Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi
wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa,
haƙĩƙa,daga gafalallu.
Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla
maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.
"Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga
fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba
kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle
Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."
A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu
daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin
ɓata bayyananniya.
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin
duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
To, a lõkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin
duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da
wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."
Suka ce: "Yã bãbanmu! Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a
wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne,
kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku
suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake
nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa."
Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa,
ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa.
Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa,
akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka
tabbatar ga Yũsufu,a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru,
kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su
sani ba."
Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi,
kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne
Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"
Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga
dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da
alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske
mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da
iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar
da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya,
kuma shĩ ne daga maƙaryata."
Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa
zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai
wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin
da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce:
"Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika
ne mai daraja!"
Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na
nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata
abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga
ƙasƙantattu."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã
na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan
karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."
Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce: "Lalle
ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã
yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare
ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu
kyautatãwa."
Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku
lãbãrin fassararsa , kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna
Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da
Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne."
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare
mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da
mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."
"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ
da ubanninku.Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na
Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini
madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
"Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa
giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An
hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa."
Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka
ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar
Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba,
waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu
ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance
ga mafarki kunã fassarawa."
"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai
mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da
waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa
(Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi;
Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna
ne Masani game da kaidinsu."
Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?"
Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar
Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma
lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.
"Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da
mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai."
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da
Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne,
amintacce."
Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda
duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da
lãdar mãsu kyautatawa.
Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani
ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma
nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"
To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo
sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu
lũra da Shi ne."
Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a
kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne
Mafi rahamar mãsu rahama."
Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita,
suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita,
kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon
kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."
Ya ce: "Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah,
haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka
yi mãsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa."
Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi
dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga
Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."
Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance
yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu,ya
bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka
sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi,
ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da
suka kasance sunã aikatãwa."
Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a
cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari!
lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."
To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya
fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai
kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah
Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin
ilmi akwai wani masani.
Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a
gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare
su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke
siffantãwa."
Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka
ka kãma ɗayanmu amatsayinsa.Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã
mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi
alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na
sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã
yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin
mahukunta."
"Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta,
kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san
gaibu ba."
Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo,
akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya ( Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle
ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."
"Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da ɗan'uwansa. Kada ku yanke
tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar
Allah fãce mutãne kãfirai."
Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe
mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana
ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin
sadaka. "
Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian
shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi
Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu
kyautatãwa."
Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan
fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã
sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"
Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna
mãsu sujada. Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa.
Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata
game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga
ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana,
Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ,Shĩ ne
Masani, Mai hikima."
"Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar
lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka
karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
Wannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka
kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli
sunã yin mãkirci.
Ka ce: "Wannan ce hanyãta ; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda
suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki
ba."
Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga
mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda
ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira
shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?
Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an
jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke
so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.
Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai
kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a
gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne
waɗanda suka yi ĩmãni.