Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga
bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni,
sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa
gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa,
Mai tausayi, Maijin ƙai.
Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma
daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne
waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da
umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke
hankalta.
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã
fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge
sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma
mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke
ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu
daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu
daga inda ba su sani ba.
Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan
tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda
aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan
kãfirai."
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce,
"Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu
mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan
mãsu taƙawa.
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã
cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance
kuna aikatãwa."
Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka.
Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su
ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba,
baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya
haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai
wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce):
"Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah
Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi
tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda
yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce,
kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su,
haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce
mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka,
dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don
ɗammãninsu su yi tunãni.
Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai
shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna
karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu
ƙasƙantar da kai?
Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su.
Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã
ƙirƙirãwa.
Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai
riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke
hukuntãwa ya mũnana.
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan
ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan
ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta
ba.
Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa
lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma
lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta) .
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai
Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma
sunã da azãba mai raɗaɗi.
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da
suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke
yin ĩmãni.
Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a
bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke
saurãre.
Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima;Munã shãyar da ku daga
abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan
mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da
abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke
hankalta.
"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin
Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar
launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan,
haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku
akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a
bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta
ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka
ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga
mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa,
da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki
dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme) .
Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme,
da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan
shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya
ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba.
Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon
yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi,
bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda
yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce
kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai
ikon yi ne.
Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake
riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne
waɗanda suke yin ĩmãni.