Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce:
"Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne
wãwãye, kuma amma bã su sani.
Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan
sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu
izgili, kawai ne."
Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake
abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su
a cikin duffai, bã su gani.
Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da
walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin
tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!
Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su
yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã
Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme
Mai ĩkon yi ne.
Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa,kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga
sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku.
Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.
Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to,
ku zõ da sũra guda daga misalinsa (Alƙur'ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku baicin
Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.
To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji
tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin
kãfurai.
Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na
ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu.
Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai
su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da
shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki,
kuma su, cikin su madawwama ne.
Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da
abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa
lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su
ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu
yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da
shi fãce fasiƙai.
Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da
Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne
mãsu hasãra.
Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar
da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa
gare Shi ake mayar da ku?
Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma
Ya daidaita zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan
kõmai Masani ne.
Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani
halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi
ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma muna
tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."
Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku,
sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."
Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu
sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin
sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka
kasance kuna ɓõyewa?"
Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi
sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga
gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku
kasance daga azzãlumai."
Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da
suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da
a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."
Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku
daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin
baƙin ciki."
Yã Banĩ Isrã'Ĩla ! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika
muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na. Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na
saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon
kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji
tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme,
kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma
bã su zama ana taimakon su ba.
Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku
muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin
wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.
Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun
zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku
kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi
tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da
tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su
zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.
Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta,
idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kãyar
da zunubai" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa."
Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda
haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da
suka kasance suna yi na fãsiƙanci.
Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki
dũtsen da sandarka." Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne
mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma
kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna."
Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda.
Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga
ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da
yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin
birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da
talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun
kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba.
Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba , da Nasãra da Makarkata,
wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna
da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna
yin baƙin ciki ba.
Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku:
"Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa,
tsammãninku ku kãrekanku.
Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku
yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina
nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai."
Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle
ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba,
tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."
Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce:
"Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi,
tana faranta ran mausu kallonta."
Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne
shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne."
Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman
ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta."
Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.
San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto
kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka,
akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su,
haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma
lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah,
kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa.
Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata
ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su
karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane?
Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan
sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin
da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?"
Shin fa, bã ku hankalta?
To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma
su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan
bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya
tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa.
Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce:
"Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa
alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?"
Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla : "Kada ku bauta wa kõwa
fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta,
kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku
bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku,alhãli kuwa
kuna mãsu bijirẽwa.
Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku
fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar
da shaida (a kanku).
Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani
ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da
zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su
abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku
kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce
wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga
mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke
aikatãwa.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da
wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka
ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre
da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma
wani ɓangare kuna kashẽwa?
Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga
abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar
taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya
je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan
kãfirai.
Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya
saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so
daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai
azãba mai wulãƙantarwa.
Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna
ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke
bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da
yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah
gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"
Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku,
(Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji
kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka
ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu
ĩmãni!"
Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne
mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a
rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin
an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a
kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi,
kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.
Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai
gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa
Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ
ba su sani ba.
Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma
Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna
karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a
Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina
kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da
suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin
sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna
nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne,
haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira.
Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.
Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a
kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da
wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.
Abin da Muka shãfe daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi
alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah
a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?
Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka?
Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya.
Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan
ĩmãninku, kãfirai,sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã
bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa.
Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.
Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin
kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke
aikatãwa Mai gani ne.
Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to,
yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama
suna baƙin ciki ba.
Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba," kuma Nasãra suka ce:
"Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi.
Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka
Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka
kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a
ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya
kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya
wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma.
Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da
abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.
Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata
ãyã ta zo mana?" Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar
maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne
masu sakankancewa.