Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa
ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu
yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?
Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda
ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi
ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da
hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu
suka kasance sunã zãlunta.
Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu
zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan
akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma
Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan
mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi
sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã
kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin
da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a
ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi,
daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa.
Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba.
To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya,
halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah,
wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da
al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai
gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma
idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã
yanke ƙauna,
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma
Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne
alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban
rabo.
Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai
ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar
Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).
Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku,
sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke
aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya
ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka
aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su
kõmo.
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya
zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu
biyu).
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya
ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa,
kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode.
Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je
musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi,
kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.
Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa
shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga
ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga
bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.
Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta.
Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai
ikon yi ne a kan kõme.
Allah ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani
rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na
halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin
Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar,
kuma amma kũ, kun kasance ba ku sani ba."
Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan
Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta
zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."