Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma
kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa,
yã Ubangiji!"
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin
Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin
yã kasance wani al'amari hukuntacce."
Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na
mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya
daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda
haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã
hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka
hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."
Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu,
kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da
Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun
ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ
ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a
tsakãnin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.
To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun
sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma,
lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su
ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri
ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"
Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa,
har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani,
wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"
Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu
wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga
makõma.
Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka
yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne
mãsu tsananin husũma.