Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845.
Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo
muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin
kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka
kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne
Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata
shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.
Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre
da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da
abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa
jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai." Fãce
maganar Ibrãhĩm ga ubansa (da yace), "Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban
mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai." "Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara,
kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take."
Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya
kasance yanã fãtan (rahamar) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to,
lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde.
Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya
da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai.
Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su
fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle
Allah Yanã son mãsu ãdalci.
Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar
da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su,
kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira,
to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ
mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga
aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka
ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su
sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka
ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya.
Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai
hikima
Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa'an nan kuma
kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin
da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu
ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai.
Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã
su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma
bã su kashe, ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa a tsãkanin
hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a,
to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi
a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai
suka yanke tsammãni daga mazõwa kaburbura.