Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka
daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan
kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs,
bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.
Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya
ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã
halitta shi daga lãka."
"Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su,
kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu
mãsu gõdiya ba."
Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga
barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan
itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga
madawwama."
Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar,
al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga
ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan
itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?"
Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku
al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga
ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!
Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da
iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu
al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku,shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin
su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.
Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne
Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã
faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?"
Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin
kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar
yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa."
Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle
ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ,
mãsu shiryuwa ne.
Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu
dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar
dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi,
daki-daki, ga mutãnen da suke sani.
Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana
daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki
ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare
shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."
Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku
ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu,
kuma bã su yin baƙin ciki.
To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya
ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a
lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da
kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su
yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai."
Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku,
daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai
ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta
ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu,
sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma
amma ba ku sani ba."
Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga
barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai
raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa
rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.
Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã
gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya
shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah
Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da
gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda
abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da
Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da
Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi
yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."
Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã
sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata
a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.
Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce:
"Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba
daga barinku?"
"Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba?
Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba."
Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa
daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan
kãfirai."
"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe
su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu
wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.
Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka
manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ
da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a
mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun
yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu.
Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki
shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini,
yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa.
To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã
bayyana!
Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda
tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa.
Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun
ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu
saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan
itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.
Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku
bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku
tsõron azãbar wani Yini mai girma."
"Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji,
daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma
tsammãninku anã jin ƙanku?"
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi,
a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu.
Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu.
Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka,
Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga
maƙaryata."
"Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani
namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya
sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin
halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara."
Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar
abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi
mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã
jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da
ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle
ne ni, tãre da ku mai jira ne."
To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama
daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu,
kuma ba su kasance mũminaiba.
Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa
Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo
muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku
bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba
mai raɗaɗi ta kãmã ku."
"Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da
ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar
ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna
a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi."
Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka
raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu
manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu
ĩmãni ne."
Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma
suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã
kasance daga manzanni !"
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar
muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu
nasĩha!"
Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah;
bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga
Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne
kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi
alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai."
"Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga
hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama
karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku,
kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:"
"Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko
ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya
yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."
Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar
da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu;
kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance
mãsu ƙĩ?"
"Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan
lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu,
mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci
dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a
tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu
hukunci."
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da
sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan
mutãne kãfirai?"
Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su
ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." ( sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã
su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa."
Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun
bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka
kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa.
Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa
da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su
zama bã su ji?
Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa
manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin
ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a
kan zukãtan kãfirai.
Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da
majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata
take.
"Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo
muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda
ni."