First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالذَّارِيَاتِ ذَرْوًا
Hausa
Ină rantsuwa da iskőki măsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
|
Ayah 51:2 الأية
فَالْحَامِلَاتِ وِقْرًا
Hausa
Sa'an nan da girăgizai măsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
|
Ayah 51:3 الأية
فَالْجَارِيَاتِ يُسْرًا
Hausa
Sa'an nan da jirăge măsu gudăna (a kan ruwa) da sauƙi.
|
Ayah 51:4 الأية
فَالْمُقَسِّمَاتِ أَمْرًا
Hausa
Sa'an nan da Mală'iku măsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
|
Ayah 51:5 الأية
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٌ
Hausa
Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
|
Ayah 51:6 الأية
وَإِنَّ الدِّينَ لَوَاقِعٌ
Hausa
Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
|
Ayah 51:7 الأية
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْحُبُكِ
Hausa
Ină rantsuwa da samă ma'abũciyar hanyőyi ( na tafiyar taurări da sautin rediyo).
|
Ayah 51:8 الأية
إِنَّكُمْ لَفِي قَوْلٍ مُّخْتَلِفٍ
Hausa
Lalle kũ, haƙĩƙa, kună cikin magana mai săɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
|
Ayah 51:9 الأية
يُؤْفَكُ عَنْهُ مَنْ أُفِكَ
Hausa
Ană karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
|
Ayah 51:10 الأية
قُتِلَ الْخَرَّاصُونَ
Hausa
An la'ani măsu ƙiri-faɗi.
|
Ayah 51:11 الأية
الَّذِينَ هُمْ فِي غَمْرَةٍ سَاهُونَ
Hausa
Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jăhilci.
|
Ayah 51:12 الأية
يَسْأَلُونَ أَيَّانَ يَوْمُ الدِّينِ
Hausa
Sună tambaya: "Yaushe ne rănar sakamako ză ta auku?"
|
Ayah 51:13 الأية
يَوْمَ هُمْ عَلَى النَّارِ يُفْتَنُونَ
Hausa
Ranar da suke a kan wuta ană fitinar su.
|
Ayah 51:14 الأية
ذُوقُوا فِتْنَتَكُمْ هَٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تَسْتَعْجِلُونَ
Hausa
(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kună
nẽman zuwansa da gaggăwa."
|
Ayah 51:15 الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Hausa
Lalle măsu taƙawa, sună a cikin lambunan ităce da marẽmari.
|
Ayah 51:16 الأية
آخِذِينَ مَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُحْسِنِينَ
Hausa
Sună măsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bă su. Lalle sũ, sun kasance măsu
kyautatăwa a gabănin haka (a dũniya).
|
Ayah 51:17 الأية
كَانُوا قَلِيلًا مِّنَ اللَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ
Hausa
Sun kasance a lőkaci kaɗan na dare suke yin barci.
|
Ayah 51:18 الأية
وَبِالْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ
Hausa
Kuma a lőkutan asuba sună ta yin istigfări.
|
Ayah 51:19 الأية
وَفِي أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ لِّلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ
Hausa
Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rőƙo da wanda aka hana wa
rőƙo.
|
Ayah 51:20 الأية
وَفِي الْأَرْضِ آيَاتٌ لِّلْمُوقِنِينَ
Hausa
Kuma a cikin ƙasă akwai ăyőyi ga măsu yaƙĩni.
|
Ayah 51:21 الأية
وَفِي أَنفُسِكُمْ ۚ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
Hausa
Kuma a cikin răyukanku (akwai ăyőyi). To, bă ză ku dũbă ba?
|
Ayah 51:22 الأية
وَفِي السَّمَاءِ رِزْقُكُمْ وَمَا تُوعَدُونَ
Hausa
Kuma a cikin sama arzikinku ( yake fitőwa) da abin da ake yi muku alkawari.
|
Ayah 51:23 الأية
فَوَرَبِّ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ إِنَّهُ لَحَقٌّ مِّثْلَ مَا أَنَّكُمْ
تَنطِقُونَ
Hausa
To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasă, lalle shĩ (abin da ake yi muku
alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kună karantăwa na magana,
|
Ayah 51:24 الأية
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ الْمُكْرَمِينَ
Hausa
Shin, lăbărin Băƙin Ibrăhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
|
Ayah 51:25 الأية
إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلَامًا ۖ قَالَ سَلَامٌ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ
Hausa
A lőkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata
a gare ku, mutăne băƙi!"
|
Ayah 51:26 الأية
فَرَاغَ إِلَىٰ أَهْلِهِ فَجَاءَ بِعِجْلٍ سَمِينٍ
Hausa
Sai ya jũya zuwa ga iyălinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
|
Ayah 51:27 الأية
فَقَرَّبَهُ إِلَيْهِمْ قَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ
Hausa
Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bă ză ku ci ba?"
|
Ayah 51:28 الأية
فَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةً ۖ قَالُوا لَا تَخَفْ ۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَامٍ
عَلِيمٍ
Hausa
Sai ya ji tsőro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsőro." Kuma suka yi masa
bushăra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
|
Ayah 51:29 الأية
فَأَقْبَلَتِ امْرَأَتُهُ فِي صَرَّةٍ فَصَكَّتْ وَجْهَهَا وَقَالَتْ عَجُوزٌ
عَقِيمٌ
Hausa
Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallőwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce:
"Tsőhuwa bakarăriya (ză ta haihu)!"
|
Ayah 51:30 الأية
قَالُوا كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ ۖ إِنَّهُ هُوَ الْحَكِيمُ الْعَلِيمُ
Hausa
Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai
ilmi."
|
Ayah 51:31 الأية
قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ
Hausa
(Ibrăĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yă kũ Manzanni!"
|
Ayah 51:32 الأية
قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ
Hausa
Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutăne, măsu laifi.
|
Ayah 51:33 الأية
لِنُرْسِلَ عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن طِينٍ
Hausa
"Dőmin mu saka musu waɗansu duwătsu na wani yumɓu ( bom).
|
Ayah 51:34 الأية
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلْمُسْرِفِينَ
Hausa
"Waɗanda aka yi wa alăma daga wajen Ubangijinka, dőmin măsu ɓarna."
|
Ayah 51:35 الأية
فَأَخْرَجْنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
|
Ayah 51:36 الأية
فَمَا وَجَدْنَا فِيهَا غَيْرَ بَيْتٍ مِّنَ الْمُسْلِمِينَ
Hausa
Sai dai ba mu sămu ba, a cikinta, făce gida guda na Musulmi.
|
Ayah 51:37 الأية
وَتَرَكْنَا فِيهَا آيَةً لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ الْعَذَابَ الْأَلِيمَ
Hausa
Kuma Muka bar wata ăyă, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsőron azăba, mai raɗaɗi.
|
Ayah 51:38 الأية
وَفِي مُوسَىٰ إِذْ أَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Hausa
Kuma ga Mũsă, a lőkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli
bayyananne.
|
Ayah 51:39 الأية
فَتَوَلَّىٰ بِرُكْنِهِ وَقَالَ سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ
Hausa
Sai ya jũya băya tăre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kő kuwa mahaukaci
!"
|
Ayah 51:40 الأية
فَأَخَذْنَاهُ وَجُنُودَهُ فَنَبَذْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٌ
Hausa
Sabőda haka, Muka kama shi tăre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin
tẽku, alhăli kuwa yană wanda ake zargi.
|
Ayah 51:41 الأية
وَفِي عَادٍ إِذْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الرِّيحَ الْعَقِيمَ
Hausa
Kuma ga Ădăwa, a lőkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
|
Ayah 51:42 الأية
مَا تَذَرُ مِن شَيْءٍ أَتَتْ عَلَيْهِ إِلَّا جَعَلَتْهُ كَالرَّمِيمِ
Hausa
Bă ta barin kőme da ta jẽ a kansa, făce ta mayar da shi kamar rududdugaggun
ƙasũsuwa.
|
Ayah 51:43 الأية
وَفِي ثَمُودَ إِذْ قِيلَ لَهُمْ تَمَتَّعُوا حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa
Kuma ga Samũdăwa, a lőkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dăɗi har wani ɗan
lőkaci,"
|
Ayah 51:44 الأية
فَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ فَأَخَذَتْهُمُ الصَّاعِقَةُ وَهُمْ يَنظُرُونَ
Hausa
Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabőda haka tsăwa ta kăma su,
alhăli kuwa sună kallo.
|
Ayah 51:45 الأية
فَمَا اسْتَطَاعُوا مِن قِيَامٍ وَمَا كَانُوا مُنتَصِرِينَ
Hausa
Ba su kő sămu dămar tsayăwa ba, kuma ba su kasance măsu nẽman ăgaji ba.
|
Ayah 51:46 الأية
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ
Hausa
Da mutănen Nũhu a gabănin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutăne ne
făsiƙai.
|
Ayah 51:47 الأية
وَالسَّمَاءَ بَنَيْنَاهَا بِأَيْدٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
Hausa
Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhăli kuwa lalle Mũ ne Măsu
yalwatăwa.
|
Ayah 51:48 الأية
وَالْأَرْضَ فَرَشْنَاهَا فَنِعْمَ الْمَاهِدُونَ
Hausa
Kuma ƙasă Mun shimfiɗa ta, To, madalla da măsu shimfiɗăwa, Mũ,
|
Ayah 51:49 الأية
وَمِن كُلِّ شَيْءٍ خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Hausa
Kuma daga kőme Mun halitta nau'i biyu, watakila ză ku yi tunăni.
|
Ayah 51:50 الأية
فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa
Sabőda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai
bayyanannen gargaɗi.
|
Ayah 51:51 الأية
وَلَا تَجْعَلُوا مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ ۖ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ
مُّبِينٌ
Hausa
Kuma kada ku sanya, tăre da Allah wani abin bautăwa na dabam, lalle nĩ, mai
gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
|
Ayah 51:52 الأية
كَذَٰلِكَ مَا أَتَى الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا سَاحِرٌ
أَوْ مَجْنُونٌ
Hausa
Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabăninsu ba făce sun ce: "Mai
sihiri ne kő mahaukaci."
|
Ayah 51:53 الأية
أَتَوَاصَوْا بِهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
Hausa
shin, sună yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ă'a, sũ dai mutăne ne măsu girman kai.
|
Ayah 51:54 الأية
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَا أَنتَ بِمَلُومٍ
Hausa
Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
|
Ayah 51:55 الأية
وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Kuma ka tunătar, dőmin tunătarwa tană amfănin mũminai.
|
Ayah 51:56 الأية
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
Hausa
Kuma Ban halitta aljannu da mutăne ba sai dőmin su bauta Mini.
|
Ayah 51:57 الأية
مَا أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَا أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِ
Hausa
Bă Ni nufln (sămun) wani arziki daga gare su, Bă Ni nufin su (yi Mini hidimar)
ciyar da Ni.
|
Ayah 51:58 الأية
إِنَّ اللَّهَ هُوَ الرَّزَّاقُ ذُو الْقُوَّةِ الْمَتِينُ
Hausa
Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtăwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
|
Ayah 51:59 الأية
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَابِهِمْ فَلَا
يَسْتَعْجِلُونِ
Hausa
To, lalle waɗanda suka yi zălunci sună da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin
abőkansu, sabőda haka kada su yi Mini gaggăwa.
|
Ayah 51:60 الأية
فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن يَوْمِهِمُ الَّذِي يُوعَدُونَ
Hausa
Sabőda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kăfirta, daga rănar su wadda aka yi
musu alkawari.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|