"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba
)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba
ba.
Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu
Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada
kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi
hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu
zuwa, ga tsakar hanya."
(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga
tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na
zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai."
Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa
gãfara,kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin
mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga
hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai
tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya.
Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka
kãfirta daga wutã.
Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar
waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da
taƙawa kamar fãjirai makarkata?
Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya
rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ
mai mayar da al'amari ga Allah ne.
(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da
HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka
ne?"