre na shekara biyu.” (Fathul Bari, Mujalladi na 5 shafi na 249).
Abdullahi dan Umar ya ce: “Mutanen Jahiliyya sun kasance suna azumtar Ashura. Kuma Manzon Allah (SAW) da Musulmi sun azumce shi kafin a farlanta Ramadan. Da aka farlanta Ramadan sai (SAW) ya ce: “Lallai Ashura rana ce daga cikin ranakun Allah. Wanda ya so ya azumce ta, wanda ya so ya bari.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Annawawi ya ce: “Malamai sun hadu a kan azumin ranar Ashura Sunnah ne ba wajibi ba. Kuma an ruwaito makaruhancin niyyar azuminta da kebe ta da azumi daga Ibnu Umar. Sai dai malamai sun hadu a kan mustahabbancinta da ayyana ta da azumi.” (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 246).
Hikimar azumtarta:
Ranar Ashura ita ce ranar da Allah Ya tserar da Annabi Musa (AS) da mutanensa daga Fir’auna da rundunarsa. Sai Annabi Musa (AS) ya azumce ta don godiya ga Allah Madaukaki. Kuma Annabinmu (SAW) ya azumce ta kuma ya yi umarni a azumce ta ya ce: “Mu ne muka fi cancanta da Musa a kanku.”
Don haka Manzon Musulunci da Musulmi ne suka fi cancanta da Annabi Musa da sauran Annabawa da Manzanni (Aminicin Allah Ya kara tabbata a gare su.” Domin sun yi imani da abin da Manzannin suka zo da shi kuma ba su nuna bambanci a tsakanin daya daga cikinsu, sun yi imani da su baki daya, suna sonsu suna girmama su suna taimakon addininsu wanda shi ne mika wuya ga Allah Ubangijin talikai.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1854; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}