Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a
lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya
sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta
lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai
labartãwa, Ya gaya mini."
Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma
idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da
sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne.
Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure
mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu
ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta
makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri,
mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin
da ake umunin su.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa
Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen
Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da
Annabi da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su
da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka
yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne."
Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta : mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu,
sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyinMu sãlihai, saisuka yaudare su,
sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ
biyu, wutã tãre da mãsu shiga."
Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,
sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna.
Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen
nan azzãlumai."
Da Maryama ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga
rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa
ta kasance daga mãsu tawãli'u.