Prev  

17. Surah Al-Isrâ' سورة الإسراء

  Next  
Ayah  17:1  الأية
    +/- -/+  
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
سُبْحَانَ الَّذِي أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِ لَيْلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَى الْمَسْجِدِ الْأَقْصَى الَّذِي بَارَكْنَا حَوْلَهُ لِنُرِيَهُ مِنْ آيَاتِنَا ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
Hausa
 
Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da băwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dőmin Mu nũna masa daga ăyőyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Ayah  17:2  الأية
    +/- -/+  
وَآتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَجَعَلْنَاهُ هُدًى لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُوا مِن دُونِي وَكِيلًا
Hausa
 
Kuma Mun bai wa Mũsă littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isră'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa.

Ayah  17:3  الأية
    +/- -/+  
ذُرِّيَّةَ مَنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَبْدًا شَكُورًا
Hausa
 
Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tăre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani băwa mai gődiya.

Ayah  17:4  الأية
    +/- -/+  
وَقَضَيْنَا إِلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ فِي الْكِتَابِ لَتُفْسِدُنَّ فِي الْأَرْضِ مَرَّتَيْنِ وَلَتَعْلُنَّ عُلُوًّا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isră'ĩla a cikin Littăfi, cewa lalle ne, kună yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kună zălunci, zălunci mai girma.

Ayah  17:5  الأية
    +/- -/+  
فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ أُولَاهُمَا بَعَثْنَا عَلَيْكُمْ عِبَادًا لَّنَا أُولِي بَأْسٍ شَدِيدٍ فَجَاسُوا خِلَالَ الدِّيَارِ ۚ وَكَانَ وَعْدًا مَّفْعُولًا
Hausa
 
To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu băyi Nămu, ma'abũta yăƙi mafĩ tsanani, har su yi yăwo a tsakănin gidăjenku, kuma yă zama wa'adi abin aikatawa.

Ayah  17:6  الأية
    +/- -/+  
ثُمَّ رَدَدْنَا لَكُمُ الْكَرَّةَ عَلَيْهِمْ وَأَمْدَدْنَاكُم بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَجَعَلْنَاكُمْ أَكْثَرَ نَفِيرًا
Hausa
 
Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyőyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan măsu fita yăƙi.

Ayah  17:7  الأية
    +/- -/+  
إِنْ أَحْسَنتُمْ أَحْسَنتُمْ لِأَنفُسِكُمْ ۖ وَإِنْ أَسَأْتُمْ فَلَهَا ۚ فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ الْآخِرَةِ لِيَسُوءُوا وُجُوهَكُمْ وَلِيَدْخُلُوا الْمَسْجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَلِيُتَبِّرُوا مَا عَلَوْا تَتْبِيرًا
Hausa
 
Idan kun kyautata, kun kyautata dőmin kanku, kuma idan kun mũnana to dőmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe ya jẽ, (za su je) dőmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lőkaci, kuma dőmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.

Ayah  17:8  الأية
    +/- -/+  
عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يَرْحَمَكُمْ ۚ وَإِنْ عُدتُّمْ عُدْنَا ۘ وَجَعَلْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَافِرِينَ حَصِيرًا
Hausa
 
Akwai tsammănin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun săke Mu săke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kăfirai.

Ayah  17:9  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ هَٰذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ وَيُبَشِّرُ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْرًا كَبِيرًا
Hausa
 
Lalle ne wannan Alƙur'ăni yană shiryarwa ga (hălayen) waɗanda suke mafi daidaita kuma yană băyar da bushăra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sună da wata ijăra. mai girma."

Ayah  17:10  الأية
    +/- -/+  
وَأَنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmăni da Lăhira, Mun yimusu tattalin wata azăba mai raɗaɗi.

Ayah  17:11  الأية
    +/- -/+  
وَيَدْعُ الْإِنسَانُ بِالشَّرِّ دُعَاءَهُ بِالْخَيْرِ ۖ وَكَانَ الْإِنسَانُ عَجُولًا
Hausa
 
Kuma mutum yană yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggăwa.

Ayah  17:12  الأية
    +/- -/+  
وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ آيَتَيْنِ ۖ فَمَحَوْنَا آيَةَ اللَّيْلِ وَجَعَلْنَا آيَةَ النَّهَارِ مُبْصِرَةً لِّتَبْتَغُوا فَضْلًا مِّن رَّبِّكُمْ وَلِتَعْلَمُوا عَدَدَ السِّنِينَ وَالْحِسَابَ ۚ وَكُلَّ شَيْءٍ فَصَّلْنَاهُ تَفْصِيلًا
Hausa
 
Kuma Mun sanya dare da răna, ăyőyi biyu, sa'an nan Muka shăfe ăyar dare, kuma Muka sanya ăyar răna mai sanyăwa a yi gani, dőmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dőmin ku san ƙidăyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kőme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanăwa.

Ayah  17:13  الأية
    +/- -/+  
وَكُلَّ إِنسَانٍ أَلْزَمْنَاهُ طَائِرَهُ فِي عُنُقِهِ ۖ وَنُخْرِجُ لَهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ كِتَابًا يَلْقَاهُ مَنشُورًا
Hausa
 
Kuma kőwane mutum Mun lazimta masa abin rekődinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rănar ˇiyăma da littăfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.

Ayah  17:14  الأية
    +/- -/+  
اقْرَأْ كِتَابَكَ كَفَىٰ بِنَفْسِكَ الْيَوْمَ عَلَيْكَ حَسِيبًا
Hausa
 
"Karanta Littăfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisăbi a kanka a yau."

Ayah  17:15  الأية
    +/- -/+  
مَّنِ اهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبْعَثَ رَسُولًا
Hausa
 
Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dőminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bă ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama măsu yin azăba ba, sai Mun aika wani Manzo.

Ayah  17:16  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا أَرَدْنَا أَن نُّهْلِكَ قَرْيَةً أَمَرْنَا مُتْرَفِيهَا فَفَسَقُوا فِيهَا فَحَقَّ عَلَيْهَا الْقَوْلُ فَدَمَّرْنَاهَا تَدْمِيرًا
Hausa
 
Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadătanta, har su yi făsicci a cikinta, sa'an nan maganar azăba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkăke ta, darkăkẽwa.

Ayah  17:17  الأية
    +/- -/+  
وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِنَ الْقُرُونِ مِن بَعْدِ نُوحٍ ۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِ خَبِيرًا بَصِيرًا
Hausa
 
Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a băyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban băyinSa, Mai gani.

Ayah  17:18  الأية
    +/- -/+  
مَّن كَانَ يُرِيدُ الْعَاجِلَةَ عَجَّلْنَا لَهُ فِيهَا مَا نَشَاءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلْنَا لَهُ جَهَنَّمَ يَصْلَاهَا مَذْمُومًا مَّدْحُورًا
Hausa
 
Wanda ya kasance yană nufin mai gaggăwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙőnu da ita, yană abin zargi kuma abin tunkuɗewa.

Ayah  17:19  الأية
    +/- -/+  
وَمَنْ أَرَادَ الْآخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعْيَهَا وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُولَٰئِكَ كَانَ سَعْيُهُم مَّشْكُورًا
Hausa
 
Kuma wanda ya nufi Lăhira, kuma ya yi aiki sabőda ita irin aikinta alhăli kuwa yană mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gődadde.

Ayah  17:20  الأية
    +/- -/+  
كُلًّا نُّمِدُّ هَٰؤُلَاءِ وَهَٰؤُلَاءِ مِنْ عَطَاءِ رَبِّكَ ۚ وَمَا كَانَ عَطَاءُ رَبِّكَ مَحْظُورًا
Hausa
 
Dukkansu Mună taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba.

Ayah  17:21  الأية
    +/- -/+  
انظُرْ كَيْفَ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ وَلَلْآخِرَةُ أَكْبَرُ دَرَجَاتٍ وَأَكْبَرُ تَفْضِيلًا
Hausa
 
Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da săshensu a kan săshe! Kuma lalle ne Lăhira ce mafi girman darajőji, kuma mafi girman fĩfĩtăwa.

Ayah  17:22  الأية
    +/- -/+  
لَّا تَجْعَلْ مَعَ اللهِ إِلَٰهًا آخَرَ فَتَقْعُدَ مَذْمُومًا مَّخْذُولًا
Hausa
 
Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tăre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe.

Ayah  17:23  الأية
    +/- -/+  
وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا ۚ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا
Hausa
 
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kőwa făce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsăwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.

Ayah  17:24  الأية
    +/- -/+  
وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُل رَّبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا
Hausa
 
Kuma ka sassauta musu fikăfikan tausasăwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnőna, ina ƙarami."

Ayah  17:25  الأية
    +/- -/+  
رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمْ ۚ إِن تَكُونُوا صَالِحِينَ فَإِنَّهُ كَانَ لِلْأَوَّابِينَ غَفُورًا
Hausa
 
Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin răyukanku. Idan kun kasance sălihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga măsu kőmawa gare Shi, Mai găfara.

Ayah  17:26  الأية
    +/- -/+  
وَآتِ ذَا الْقُرْبَىٰ حَقَّهُ وَالْمِسْكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرْ تَبْذِيرًا
Hausa
 
Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyarka, bazzarăwa.

Ayah  17:27  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ الْمُبَذِّرِينَ كَانُوا إِخْوَانَ الشَّيَاطِينِ ۖ وَكَانَ الشَّيْطَانُ لِرَبِّهِ كَفُورًا
Hausa
 
Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kăfirci.

Ayah  17:28  الأية
    +/- -/+  
وَإِمَّا تُعْرِضَنَّ عَنْهُمُ ابْتِغَاءَ رَحْمَةٍ مِّن رَّبِّكَ تَرْجُوهَا فَقُل لَّهُمْ قَوْلًا مَّيْسُورًا
Hausa
 
Ko dai ka kau da kai daga gare su dőmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fătanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi.

Ayah  17:29  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَجْعَلْ يَدَكَ مَغْلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبْسُطْهَا كُلَّ الْبَسْطِ فَتَقْعُدَ مَلُومًا مَّحْسُورًا
Hausa
 
Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗăwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.

Ayah  17:30  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ رَبَّكَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُ كَانَ بِعِبَادِهِ خَبِيرًا بَصِيرًا
Hausa
 
Lalle ne Ubangijinka Yană shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yană ƙuƙuntăwa. Lalle Shi, Yă kasance Mai sani ga băyinSa, Mai gani.

Ayah  17:31  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَاقٍ ۖ نَّحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُمْ ۚ إِنَّ قَتْلَهُمْ كَانَ خِطْئًا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma kada ku kashe 'yă'yanku dőmin tsőron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yă kasance kuskure babba.

Ayah  17:32  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
Hausa
 
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfăsha ce kuma tă mũnăna ga zama hanya.

Ayah  17:33  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَقْتُلُوا النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللهُ إِلَّا بِالْحَقِّ ۗ وَمَن قُتِلَ مَظْلُومًا فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِ سُلْطَانًا فَلَا يُسْرِف فِّي الْقَتْلِ ۖ إِنَّهُ كَانَ مَنصُورًا
Hausa
 
Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta făce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yană wanda aka zălunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.

Ayah  17:34  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَقْرَبُوا مَالَ الْيَتِيمِ إِلَّا بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ حَتَّىٰ يَبْلُغَ أَشُدَّهُ ۚ وَأَوْفُوا بِالْعَهْدِ ۖ إِنَّ الْعَهْدَ كَانَ مَسْئُولًا
Hausa
 
Kuma kada ku kusanci dũkiyar marăya făce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yă kasance abin tambayăwa ne.

Ayah  17:35  الأية
    +/- -/+  
وَأَوْفُوا الْكَيْلَ إِذَا كِلْتُمْ وَزِنُوا بِالْقِسْطَاسِ الْمُسْتَقِيمِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
Hausa
 
Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.

Ayah  17:36  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ ۚ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا
Hausa
 
Kuma kada ka bi abin da bă ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yă kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

Ayah  17:37  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تَمْشِ فِي الْأَرْضِ مَرَحًا ۖ إِنَّكَ لَن تَخْرِقَ الْأَرْضَ وَلَن تَبْلُغَ الْجِبَالَ طُولًا
Hausa
 
Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bă ză ka hũda ƙasa ba kuma bă ză ka kai a duwătsu ba ga tsawo.

Ayah  17:38  الأية
    +/- -/+  
كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُ عِندَ رَبِّكَ مَكْرُوهًا
Hausa
 
Dukan wancan mli mũninsa yă kasance abin ƙyăma a wurin Ubangijinka.

Ayah  17:39  الأية
    +/- -/+  
ذَٰلِكَ مِمَّا أَوْحَىٰ إِلَيْكَ رَبُّكَ مِنَ الْحِكْمَةِ ۗ وَلَا تَجْعَلْ مَعَ اللهِ إِلَٰهًا آخَرَ فَتُلْقَىٰ فِي جَهَنَّمَ مَلُومًا مَّدْحُورًا
Hausa
 
Wancan yănă daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautăwa na daban tăre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kană wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa

Ayah  17:40  الأية
    +/- -/+  
أَفَأَصْفَاكُمْ رَبُّكُم بِالْبَنِينَ وَاتَّخَذَ مِنَ الْمَلَائِكَةِ إِنَاثًا ۚ إِنَّكُمْ لَتَقُولُونَ قَوْلًا عَظِيمًا
Hausa
 
Shin fa, Ubangijinku Ya zăɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya măta daga mală'iku? Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kună faɗar magana mai girma!

Ayah  17:41  الأية
    +/- -/+  
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ لِيَذَّكَّرُوا وَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا نُفُورًا
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayăni a cikin wannan Alƙur'ăni dőmin su yi tunăni, kuma bă ya ƙăra musu kőme făce gudu.

Ayah  17:42  الأية
    +/- -/+  
قُل لَّوْ كَانَ مَعَهُ آلِهَةٌ كَمَا يَقُولُونَ إِذًا لَّابْتَغَوْا إِلَىٰ ذِي الْعَرْشِ سَبِيلًا
Hausa
 
Ka ce: "Dă akwai waɗansu abũbuwan bautăwa tăre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lőkacin, dă (abũbuwan bautăwar) sun nẽmi wata hanya zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."

Ayah  17:43  الأية
    +/- -/+  
سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوًّا كَبِيرًا
Hausa
 
TsarkinSa yă tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗă, ɗaukaka mai girma.

Ayah  17:44  الأية
    +/- -/+  
تُسَبِّحُ لَهُ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ وَالْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا
Hausa
 
Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sună yi Masa tasbĩhi. Kuma băbu wani abu făce yană tasbĩhi game da gőde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai găfara.

Ayah  17:45  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآنَ جَعَلْنَا بَيْنَكَ وَبَيْنَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ حِجَابًا مَّسْتُورًا
Hausa
 
Kuma idan ka karanta Alƙur'ani, sai Mu sanya a tsakăninka da tsakanin waɗanda bă su yin ĩmăni da Lăhira wani shămaki mai suturcẽwa.

Ayah  17:46  الأية
    +/- -/+  
وَجَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْرًا ۚ وَإِذَا ذَكَرْتَ رَبَّكَ فِي الْقُرْآنِ وَحْدَهُ وَلَّوْا عَلَىٰ أَدْبَارِهِمْ نُفُورًا
Hausa
 
Kuma Mu sanya marufai a kan zukătansu dőmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ăni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dőmin gudu.

Ayah  17:47  الأية
    +/- -/+  
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَسْتَمِعُونَ بِهِ إِذْ يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ وَإِذْ هُمْ نَجْوَىٰ إِذْ يَقُولُ الظَّالِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا
Hausa
 
Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurăre da shi a lőkacin da suke yin saurăren zuwa gare ka, kuma a lőkacin da suke măsu gănăwa a tsakăninsu a lőkacin da azzălumai suke cẽwa, "Bă ku biyar kőwa făce wani namiji sihirtacce."

Ayah  17:48  الأية
    +/- -/+  
انظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا لَكَ الْأَمْثَالَ فَضَلُّوا فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا
Hausa
 
Ka dũba yadda suka buga maka misălai, sai suka ɓace bă su iya sămun hanya.

Ayah  17:49  الأية
    +/- -/+  
وَقَالُوا أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا وَرُفَاتًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا
Hausa
 
Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓăɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tăyarwa ne a wata halitta săbuwa?"

Ayah  17:50  الأية
    +/- -/+  
قُلْ كُونُوا حِجَارَةً أَوْ حَدِيدًا
Hausa
 
Ka ce: "Ku kasance duwătsu ko kuwa baƙin ƙarfe."

Ayah  17:51  الأية
    +/- -/+  
أَوْ خَلْقًا مِّمَّا يَكْبُرُ فِي صُدُورِكُمْ ۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَا ۖ قُلِ الَّذِي فَطَرَكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ فَسَيُنْغِضُونَ إِلَيْكَ رُءُوسَهُمْ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَ ۖ قُلْ عَسَىٰ أَن يَكُونَ قَرِيبًا
Hausa
 
"Kő kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To ză su ce "Wăne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lőkaci." To, ză su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sună cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammăninsa ya kasance kusa."

Ayah  17:52  الأية
    +/- -/+  
يَوْمَ يَدْعُوكُمْ فَتَسْتَجِيبُونَ بِحَمْدِهِ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
"A rănar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓăwa game dă gőde Masa, kuma kună zaton ba ku zauna ba făce kaɗan."

Ayah  17:53  الأية
    +/- -/+  
وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُوا الَّتِي هِيَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ الشَّيْطَانَ يَنزَغُ بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ الشَّيْطَانَ كَانَ لِلْإِنسَانِ عَدُوًّا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma ka cẽ wa băyiNa, su faɗi kalma wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yană sanya ɓarna a tsakăninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne.

Ayah  17:54  الأية
    +/- -/+  
رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِكُمْ ۖ إِن يَشَأْ يَرْحَمْكُمْ أَوْ إِن يَشَأْ يُعَذِّبْكُمْ ۚ وَمَا أَرْسَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ وَكِيلًا
Hausa
 
Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kő kuwa idan Yă so zai azabtăku. Kuma ba Mu aika ka kană wakĩli a kansu ba.

Ayah  17:55  الأية
    +/- -/+  
وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِمَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ وَلَقَدْ فَضَّلْنَا بَعْضَ النَّبِيِّينَ عَلَىٰ بَعْضٍ ۖ وَآتَيْنَا دَاوُودَ زَبُورًا
Hausa
 
Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta săshen Annabăwa a kan săshe kuma Mun bai wa Dăwũda zabũra.

Ayah  17:56  الأية
    +/- -/+  
قُلِ ادْعُوا الَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِهِ فَلَا يَمْلِكُونَ كَشْفَ الضُّرِّ عَنكُمْ وَلَا تَحْوِيلًا
Hausa
 
Ka ce: "Ku kirăyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa."

Ayah  17:57  الأية
    +/- -/+  
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ يَدْعُونَ يَبْتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ الْوَسِيلَةَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ وَيَرْجُونَ رَحْمَتَهُ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُ ۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحْذُورًا
Hausa
 
Waɗancan, waɗanda suke kiran, sună nẽman tsăni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sună fătan sămun rahamarSa, kuma sună tsőron azăbarSa. Lalle ne azăbar Ubangijinka ta kasance abar tsőro ce.

Ayah  17:58  الأية
    +/- -/+  
وَإِن مِّن قَرْيَةٍ إِلَّا نَحْنُ مُهْلِكُوهَا قَبْلَ يَوْمِ الْقِيَامَةِ أَوْ مُعَذِّبُوهَا عَذَابًا شَدِيدًا ۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورًا
Hausa
 
Kuma băbu wata alƙarya făce, Mu ne măsu halaka ta a gabănin Rănar ˇiyăma kő kuwa Mũ măsu azăbta ta ne da azăba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littăfi rubũtacce.

Ayah  17:59  الأية
    +/- -/+  
وَمَا مَنَعَنَا أَن نُّرْسِلَ بِالْآيَاتِ إِلَّا أَن كَذَّبَ بِهَا الْأَوَّلُونَ ۚ وَآتَيْنَا ثَمُودَ النَّاقَةَ مُبْصِرَةً فَظَلَمُوا بِهَا ۚ وَمَا نُرْسِلُ بِالْآيَاتِ إِلَّا تَخْوِيفًا
Hausa
 
Kuma băbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ăyőyi făce sabőda mutănen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdăwa tăguwa, ăyă bayyananna, sai suka yi zălunci game da ita. Kuma bă Mu aikăwa da ăyőyi făce dőmin tsőratarwa.

Ayah  17:60  الأية
    +/- -/+  
وَإِذْ قُلْنَا لَكَ إِنَّ رَبَّكَ أَحَاطَ بِالنَّاسِ ۚ وَمَا جَعَلْنَا الرُّؤْيَا الَّتِي أَرَيْنَاكَ إِلَّا فِتْنَةً لِّلنَّاسِ وَالشَّجَرَةَ الْمَلْعُونَةَ فِي الْقُرْآنِ ۚ وَنُخَوِّفُهُمْ فَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا طُغْيَانًا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yă kẽwaye mutăne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda Muka nũna maka ba, făce dőmin fitina ga mutăne, da ităciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Mună tsőratar da su, sa'an nan (tsőratarwar) bă ta ƙăra su făce da kangara mai girma.

Ayah  17:61  الأية
    +/- -/+  
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ قَالَ أَأَسْجُدُ لِمَنْ خَلَقْتَ طِينًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da Muka cẽ wa mală'iku, "Ku yi sujada ga Ădamu," sai suka yi sujada, făce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka halitta shi yană lăka?"

Ayah  17:62  الأية
    +/- -/+  
قَالَ أَرَأَيْتَكَ هَٰذَا الَّذِي كَرَّمْتَ عَلَيَّ لَئِنْ أَخَّرْتَنِ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَأَحْتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Ya ce: "Shin, kă gan ka ! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtă mini zuwa ga Rănar ˇiyăma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, făce kaɗan."

Ayah  17:63  الأية
    +/- -/+  
قَالَ اذْهَبْ فَمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ فَإِنَّ جَهَنَّمَ جَزَاؤُكُمْ جَزَاءً مَّوْفُورًا
Hausa
 
Ya ce: "Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku,(Mu ba ku shi) sakamako cikakke."

Ayah  17:64  الأية
    +/- -/+  
وَاسْتَفْزِزْ مَنِ اسْتَطَعْتَ مِنْهُم بِصَوْتِكَ وَأَجْلِبْ عَلَيْهِم بِخَيْلِكَ وَرَجِلِكَ وَشَارِكْهُمْ فِي الْأَمْوَالِ وَالْأَوْلَادِ وَعِدْهُمْ ۚ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا
Hausa
 
"Kuma ka rikitar da wanda ka sămi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawăkinka da dăkărunka kuma ka yi tărẽwa da su a cikin dũkiyőyi da ɗiyă, kumaka yi musu wa'adi. Alhăli kuwa Shaiɗan bă ya yi musu wa'adin kőme făce da ruɗi."

Ayah  17:65  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ ۚ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ وَكِيلًا
Hausa
 
"Lalle ne băyiNa, bă ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli."

Ayah  17:66  الأية
    +/- -/+  
رَّبُّكُمُ الَّذِي يُزْجِي لَكُمُ الْفُلْكَ فِي الْبَحْرِ لِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ ۚ إِنَّهُ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا
Hausa
 
Ubangijinku ne Yake gudănar da jirgi a cikin tẽku, dőmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yă kasance a gare ku Mai jin ƙai.

Ayah  17:67  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فِي الْبَحْرِ ضَلَّ مَن تَدْعُونَ إِلَّا إِيَّاهُ ۖ فَلَمَّا نَجَّاكُمْ إِلَى الْبَرِّ أَعْرَضْتُمْ ۚ وَكَانَ الْإِنسَانُ كَفُورًا
Hausa
 
Kuma idan cũta ta shăfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace făce Shi. To, a lőkacin da Ya tsira da ku zuwa,ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci.

Ayah  17:68  الأية
    +/- -/+  
أَفَأَمِنتُمْ أَن يَخْسِفَ بِكُمْ جَانِبَ الْبَرِّ أَوْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ثُمَّ لَا تَجِدُوا لَكُمْ وَكِيلًا
Hausa
 
Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bă Ya shăfe gẽfen ƙasa game da ku kő kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bă ză ku sămi wani wakĩli ba dőminku?

Ayah  17:69  الأية
    +/- -/+  
أَمْ أَمِنتُمْ أَن يُعِيدَكُمْ فِيهِ تَارَةً أُخْرَىٰ فَيُرْسِلَ عَلَيْكُمْ قَاصِفًا مِّنَ الرِّيحِ فَيُغْرِقَكُم بِمَا كَفَرْتُمْ ۙ ثُمَّ لَا تَجِدُوا لَكُمْ عَلَيْنَا بِهِ تَبِيعًا
Hausa
 
Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lőkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabőda abin da kuka yi na kăfirci? Sa'an nan kuma bă ku sămun mai bin hakki sabőda ku, a kanMu, game da Shi.

Ayah  17:70  الأية
    +/- -/+  
وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا
Hausa
 
Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa măsu dăɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan măsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtăwa.

Ayah  17:71  الأية
    +/- -/+  
يَوْمَ نَدْعُو كُلَّ أُنَاسٍ بِإِمَامِهِمْ ۖ فَمَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَأُولَٰئِكَ يَقْرَءُونَ كِتَابَهُمْ وَلَا يُظْلَمُونَ فَتِيلًا
Hausa
 
A rănar da Muke kiran kőwane mutăne da lĩmăminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dă, mansa, to, waɗannan sună karătun littăfinsu, kuma bă a zăluntar su da zaren băkin gurtsin dabĩno.

Ayah  17:72  الأية
    +/- -/+  
وَمَن كَانَ فِي هَٰذِهِ أَعْمَىٰ فَهُوَ فِي الْآخِرَةِ أَعْمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
 
Kuma wanda ya kasance makăho a cikin wannan sabőda haka shi a Lăhira makăho ne kuma mafi ɓata ga hanya.

Ayah  17:73  الأية
    +/- -/+  
وَإِن كَادُوا لَيَفْتِنُونَكَ عَنِ الَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ لِتَفْتَرِيَ عَلَيْنَا غَيْرَهُ ۖ وَإِذًا لَّاتَّخَذُوكَ خَلِيلًا
Hausa
 
Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dőmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lőkacin, haƙĩƙa, dă sun riƙe ka masoyi.

Ayah  17:74  الأية
    +/- -/+  
وَلَوْلَا أَن ثَبَّتْنَاكَ لَقَدْ كِدتَّ تَرْكَنُ إِلَيْهِمْ شَيْئًا قَلِيلًا
Hausa
 
Kuma bă dőmin Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dă kă yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.

Ayah  17:75  الأية
    +/- -/+  
إِذًا لَّأَذَقْنَاكَ ضِعْفَ الْحَيَاةِ وَضِعْفَ الْمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيْنَا نَصِيرًا
Hausa
 
A lőkacin, lalle ne, dă Mun ɗanɗana maka ninkin azăbar răyuwa da ninkin azăbar mutuwa, sa'an nan kuma bă ză ka sămi mataimaki ba a kanMu.

Ayah  17:76  الأية
    +/- -/+  
وَإِن كَادُوا لَيَسْتَفِزُّونَكَ مِنَ الْأَرْضِ لِيُخْرِجُوكَ مِنْهَا ۖ وَإِذًا لَّا يَلْبَثُونَ خِلَافَكَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Kuma lalle ne, sun yi kusa, haƙĩƙa, su tăyar da hankalinka daga ƙasar, dőmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lőkacin, bă ză su zauna ba a kan săɓăninka făce kaɗan.

Ayah  17:77  الأية
    +/- -/+  
سُنَّةَ مَن قَدْ أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ مِن رُّسُلِنَا ۖ وَلَا تَجِدُ لِسُنَّتِنَا تَحْوِيلًا
Hausa
 
Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabăninka, daga ManzanninMu, kuma bă ză ka sămi jũyarwa ba ga hanyarMu.

Ayah  17:78  الأية
    +/- -/+  
أَقِمِ الصَّلَاةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَىٰ غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ ۖ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا
Hausa
 
Ka tsayar da salla a karkatar rănă zuwa ga duhun dare da lőkacin fitar alfijir lalle ne karătun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.

Ayah  17:79  الأية
    +/- -/+  
وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَّكَ عَسَىٰ أَن يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَّحْمُودًا
Hausa
 
Kuma da dare, sai ka yi hĩra da shi (Alƙur'ăni) akan ƙări gare ka. Akwai tsammănin Ubangijinka Ya tăyar da kai a wani matsayi gődadde.

Ayah  17:80  الأية
    +/- -/+  
وَقُل رَّبِّ أَدْخِلْنِي مُدْخَلَ صِدْقٍ وَأَخْرِجْنِي مُخْرَجَ صِدْقٍ وَاجْعَل لِّي مِن لَّدُنكَ سُلْطَانًا نَّصِيرًا
Hausa
 
Kuma ka ce: "Yă Ubangijĩna! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gunKa, wani ƙarfi mai taimako."

Ayah  17:81  الأية
    +/- -/+