Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã
karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin
da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata
bayyanãnna.
Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar
misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen nan da suka
ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
Ka ce: "Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah
bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta,to, lalle ita mai haɗuwa da ku
ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku
lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai
ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi
alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga
falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban
rabo.
Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar
fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah
ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa."